Tauhidi



Tauhidi

Mun yi imani ya wajaba a kadaita Allah ta kowace nahya, kamar yadda ya wajaba a kadaita Shi a zatinSa,   kazalika Ya wajaba kadaita Shi a siffofi. Wannan kuwa saboda imani ne da cewa siffofinSa ainihin zatinSa ne kuma Shi a ilimi da kudura ba Shi da na biyu a halitta da arzutawa haka nan babu mai azirtawa sai shi  ba Shi da abokin tarayya, a cikin dukkan kamala kuma ba Shi da tamka.

Kazalika mun yi imani da kadaita Shi a bauta. Bai halatta a bauta wa waninSa ba ko ta wace fuska, kamar kuma yadda bai halatta ba a hada Shi da wani ba a cikin  nau'i na nau'o'in ibada, wajiba ce ko kuma wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma a wasu da ba ita ba na daga ibadoji.
Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to shi Mushiriki ne kamar kuma wanda yake riya a ibadarsa yana neman kusancin wanin Allah Ta'ala, hukuncinsa  wanda ya yi haka hukuncin wanda ya bauta wa gumaka ne babu bambanci a tsakaninsu.
Amma abinda ya shafi ziyatar kaburbura da kuma gudanar da bukukuwa, da suka shafi bayn Allah ba sa daga cikin nau'in neman kusanci ga wanin Allah (ibada) kamar yadda wasu daga masu son suka ga tafarkin Shi'a Imamiyya suke rayawa suna masu jahiltar hakikanin al'amarinsu. Sai dai ma wannan wani nau'i ne na kusanci ga Allah Ta'ala ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare Shi ta hanyar gaishe da marar lafiya, da raka gawa zuwa kabari, da ziyartar 'yan'uwa a addini, da kuma taimakon fakirida makamantansu.
Don haka zuwa gaishe da marar lafiya shi a kan kansa,  kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci ga Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci ba ne ga marar lafiyar. Da zai zamar da aikata wanann da niyyar  bauta,ya zama bauta ga wanin Allah Ta'ala ko kuma shirka a bautarSa. Kazalika sauran misalan kyawawan ayyuka irin wadannan wadanda a cikinsu har da ziyartar kaburbura, da gudanar da bukukuwa, da rakiyar gawa zuwa kabari da kuma ziyartar 'yan'uwa.Amma kasancewar ziyartar kaburbura da bukukuwan addini a matsayin kyawawan ayyuka a shari'a al'amari ne da fannin fikihu ke tabbatar da Shi ba nan ne gurin tabbatar da Shi ba.
Manufa ita ce cewa aikata irin wadannan ayyukan ba sa daga cikin shirka a ibada kamar yadda wasu suke rayawa kuma ba ma ana nufin bauta wa Imamai da su ba ne, abin nufin da su kawai shi ne  raya al'amarinsu, da kuma sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin addinin Allah da tare da su  Kamat yadda Allah yake fada a cikin kur'ani mai girma"wancan duk wanda ya girmama alamomin addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin takawar zukata." Surar Hajj: 32.

SiffofinSa Ta'ala

Mun yi imani cewa daga cikin siffofinsa Ta'ala akwai wajiban siffofi tabbatattu na Hakikanin kamala da ake kira siffofin jamal da kamal, wato kyawu da kamala, kamar ilimi da kudura, da wadata, da irada, nufi, da rayuwa wadanda su kansu su ne ainihin zatinSa, su ba siffofi ba ne kari ne dabam a kan zatinSa. Ainihin samuwarSa ba wani abu ba ne a kan zatinSa, kudurarSa kuma dangane da rayuwarSa, rayuwarSa ita ce kudurarSa, Shi mai kudura ne ta yadda Ya ke rayayye, kuma rayayye ta yadda Yake mai kudura, babu tagwaye tsakanin siffofinSa da samuwarSa, haka nan kuma a sauran siffofinSa na kamala.
Na'am siffofinSa sun sha bamban a ma'anoninsu da manufofinsu amma ba wai a hakikaninsu da samuwarSa ba saboda idan da sun kasance haka to da lalle Ya kasance an sami wajibabbun samammu da dama kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ba wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi.

Tabbatattun siffofi kamarsu halitta da arzurtawa kuwa, da gabatarwa, da kuma musabbabi duk alal hakika suna komawa ne ga siffa guda ta Hakika, ita ce kasancewarSa mai tafiyar da al'amuran bayinSa. Wannan ita ce siffa guda wadda siffofi da dama ke samuwa daga gare ta gwargwadon tasirori dabam-daban da kuma la'akari iri dabam-daban.
Amma siffofn da ake kira salbiyya wato korarru wadanda har wa yau ake kiran su siffofn Jalala, siffofi girma, su dukansu suna komawa ne ga siffa korarriya guda, wanda ita ce siffar kore kasancewarSa mai yiwuwar samamme ba wajibin samamme ba, ma'anarsa kore jiki gare Shi, da kore sura, da kore motsi, da kore rashin harka, da kore nauyi, da kore rashin nauyi, da dai sauran makamantansu, wato dai kore dukkan nakasa.
Sa'an nan kuma tushen kore kasancewarSa ba wajibin samamme ba-Shi ne kasancewarSa wajibin samamme, wajabcin samuwa kuwa na daga cikin siffofi tabbatattu na kamala, don haka siffofin Jalala korarru dai a karshe suna komawa ne ga siffofin kamala tabbatattu, Allah Ta'ala kuwa Shi kadai ne Makadaici ta kowace fuska, babu adadin yawantaka a zatinSa, babu kuma hauhawarwa a hakikaninSa makadaici abin nufi da bukata.
Abin mamaki ba zai kare ba ga maganar wanda yake da ra'ayin cewa siffofin tabbatarwa wadanda suke wajibai ga Allah duk suna komawa ne ga siffofin da suke korarru. Saboda haka ne Siffofin da suke korarru. Saboda Ya yi masa wahala ya fahinci cewa siffofinSa su ne ainihin zatinSa, don haka Ya kintata cewa siffofin subutiyya, tabbatattu wajibai ba sa koruwa ga Allah, duk suna komawa ga korarrun siffofi ne domin kawai Ya natsu da fadin kadaitaikar zati da rashin yawaitarsa sai kawai ya auka a cikin abinda ya fi shi muni, domin zamar da ainihin zati wanda shi ne samuwa, tsantsan samuwa, wanda ba shi da duk wata nakasa, da kore duk wata mafuskanta da ba ta dace da samamme wajibin samuwa ba, Ya sanya shi Ya aininin ma shi ne rashi kuma ainihin korarre, Allah Ya kiyayye mu daga tabewar wahamce-wahamce da kuma tuntubewar duga-dugai.
Kamar kuma yadda mamaki ba zai kare ba ga wanda ke da ra'ayin cewa siffofinSa na subutiyya, tabbatattu, kari ne a kan zatinSa, saboda haka wanzazzu suna da dama kenan, ya kuma wajabta abokan tarayya ke nan ga wajibin samamme, ko kuma kenan ya ce Shi mai hauhawa ne sashe bisa sashe.
Sayyyidina Ali Amirul Muminin (A.S.) kuwa Ya ce:
Cikar Ikhlasi gare Shi kuwa shi ne kore siffofi gare Shi saboda shaidar cewa dukkan abin siffantawa to ba shi ne siffar ba, da kuma shaidar cewa dukkan abin siffantawa ba shi ne siffar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi wanda ya tagwaita Shi kuwa ya zamar da Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi."

Adalcin Ubangiji.

Mun yi imani da cewa: Lalle daga cikin siffofin, Allah Ta'ala, As-Subutiyya Kamaliyya wato tabbatattun siffofin kamala akwai cewa Shi, Adali ne ba azzalumi ba, ba Ya karkacewa a hukuncinSa ba Ya tabewa a hukuncinSa, Zai yi sakayya ga masu biyayya, kuma yana gare Shi Ya hukunta masu sabo, ba Ya kallafa wa bayinsa abinda ba za su iya ba, ba zai musu ukuba fiye da abinda suka cancanta ba.

Kuma mun yi imani cewa Allah Ta'ala ba Ya barin abu mai kyau matukar ba gwamuwa ya yi da abu wanda shi ne mafi kyau ba kuma ba Ya aikata mummuna saboda Shi Allah Ta'ala Mai kudura ne a kan Ya aikata kyakkyawa Ya bar mummuna tare da kaddara saninSa game da kyawun kyakkyawa da kuma munin mummuna da wadatuwarSa ga barin kyakkyawan da kuma aikata mummunan. Babu wani kyakkyawan (aiki) da aikata shi zai cutar da Shi balantana Ya bukaci barin sa, babu kuma wani mugun aiki da yake bukatarSa ballantana Ya aikata shi kuma duk da haka Mai hikima ne babu makawa aikinSa Ya kasance ya dace da hikima kuma daidai gwargwadon tsari mafi kamala.
Idan har da zai aikata zalunci da kuma mummunan aiki -Shi Ya daukaka ga aikatawa- to da al'amarin hakan ba zai zamanto ya rabu da daya daga cikin surorin nan hudu:
1- Ya kasance Ya jahilci al'amarin bai san cewa mummuna ba ne.
2- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi amma kuma Ya zamanto Ya aikata shi ala tilas Ya gaza barin aikata shi.
3- Ko kuma Ya kasance Ya na sane da shi ba a kuma tilasta Shi Ya aikata ba bai kuma gaza kin bari ba amma Ya zamanto Yana bukatar aikatawa.
4- Ko kuma Ya kasance Yana sane da shi, ba mai aikata shi ala tilas ba, ba kuma mai bukata Ya zama Ya takaita ke nan da aikata shi a bisa sha'awa da wasa da bata lokaci.
Dukan wadannan surori kuwa sun koru ga Allah Ta'ala, Kuma tabbatar da nakasa gare Shi alhali Shi kuwa zallan kamala ne saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa Shi tsarkakakke ne daga zalunci da kuma aikata abinda yake mummuna.
Sai dai kuma wani bangare daga cikin musulmi sun halatta wa Allah Ta'ala aikata mummuna[1], sunayenSa sun Tsarkaka, suka halatta cewa zai iya hukunta musu biyayya, Ya kuma shigar da masu sabo aljanna kai hatta katirai ma, kuma suka halatta cewa Yana iya kallafa wa bayinSa abinda Ya fi karfinsu da abinda ba za su iya aikatawa ba amma kuma duk da haka Ya azabtar da su idan har suka bari ba su aikata shi ba. Har ila yau kuma sun halatta zalunci na iya faruwa daga gare Shi da tabewa, da karya da yaudara, kuma Ya aikata aiki ba tare da wata hikimaba, ba da manufa ba, ba da amfani ba, ba da fa'ida ba da hujjar cewa "Ba a tambayar sa a kan abinda yake aikatawa su kuwa ana tambayar su." Surar Anbiya: 23.
Da yawa daga cikin irin wadannan da suka suranta Shi a kan wannan akida tasu batacciya da cewa Shi, Azzalumi ne, mai Ja'irci, mai wauta ne, mai wasa ne, mai karya ne, mai yaudara ne, Yana aikata mummuna, Yana kuma barin kyakkyawa, Allah Ya daukaka ga aikata wadannan abubuwa, daukaka mai girma, wannan shi ne kafirci tsantsansa. Kuma Allah Ta'ala Ya ce:

"Kuma Allah ba Ya nufin Zalunci ga bayi." Surar Mumin aya ta 23. "Kuma Allah ba Ya son barna." Surar Bakara: 31 "Kuma ba mu halitta sammai da kasa da abinda ke tsakaninsu muna Masu wasa ba." Surar Dukhan: 205. "Kuma ban halitta Aljannu da Mutane ba face don su bauta Mini." Surar Zariyat: 56.

Mazhabar Ja'afariyya wato Shi'a Isna Ashariyya ta dauki adalci a matsayin jigo daga cikin ginshikan addini sai dai kuma alal hakika shi ba ginshiki ne guda shi kadai mai zaman kansa ba sai dai shi yana kunshe ne a cikin siffofin Allah Ta'ala kuma wajabcin samunsa ya lizimta tattara siffofin kyawu da kamala saboda haka shi dai adalci yana daga cikin al'amuran tauhidi ne. Sai dai kuma su Asha'irawa da suka saba wa Adaliyyawa, wato Mu'utazilawa da kuma `yan Ja'afariyya, Shi'a Isna Ashariyya sai suka musa abu mai kyau da kuma mummuna wadanda hankali ya tabbatar da su. Suka ce babu wani abu mai kyau sai wanda shari'a ta ce mai kyau ne, babu mummuna kuma a sai wanda shari'a ta ce mummuna ne kuma cewa idan da Allah zai dawwamar da mai biyayya a gidan wuta mai sabo kuma a gidan aljanna to wannan ba mummuna ba ne saboda yana jujjuya al'amura ne da ke karkashin mulkinSa kuma kamar yadda Alkur'ani ya ce: "Ba a tambayarSa a kan abinda ya aikata su kuwa ana tambayar su" Surar Anbiya'i aya ta 23. Su kuwa Adaliyyawa kuwa cewa suka yi: Mai yanke hukunci a wannan al'amari shi ne hankali shi kadai dinsa, babu abinda zai shigar da shari'a a cikinsa sai dai karin ta'akidi da kuma shiryarwa. Shi kuma hankali ya kebantu da hukunta kyawun wasu ayyuka da hukumta munin wasu kuma yana hukumta cewa danganta mummunan abu ga Allah abu ne da ba shi da kyau kuma ba zai yiwu ba Allah Ya aikata shi domin Shi Mai hikima ne azabtar da mai biyayya kuwa zalunci ne; zalunci kuwa mummunan abu ne kuma ba zai taba faruwa daga Allah Ta'ala ba.
Da haka ne suka tabbatar da siffar Adalci ga Allah suka kebance ta da ambato banda sauran siffofn don ishara ga sabani da Asha'ira. Su kuwa Adaliyawa ta hanyar ka'idar kyakkyawa da mummuna kamar yadda suke a hankali sun tabbatar da wasu ka'idoji daga ka'idojin ilimin sanin Allah: Kamar su Ka'idar Tausasawa, da kuma Wajabcin godiva ga wanda ya yi alheri da wata ni'ima, da kuma wajabcin bincike da nazari a mu'ujiza, kuma a kan wadannan ka'idojin suka gina al'amari tilasta wa da kuma `yancin zabi da ke daga cikin mafi wahalar matsaloli.
Domin karin bayani a duba: Aslus Shi'a da kuma Matarihun Nazar na Shaikh Turaihi, Fasali na 4 shafi na 164.


[1] - Da dai sauran wadannan da Asha'irawa suka tafi a kai na daga maganganunsu na cewa Allah Ta'ala Ya aikata mummuna da maimaitawarSa na nau'o'in zalunci da shirka da dagawa da ketare haddi da kiyayya da yarda da su ya kuma so su -Allah Ta'ala Ya daukako ga haka, Tsarki ya tabbata gare Shi-, domin kara samun filla-fillan wadannan munanan ra'ayoyi'a duba littafi Nahjul Hak na Allama Hilli shafi na 85, da kuma sharhin Aka'ida da kuma Hashiyar na kistal, shafi na 109-113, da Milal wan Nahal Juzu'i 1 shafi na 85, 91 da kuma Al- Faslu na Ibin Hazm Juzu'i na 3 shafi na 66 da 69 da kuma Sharhit Tajrid na Kurshaji shafi na 373.



1