Tattaunawar Addinai



Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Na yi imani da Allah daya ba shi da abokin tarayya, na kuma kafirce wa duk wani abin bauta ba shi ba. Sannan ya ce: Allah (S.W.T) ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya Mai albishir da gargadi ga mutane, sannan zai mayar da kaidin duk mai kaidi kansa.

Yahudawa

 Sannan ya ce da Yahudawa: Shin kun taru ne nan domin in karbi maganarku babu wata hujja sai suka ce: A’a,. Ya ce: Me ya kai ku ga cewa Uzairu (A.S) dan Allah ne? Sai suka ce: Domin ya raya wa Bani Isra’ila Attaura kuma ba wanda Allah zai yi masa haka sai dansa. Sai Manzon Allah ya ce: Domin me Uzairu (A.S) zai zama dan Allah ga Musa (A.S) alhalin shi ne ya zo wa Bani Isra’ila da Attaura kuma aka ga mu’ujizozi daga gare shi kamar yadda kuka sani. Idan kuwa Uzairu (A.S) zai zama dan Allah saboda karamar raya Attaura, me ya sa kuka kira shi dan Allah ba Musa ba? Sai suka ce: Saboda ya raya wa Bani Isra’ila Attaura bayan ta bace, kuma ba yadda zai ba wani damar haka sai wanda yake dansa. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ya ya Uzairu (A.S) ya zama dan Allah ba Musa (A.S) ba wanda shi ne ya zo da Attaura din aka ga mu’ujizozi a hannunsa kamar yadda kuka sani? Idan kuwa Uzairu (A.S) zai samu wannan matsayi saboda ya raya Attaura to Musa (A.S) shi ne ya fi cancanta da ya zama dan ba shi ba, domin shi ne ya zo da Attaurar tun farko.

 Idan kuma shi Uzairu (A.S) ya cancanci girmama wa a matsayin da saboda ya raya Attaura to Musa ya cancanci matsayin da ya fi na da, domin ku idan kuna nufi da da ma’anar da kuke gani a Duniya na â€کya’ya da iyaye suke haifarsu ta hanyar takinsu (kwanciya) daga iyaye maza ga su matan to kun kafircewa Allah kun kwatanta shi da bayinsa kuma kun wajabta masa abin da yake da siffa na fararru, saboda haka ya wajaba ke nan ya zama Fararre abin halitta a wajanku ya zama yana da mahalicci da ya fare shi.

Sai suka ce: Ba haka muke nufi ba, hakika wannan kafirci ne kamar yadda ka fada sai dai mu muna nufin girmamawa kamar yadda wasu malamai sukan kira wanda suke son girmamawa da wani matsayi da “Ya dana!â€‌ ko kuma ya ce: “Wannan dana neâ€‌ ba domin ya haife shi ba, domin saudayawa yakan gaya wa wanda ba su da wata nasaba da shi hakan. Haka nan yayin da Allah ya yi wa Uzairu (A.S) wannan ni’ima sai muka fahimci cewa bai yi masa haka ba sai don ya rike shi dansa ta hanyar girmamawa ba domin ya haife shi ba. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Wannan shi ne abin da nake gaya muku cewa, idan da wannan Uzairu (A.S) ya zama dansa to wannan matsayi ya fi cancanta ga Musa (A.S) kuma Allah zai kunyata duk mai karya da furucinsa da kansa kuma aniyarsa zata dawo kansa. Ku sani cewa abin da kuka kafa dalili da shi zai lizimta muku fiye da abin da ya wuce haka, domin ku (a misali) kuna cewa: Wani mai girma daga cikinku yakan gaya wa waninsa da ba su da nasaba: "Ya dana!" ba don ya haife shi ba, sai don girmamawa, kuma zaku iya samun wannan mai girma din yana gaya wa wani cewa: "Dan’uwana ne" ya kira wani kuma da "Wannan shehina ne" ko "Babana ne" ko "Shugabana ne" ko "Ya shugabana!" ta hanyar girmamawa, wato duk sa’adda aka samu wanda ya fi girma to sai ya dada masa kalma ta girmamawa fiye da dayan, idan kuwa haka ne a bisa abin da kuke cewa ya halatta Musa (A.S) ya zama Dan’uwan Allah ko Shehinsa ko Babansa ko Shugabansa, domin ya fi Uzairu (A.S) daraja, kamar yadda idan wani ya fi da daraja sai a ba shi girmamawa fiye da shi, sai ya ce masa: "Ya Shugabana! Ko Ya Shehina! Da Ya Ammina! Da Ya Shugabana! ta hanyar girmamawa domin karin girma, shin ya halatta a ganinku Musa (A.S) ya zama Dan’uwan Allah ko Shehinsa ko Amminsa ko Shugabansa ta hanyar girmamawa domin girmansa ya fi na Uzairu (A.S) kamar yadda ake dada girma ga wanda ya fi da a fadarku  a ce da shi: "Ya Shugabana! Ya Shehina! Ya Ammina! Ya Sarkina".

Imam Sadik (A.S) Ya ce: Sai mutanen suka dimauce suka ce "Ya Muhammad! Ka saurara mana mu yi tunani tukuna game da abin da ka ce. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ku yi duba da zukata masu kudurce yin adalci, Allah ya shiryar da ku.

Kiristoci

Sa’annan sai ya fuskanci Kiristoci ya ce da su: Ku kuna cewa Dadadde Madaukaki (S.W.T) ya hade da Masihi Dansa (A.S). Me kuka nufi da wannan magana?. Shin kuna nufin Dadadde ya zama Fararre saboda wannan Fararren da ya hade da shi wanda shi ne Isa (A.S) ko kuna nufin Fararren da yake shi ne Isa (A.S) ya koma Maras farko kamar samuwar Dadadde wanda yake shi ne Allah?. Ko kuma ma’anar ya hade da shi ya shiga jikinsa a wajanku yana nufin ya kebance shi da karama da girmamawa ne wacce bai girmama waninsa da irinta ba?. Idan kuka ce: Dadadde ya koma Fararre to kun rushe, domin Dadadde bai yiwuwa ya juya ya koma Fararre. Idan kuma kuna nufin Fararre ya koma Dadadde to kun yi warwarar magana domin mustahili ne Fararre ya koma Dadadde. Idan kuma kuna nufin ya hade da shi domin ya kebance shi ya zabe shi a kan sauran bayi to kun yi furuci da cewa Isa (A.S) Fararre ne da ma’anar ya hade shi saboda haka, domin idan Isa (A.S) ya kasance Fararre Allah (S.W.T) ya kasance ya hade da shi da ma’anar ya sanya shi Mafificin halitta a wajansa to Isa (A.S) ya zama daya daga cikin fararru da wannan ma’ana, wannan kuwa sabanin abin da ku kuke bayyanawa ne.

Sai Kiristocin suka ce: Ya Muhammad! Yayin da Allah ya bayyanar da abubuwan mamaki a hannun Isa (A.S) to ya rike shi da ne ta hanyar girmamawa. Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Ai kun ji abin da na gaya wa Yahudawa a irin wannan ma’ana da kuka ambata, sannan ya maimaita abin da ya fada wa Yahudawa dalla -dalla, sai suka yi shiru banda mutum daya a cikinsu da ya ce da shi: Ya Muhammad! Shin ba kuna cewa Ibrahim (A.S) Khalilul-Lahi ba? Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Mu Muna cewa hakan. Sai ya ce: Idan kuna cewa haka domin me zaku hana mu fadar waccan maganar? Sai Manzo (S.A.W) ya ce: Maganganun ba su yi kama da juna ba, domin ma’anar Khalilul-Lahi an ciro shi daga Khulla wato Bukata da Talauci domin shi ya kasance Mabukaci zuwa ga Ubangijinsa ne, Mai yankewa zuwa gare shi, Mai kamewa ga barin waninsa, wannan a lokacin da aka jefa shi wuta da manjanik (majaujawa) ne sai Allah ya aika Jibra’il (A.S) da ka je ka riski bawana, sai ya zo ya riske shi a cikin iska, Ya ce da shi: Ka umarce ni da duk abin da kake so hakika Allah ya aiko ni da in taimake ka, Sai Ibrahim (A.S) ya ce da shi: "Hasbiyal-Lahu Wa ni’imal Wakilâ€‌, Ni ba na tambayar wani wata bukata sai Shi, ba na bukata sai gare Shi". Saboda haka sai ya kira shi da Khalilinsa wato Mabukaci Mai yankewa daga komai sai zuwa gare shi, idan ya zama ma’anar Khulla wato ya tsaya a kan wasu sirri da babu wanda ya same su, ma’anar Khulla zata zama masani da sirrinsa, a nan babu wani kamanta shi da halittarsa. Shin ba kwa gani ne cewa idan bai yanke zuwa gare shi ba bai zama Khalilinsa ba haka ma idan bai san sirrinsa ba bai zama Khalilinsa ba? Amma wanda mutum ya haifa ko da kuwa ya wulakanta shi ya nesantar da shi daga gare shi ba ya fita daga kasancewa dansa ne, domin ma’anar haihuwa ta tsayu da wannan. Sa’anan idan ya wajaba domin ya ce da Ibrahim (A.S) Khalili ku kiyasta ku ce da Isa (A.S) dansa ya wajaba kenan ku ce da Musa (A.S) dansa domin mu’ujizar da take tare da shi ba ta gaza ta Isa (A.S) ba. Sai ku ce Musa (A.S) shi ma dansa ne, kuma ya halatta inda haka ne ku ce da shi: Shaihin Allah ko Shugabansa ko Amminsa ko Amirinsa kamar yadda na riga na gaya wa Yahudawa hakan.

Sai wadansunsu suka ce: Ai a cikin Littafi saukakke hakika Isa (A.S) ya ce: “Ni zan tafi zuwa ga Babana kuma Babankuâ€‌. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Idan kun kasance kuna amfani da Littafin ne, to a cikinsa an ce: “Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babankuâ€‌, Idan haka ne ku ce da wadanda Isa (A.S) ya yi magana da su gaba daya â€کYa’yan Allah ne kamar yadda Isa (A.S) yake dansa ta fuskar da Isa (A.S) yake dansa.

Sa’annan abin da yake cikin wannan littafin yana karyata abin da kuke rayawa cewa Isa (A.S) ya zama dansa ta fuskacin kebanta, domin kuna cewa shi dansa ne ta fuskacin kebantarsa da ya yi da abin da bai kebanci wani da shi ba, sannan kun sani cewa abin da ya kebanci Isa (A.S) da shi bai kebanci wadannan mutane da Isa (A.S) ya ce da su “Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babankuâ€‌ da shi ba, sai wannan ya nuna cewa bai kebanta da Isa (A.S) ba domin ya tabbata a wajanku cewa Isa (A.S) ya gayawa wanda bai da wannan matsayi irin nasa, sai kuka hakaito maganar Isa (A.S) kuka yi tawilinsa ba bisa ma’anarsa ba, domin shi da ya ce: “Ni mai tafiya ne zuwa ga Babana kuma Babankuâ€‌  abin da yake nufi ba shi ne abin da kuka tafi a kai ba. Me ya sanar da ku ko yana nufin ni mai tafiya ne zuwa ga Babana Adam (A.S) ko zuwa ga Nuhu (A.S) kuma Allah zai daukaka ni zuwa gare su ya hada ni tare da su, tare da Adam Babana kuma Babanku, kai ba abin da yake nufi sai wannan. Imam Sadik (A.S) ya ce: Sai Kiristoci suka yi shiru suka ce: Ba mu taba ganin mai wuyar kayarwa mai hujjoji masu karfi irinka ba, zamu tafi mu duba al’amuranmu.

Dahriyya

Sa’annan sai ya fuskanci â€کyan Dahriyya ya ce da su: Me ya sa kuke cewa abubuwa ba su da farko ba su da karshe?. Kuma ba su gushe ba kuma ba sa gushewa?. Sai suka ce: Domin mu ba ma hukunci sai da abin da muka gani, kuma ba mu samu farko ga abubuwa ba sai muka yi hukunci da cewa ba su gushe ba tun farko samammu ne, ba mu gan su suna karewa ba sai muka yi musu hukunci da cewa su madawwama ne. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Shin kun same ta Maras farko ko kun same ta Mai wanzuwa har abada ba za ta gushe ba?. Idan kuka ce: Kun same ta hakan, to kun tabbatar wa kawukanku cewa ba ku gushe ba a kamanninku da hankulanku ba ku da farko kamar yadda ba zaku gushe ba a halinku kamar yadda kuke, kuma idan kuka ce haka, to kun yi musun hakikanin zahiri kuma masana wadanda suke ganinku zasu karyata ku.



back 1 2 3 4 5 6 7 next