Musulunci



Musulunci

Mun yi imani cewa lalle addini a gurin Allah kawai shi ne Musulunci kuma shi ne Shari'ar Ubangiji ta gaskiya wadda ita ceShari' ar karshe kuma ita ce mafi kamala kuma mafi dacewa ga alherin bil Adama, ita ce ta fi kunsar maslaharsu ga al'amuran duniya da lahira, ita ce mafi dacewa duk tsawon zamani ba ta canjawa ba ta sakewa. kuma matattara ce ga dukan abinda Dan Adam yake bukata daga tsarin rayuwar daidaiku da halin zaman jama'a da na siyasa.

Da yake Shari'ar Musulunci ita ce ta karshe, kuma ba ma jiran wata shari'a da za ta zo ta yi gyara ga dan Adam da ya rigaya ya dulmuya cikin zalunci da fasadi, don haka babu makawa wata rana ta addinin Musulunci ya yi karfi har ya game rayuwa da adalcinsa da dokokinsa.

Idan da angudanar da Shari'ar Musulunci da dokokinta a bayan kasa daidai wa daidai yadda ya dace to da addinin Musulunci ya game tsakanin ‘yan Adam kuma da alheri ya game su, kuma da sun kai kololuwar abinda dan Adam ke mafarkinsa na daga daukaka da sa'ada da ginuwa da halin kwarai, kuma da zalunci ya kwau duniya. soyayya da 'yan'uwantaka, kuma da talauci da fatara da miyata sun kare baki daya.

Koda a yau muna ganin halin ban kunya da ketare hakki daga gurin wadanda ke kiran kansu musulmi dalili shi ne kawai cewa ba a aiwatar da musulunci a aikace ba a hakikaninsa tun daga karni na farko kuma muka ci gaba a cikin wannan hali mu da muke kiran kanmu musulmi, daga mummuna hali zuwa wanda ya fi shi muni har zuwa yau din nan da muke ciki. Sai dai kuma ba wai riko da Musulunci ko aiki da shi ne ya jawo wa Musulmi wannan jinkiri ba sai dai ma akasin haka, wato kangare wa koyarwar Musulunci da tozarta dokokinsa da yaduwar zalunci da ketare haddi daga bangaren Sarakunansu da talakawansu da kebantattu da kuma baki dayansu, Shi'ansu da Ahlussunnansu. Wannan shi ne abinda ya lahanta yunkurin ci gaba, ya raunana karfinsu, ya ruguza tsarkin ruhinsu, ya jawo musu bala'i da halaka har Allah ta'ala Ya halaka su saboda zunubinsu. Allah Ta'ala Yana cewa:

"Wannan kuwa domin lalle Allah bai kasance Yana canja wata ni'ima da Yani'imtar da ita a kan wasu face sun sauya abinda ke zukatansu ne kuma lalle Allah mai Ji ne masani." Surar Anfak 53.

Wannan itace sunnar Allah a halittunSa "Cewa lalle tabbas masu laifi ba sa cin nasara." Surar Yunus: 17.

"kuma Ubangijinka bai kasance yana halaka Alkaryu saboda wani zalunci ba alhali mutanensu suna masu gyara." Surar Hudu: 117.

"Kuma haka nan kamun ubangijin ka yake idan Ya kama alkarya alhali tana azzaluma lalle kamunsa mai zafi ne mai tsanani." Surar 1-1udu: 102.

Ta yaya za a tsammaci addinin musulunci ya daga al'umma daga dogon barcinta alhali kuwa tana da Alkalami da tawada ba ta amfani da mafi karanci daga koyarwarsa. Lalle imani da amana da gaskiya da ikhlasi tsarkin niyya, da kyautata mu'amala, sadaukarwa, da kuma cewa musulmi ya so wa dan'uwansa musulmi abinda yake sowa kansa da makamantansa duk suna daga asasan addinin Musulunci na sahun farko farko kuma musulmi sun yi ban kwana da su har muka kare ga halin da muke ciki a yau duk lokacin da zamani ya kara nisa sai mu kara jama'a-jama'a daban daban da kungiyoyi suna kifuwa a kan duniya suna ta fagamniya a cikin duhu, sashensu na kafirta sashe da wasu ra'ayoyi gagara fahimta ko kuma a kan wasu al'amura da ba su dame su ba, suka mance da ainihin addini, suka bar maslaharsu da maslahar jama'a suka shagala da jayayya a kan al'amura kamar su halitta Alkur'ani ko rashin kasancewarsa halittacce, da batun alkawari game da azaba da raja'a, da kuma cewa Aljanna da wuta halittattu ne a halin yanzu ko kuma za a halitta su ne nan gaba. Makamantan wadannan gardandamin wadanda suka rike musu wuya, wasunsu suka kafirta wasunsu da ita babu abinda suke tabbatarwa illa kawai kaucewar musulmi da madaidaicin tafarkin da aka riga aka gyara zuwa ga halaka da karewa.

Fandarewar ta karu kuma tare da shudewar zamani har ta hada da Jahilci da bata suka dukufa a kan aibobi da sabani a kan al'amura da surkulle da wahamce-wahamce tare kuma da yake-yake, da jayayyar rikitarwa Wannnan shi ne abinda ya sa suka auka a cikin halakar da ba ta da iyaka. A yau Yammacin Turai babban sanannen makiyin mlusulunci har sun iya sun yi mulkin mallaka a kan wani yanki da yake na musulmi su kuwa sun yi zamansu cikin gafala da rafkanwya yadda har Yammacin Turai din na iya jefa mummunm halin da Allah ne kadai Ya san iyakarsa da lokacin karewarsa. Allah Ta'ala Yana cewa: "Kuma ubangijin ka bai kasance yana halaka Alkaryu saboda wani zalunci ba alhali mutanensu suna masu gyara." Surar Hudu: 117.



1 2 3 next