Tashin kabari da tashin kiyama



Kuma idan yin imani da Aljanna da wuta wajibi ne to ba ya zama lalle a san da samuwarsu a halin yanzu da kuma sanin cewa suna sama ne ko suna kasa ko kuma sun saba.

kazalika idan sanin ma'auni ya zama wajibi to ba wajibi ba ne a san cewa ma'aunin na a surance ne ko kuwa yana gurin gwada nauyi ne biyu.

Kuma ba lazimi ba ne a san cewa siradi jiki ne siriri ko kuwa tsayuwar daka ce surantawa. Kuma manufar dai ita ce cewa ba sharadi ba ne a yi binciken hakikan cewa don sanin cewa da jikkuna ne ko a'a..."  Na'am wannan      akidar tashin kiyamar da saukin da take tare da shi ita ce wadda musulunci ya zo da ita, idan mutum ya so ya ketere shi kuwa filla-filla sosai fiye da yadda ya zo a Alkur'ani domin ya gamsar da kansa don kore shakkun da masu bincike ke tayarwa ta hanyar dalilan hankali ko kuma gwajin bincike to lalle yana wahalar da kansa ne kawai, kuma zai fada a cikin mushkiloli da rikice-rikice da jayayya marar iyaka.

A addini babu adinda ke kira zuwa ga wannan zurfin binciken da littafan masu bincike game da Akida da malaman falsafa, kuma babu wata larurar addini ko ta zamantakewa ko siyasa da ke kira zuwa ga irin wadannan rubuce-rubucen da makalolin da ke cike da littafan haka nan a wasa, da kuma wadanda suka kare karfin da kokarin masu jayaya da karfinsu da lokutansu da tunaninsu ba tare da fa'ida ba.

Mushkiloli da shakkun da ake tasowa da su game da filla-fillansu ya wadatar wajen raddinta mu yi imani da gazawar mutum game da fahintar wadannan al'amura boyayyu daga gare mu, da kuma wadanda suke sama da fahintarmu da samuwarmu, wadanda suka dara matsayinmu na kasa, tare da sanin cewa Allah Ta'ala mai iko ne a kan Ya ba mu labarin hakikanin aukuwar Tashin kiyama da tashin kabari.

Sanin dan adam da gwaje-gwajensa da bincike-bincikensa ba zai yiwu su tabo wani abu da ba a san shi ba su sanya shi a karkashin gwajinsu da kwarewarsu ba sai dai bayan mutuwarsa da ficewarsa daga wannan duniya ta majiyan jiki da gwaje-gwaje da bincike, to yaya za'a sa rai ya yi hukunci da 'yancin tunaninsa, da kwarewarsa wajen kore wannan abu ko tabbatar da shi? Ballantana ma game da filla-fillansa da kebantattun al'amuransa sai dai idan ya dogara a kan bokanci da dikake da al'ajabi da ban mamaki kawai kamar yadda yake a dabi"ar sake-saken zuciyar mutum ya yi mamakin duk abinda bai saba da shi ba bai sami iliminsa da fahintarsa, kamar wanda ya kore yiwuwar tashin Alkiyama da jahilcinsa yana mamaki da al'ajabin tashin kiyama da fitowa daga kabari yana cewa: "Wane ne zai tayar da kasusuwa alhali Suna rididdigaggu."

Babu wata madogara ga wannan mamaki sai dai kawai shi bai ganin matacce rididdigagge ba wanda aka koma da shi rayuwa sabuwa. Sai dai kuma ya manta yadda aka halitta shi a karo na farko ne, da ya kasance babu shi, gabobinsa da yankunan jikinsa riddidigaggu daga yankunan kasa da abubuwan da ta kunsa, da kuma a cikin iska a warwatse nan da can aka harhado shi har ya zama mutum daidai mai hankali; "Shin shi mutum ba ya gani ne mu mun halitta shi daga digon maniyi sai ga shi yana mai husuma bayyananne. Kuma ya ba mu misali Ya mance halittarsa."

Mai irin wannan maganar sai a ce masa: "Zai raya shi, wannan da Ya fare shi a karo na farko kuma shi masani ne game da dukan halitta." Kuma a cemasu: Kai lalle bayan ka san mahaliccin halittu da kudurarsa kuma ka san Manzo da abinda ya ba da labari game da shi.

tare da karancin saninka hatta ma fahintar sirrin halittarka da sirrin samar da kai da kuma yadda ka girma da kuma yadda ka fita daga marhalar digon mani da ba ya jin kome ba ya da hankali zuwa marhalolin da ke biye da ake tattaro daga kwayoyi manesanta, domin ka zamanto mutum daidaitacce mai hankali mai tuntuni mai ji na jiki da maganai.'"

Bayan wannan kuma sai a ce masa ta yaya kake mamakin komo da rayuwa sabuwa bayan zamantowa rididdigagge, kana kokari da haka ka kai ga abinda kwarewarka ka da iliminka suka yi kadan wajen gano shi.

Sa'an nana ce masa ba ka da wata mafita illa ka mika wuya kana mai ikrari game da wannan hakika wadda mai tafiyar da halittu masani mai kudura game da ita, kuma mahaliccinka daga babu kome da kuma abubuwa rididdigaggu. Ya bada labari kan duk wani kokari na binciko abinda bai gano shi ba, kuma iliminka ba zai kai gare shi ba, to kokari ne kawai na  banza, da buga ­buga a cikin rudu, da bude ido a cikin duhu mai halakarwa kawai.

Shi mutum duk da irin abinda ya kai gare shi na ilimi da shekarun nan na karshe, Ya kago lantarki, da rada, wato na'urar hangen nesa, da masaniyar amfani da makamin kare dangi da dai sauran irin wadannan kage-kagen da suka auku a shekarun baya-bayan nan wadanda idan da an ba da labarinsu a da can to da an kidaya su a cikin abubwyan da ba za su yiwu ba ya yi watsi da su ya wawaitar da su to har yanzu mutum bai san hakikanin wutar lantarki ba da sirrin kwayar zarra, kai hatta ma hakikanin daya daga cikin abubuwan da suka kebanta da su da siffofinsu, to yaya zai ji tabbacin gano sirrin halitta da samuwa, sa'annan ya kara gaba yana so ya san sirrin tashin kiyama da tashi daga kabari.

E, haka ne, ya kamata ga musulmi bayan ya yi imani da musulunci Ya nesanci bin son zuciya kuma Ya shagaltu a kan abinda zai gyara al'amarinsa na duniya da Lahira da kuma abinda zai daukaka masa matsayinsa a gurin Allah, kuma ya yi tunani a kan abinda zai taimake shi a kan son ransa da kuma abinda zai fuskanta bayan mutuwa na daga tsananin kabari da hisabi bayan hallara a gaban mai Mulki masani, kuma ya ji tsoron "wata rana da wani rai ba ya wadatarwa wani rai kome kuma ba a yarda da ceto gare shi, kuma ba a karbar fansa gare shi kuma ba a taimakon su."bakara :48.

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.

 



back 1 2