KebantattunAl’amuran Mahangar Shi'a



Da yawa daga wadannan nazarorin da suka zo game da karshen zamani suna da dunkulallun ra’ayoyi marasa fito wa fili game da hukumar karshen zamani da ‘yancin dan Adam, da tsarin mallaka, da tsarin tattalin arziki, da asasin kyawawan dabi’u, da wayewa, da al’adu, amma Shi'a sun amsa wannan dalla-dalla kamar yadda zamu iya gani nan gaba.

7- Rayuwa

Nazarin Shi'a game da karshen duniya bai takaita da nan gaba ba, ya shafi har wannan zamanin namu na  yau ne ta bangarorin siyasa da yake da gudummuwa mai yawa a kan wannan fage. Haka nan Shi'a ne kawai suke ganin mai tseratar da dan Adam a raye yake, kuma mahalarci ne a kan komai sabanin sauran addinai kamar budanci, da indiyanci, da zartush, da kiristanci, da yahudanci da kuma sauran mulhidai marasa imani da Allah.

Sauran mahangai: mai tseratar da duniya a wajensu nazari ne kawai na kwakwalwa wanda babu shi a halin yanzu a fili a zahiri, amma a gun Shi'a imam Mahadi (A.S) duk da ya buya daga ganin mutane amma yana aiki a raye, yana nan yana shiga cikin al’amari da sha’anin ‘yan Adam, kuma yana taka rawa muhimmiya a cikin al’amuran mutane kai tsaye; a al’amuran da suka hada da na siyasa, da al’adu, da al’umma, da na tattalin arziki, da tsari[4], kuma shi wasida ce na falala da shiriya tsakanin Ubangiji da halittunsa bayan wucewar annabta, domin Shi'a suna ganin alakar dan Adam da ubangiji ba yankakkiya ba ce, suna ganin ta alaka ce mai ci gaba da dorewa har abada.

Sakamakon bincike ya nuna mana cewa; mahangar Shi'a ta fi kowacce domin tana kunshe da sani da bayanin dalla-dallanta, da bayyana a fili, da tsari. Kuma wata mahada ce mai kiyaye ruwayoyi da ayoyin kur’ani masu yawa da tattararrun ilmomi a duniyar musulmi. Don haka ne har yau ba a taba samun wani tsara na wannan mahanga ba, ko kuma abin da zai zo ya bata ta, ko ya rusa ta.

Wannan mahanga ita ce mai aiki domin sa-in-sa da azzalumai da rayar da addini da ‘yanci, sabanin masu ra’ayin cewa nan gaban karshen zamani ba sananne ba ne takamaimai, kuma zai dadu ne ta hanyar daduwar kwayoyin halitta a duniya.

 

[1] Kada a manta da nazarin pozitibist gameda ma’aunin ilimi.
[2] Allama Diba’diba’i, Shi'a, shafi 89 –90.
[3] Abin da ya gabata, shafi: 94 – 103.
[4]  Dokta Hasan Buhari, Sinamaye Holiwood Wa Mahdawiyyat, Internet: www.imammahdi.net.

 



back 1 next