KebantattunAl’amuran Mahangar Shi'a



KebantattunAl’amuran Mahangar Shi'a

Mahangar Shi'a ba tare da alfahari ba tana kunshe da nazari da wata mahanga ba ta da shi, sannan kuwa ta kebanta da al’amuran da suke da dalili a hankalce sabanin mafi yawan ra’ayoyin sauran mazhabobi da addinai.

1-Yiwuwar Maimaici

Idan ma’aunin ilimi shi ne karbar maimaici[1], to irin tashin imam Mahadi (A.S) da tsayuwarsa don kafa daular adalci ta faru a lokuta masu yawa a zamanin farko kamar sauran sunnonin Allah. Don haka hukumarsa zata kasance wani bangare ne na sauran da suka gabata, tafarkin imam Mahadi da zuwansa ya yi kama da irin zuwan Annabi Musa (A.S), da Isa (A.S), da Muhammad (S.A.W).

Idan haka ne: Shin zai zama abin mamaki idan Allah ya kawo wani Musan wannan zamani wato imam Mahadi (A.S) da zai kawar da zalunci da adalcinsa? da kuma taimaka masa da zuwan Harunansa wato annabi Isa (A.S) domin su kwance raunanan mutane daga kangin daurin Fir’aunan zamani, su tseratar da su daga Dujal mai sihiri?.

Shin zai zama abin mamaki domin Allah ya sake tayar da wani mai tseratarwa ga dan Adam kamar yadda Muhammad musdafa (A.S) ya zo yana mai cewa: Ku ce la’ilaha illalLah! Don haka ne harkar imam Mahadi (A.S) mai tseratar da dan Adam wani abu ne wanda ya maimaitu a tarihin dan Adam sai dai idan an kwatanta shi da sauran harkar annabawa da suka gabata, to ita harkarsa tana da fadi da yalwa da gamewa fiye da kowace, don haka ne zai zama ya zo da mafi girman juyin juya hali a dukkan tarihin dan Adam, kuma tabbas zai ci nasara.

2- Kamalar Halitta

Mahangar Shi'a game da karshen zamani kamar wani inji ne mai motsa tafiyar tarihi, kuma yana matsayin ruwan rayuwa ne a dukkan fagen rayuwar dan Adam domin tseratar da dan Adam da kubutar da shi daga hannun azalumai. Henri Kobon a tattaunawarsa da Allama Diba’diba’i yana cewa: Wannan ra’ayi ne wanda yake matsayin wani sabon abincin ruhi, kuma asasin karfi mai motsa rayuwar kyawawan dabi’u da kamalar dan Adam [2].

3- Daidaituwa Da Tsarin Rayuwa

Ra’ayin Shi'a game da karshen duniya ya yi daidai da abin da yake shi ne ginin musulunci da tsarinsa, shi al’amari ne da yake a matsayin dunkulewar duniya waje daya a kan tsari daya.

Musulunci addini ne na duniya gaba daya, bai kebanta da wasu jama’a ko wani waje ko wani zamani da ya kasance ya ginu a kan tsari ne na kabilanci, ko larabci, ko wani yanki, da bai yi daidai da akidar mahadiyyanci ba, don haka mahangar Shi'a game da karshen duniyar musulunci ya yi daidai a tsari, idan babu wannan to musulunci zai zama ya tawaya.

 4- Daidaituwa Da Dabi’ar Halittar Dan Adam

Abin da Shi'a suke cewa ya yi daidai da dabi’ar dan Adam, dukkan mutane duk inda suke, a kowane zamani, suna da nau’in halitta daya ne, kuma an halicce su daga kasa daya ne. Sannan suna da kamanni a wajan bukatu na jiki da na ruhi, suna da bukatu iri daya na dabi’ar halitta. Mahangar Shi'a ta kafu ne a kan wannan al’amarin, don haka ne ta zama mai saukin karba ga kowane mutum, domin musulunci da al’amarinsa na mahadiyyanci ya zo ne yana mai daidaita da sunnar rayuwa da samuwar dan Adam, kuma duk sadda aka samu daidaitar sunnar halitta, to dole ne ya zama ya samo asali daga musulunci ne [3]

5- Rashin Karo Da Juna

Shi’anci a cikin wadannan ra’ayoyi shi ne yake da mahanga da ba ta da tsara a cikinsu, kuma ba ta kunshe da magana mai karo da juna, kuma da daduwar ci gaban wayewa da ilimin dan Adam a nan gaba matsayin wannan mahanga zai dada karfafa sosai.

6- Bayani Dalla-dalla

Duk sa’adda wannan nazari ya zama dalla-dalla ya fi bayyana a fili. Don haka nazirin Shi'a game da karshen zamani ya fi kowanne bayyana, domin shi ne ya yi bayani dalla-dalla game da bayyanar Mahadi (A.S) ta hanyar kusan hadisai dubu 6 wanda Ahlussunna ma suna da ruwayoyi masu yawa a ciki. Kuma Shi'a sun bayar da amsar duk wata shubuha da ake jefawa game da wannan nazari, kuma da dogaro da dalili mai karfi ne suka yi raddin ra’ayin Kaisaniyya da Wakifiyya game da Mahadi.



1