Zamanin Cin Nasara



Zamanin Cin Nasara

Daga karshe bayan yakin watanni takwas da zuwan al’ummu daban-daban sai lokacin da ake fata ya zo, juyi ya samu cin nasara.

Cin nasarar juyin imam Mahadi (A.S) da yake nufin dawowar duniya a kan tsari mafi kyau yana nufin samar da wani zamani da za a iya kiran sa da “zamanin aljannar duniya” a bayan kasa.

Tunda tsari mafi kyau na halitta ya kafu a kan gaskiya ne saboda haka karya zata kau, tunda gyara ne ya zo to barna zata gushe, kuma tunda adalci ya zo to zalunci zai rushe[1], da cin nasarar dan Hasan Askari (A.S) ne za a samu mafi kamalar zamani a tarihin dan Adam. Abin da imam Mahadi (A.S) zai aiwatar ya fi karfin aikin mutum a bisa ala’ada, kuma a wannan daular ba kawai mutum ne zai samu hakkinsa ba, al’amarin daidaito ya shafi dukkan halittu ne.

Zamanin samun nasara zamani ne na jin dadin yin ibadar bayi ‘yantattu, da kuma daular masu tsoron Allah, da tabbatar hikimar Allah ta halittar aljani da mutum wanda yake shi ne bauta ga Allah. A mahangar Shi'a: babu kuma wata daula da zata kasance bayan daular imam Mahadi (A.S). Daular karshe ita ce daular Annabi (S.A.W) karkashin jagorancin imam Mahadi (A.S) dan Hasan Askari (A.S).

Imam Sadik (A.S) yana cewa: Kowace al’umma tana da daula da suke sauraron zuwanta, amma daularmu tana karshen duniya ne[2]. Don haka cin nasarar imam Mahadi (A.S) yana nufin samuwar yaduwa da kafuwar musulunci a gabaci da yammacin duniya, kuma yana nuna karshe na musulmi ne, ba na ‘yancin jari-hujjar demokradiyya ko kwaminis da sauran fikirori ba.

Juyin imam Mahadi na musulunci da hukumar adalci na mahadiyyanci zai bayyana a fili cewa shi ne mafi girma da daukakar misali na hukuma ga mutane. Jagoran juyi zai rushe dukkan zaluncin da yake wakana a bangarorin siyasa da tattalin arziki, da tsaro, da al’adu, da zamantakewa, ya mayar da na adalci a gurbinsa ta hanyar tabbatar da addinin Allah na duniya kuma zai kawar da dukkan kabilanci da bambanci ta yadda za a sami tsari mai hedkwata daya a duk fadin duniya: Wannan tsarin ne zai kawo kaunar juna da soyayya tsakanin mutane, kuma su kasance kamar tarayyar kudan zuma a gefen shuganbansu guda daya. Manzon rahama (S.A.W) yana cewa: Al’ummar Mahadi zata tattaro zuwa gareshi, kamr yadda kudan zuma suke tattaruwa zuwa ga sarauniyarsu[3]. Da kuma fadinsa: Adalci zai game ko’ina har sai mutane sun koma kamar farkon al’amarinsu (na halitta), ba a farkar da mai bacci, ba a zubar da jini[4].

Da cin nasarar imam Mahadi (A.S) za sa mu mafi girman gyara a duniya, da yalwa, da raya kasa, da tsarkake duniya daga zalunci, a rayar da musulunci na asali, kuma duniya ta futo da taskokinta da albarkatunta, ni’ima zata samu ga kowane mutum bisa daidaito, idanuwan ‘yan Adam zasu bude wajen sanin sammai bakwai da duniyoyi shida[5].

Wannan daula a mahangar Shi'a ita ce mafi girman daula a tarihi, musulunci da ahlinsa zasu daukaka, munafunci da ma’abotansa zasu kaskanta, daula ce da zata bayar da karamar duniya da lahira ga dan Adam, ta kawar da talauci, ta tarbiyyantar da mutane masu kima da haske[6].

A takaice muna iya cewa daula ce da na sama da na kasa duk suka yarda da ita, imam Sadik yana fada: Halittun duniya da halittun sama zasu yarda da halifancinsa har da ma tsuntsu a sararin sama[7].

A mahangar Shi'a da cin nasarar juyin imam Mahadi (A.S) za a kafa juyin karshe a tarihin dan Adam, kuma bayan nan babu wani juyi da zai sake faruwa, hukumarsa zata ci gaba har tashin kiyama[8].



1