Raja'a –komowa-



Raja'a –komowa-

Abinda Mazhabar Ja'afariyya -Imamiyya take kai- tare da riko da abinda ya zo daga Ahlul Bait (A.S.) Shi ne cewa Allah Ta'ala zai komo da wasu mutane daga cikin wadanda suka mutu zuwa, duniya a bisa kamanninsu da suka kasance a kai, zai daukaka wasu kana kuma zai kaskantar da wasu, kana zai rarrabe masu gaskiya daga cikinsu daga marasa gaskiya, da wadanda aka zalunta daga azzalumai, wannan zai auku ne bayan bayyanar Mahadi daga zuriyar gidan Manzon Allah mafifita tsira da aminci su tabbata a gare su.

Ba mai dawowa sai wandadarajarsa ta imani ta daukaka, ko kuma wanda ya kai kololuwa a barna. Bayan nan kuma sai a mutu daga nan kuma sai zuwa tashin Alkiyama zuwa ga abinda suka cancance shi na kyakkyawan sakamako ko kuwa ukuba, kamar yadda Allah Ta'ala Ya kawo a cikin Alkur'ani mai girma game da burin da wadanda suka komo din ke yi, wato wadanda ba su gyaru ba da komowarsu, don haka suka sami ukubar Allah kan cewa a dawo da su zuwa na uku ko sa gyaru;

"Suka ce Ya Ubangijinmu ka matar da mu sau biyu kuma ka rayar da mu sau biyu to mun yi ikrari da zunubanmu shin akwai wata hanyar fita." Surar Mumin: 11.

Na'am Alkur'ani ya zo da yiwuwar komowa zuwa duniya hadisai da dama kuma daga Ahlul Bait (A.S.) suka zo a kan haka, mabiya Mazhabar Ja'afariyya ko kuma Imamiyya sun yi ittifaki a kan haka sai dai 'Yan kalilan daga cikinsu da suka yi tawilin abinda ya zo game da raja'a da cewa Ma'anarta ita ce komowar hukuma da Umarni da hani ga Ahlul Bait da bayyanar lmamin da ake .jira (A.S.) ba tare da komowar wasu ayyanannu ko raya matattu ba.

Batun raja'a kuwa a guriu Ahlus Sunna yana daga cikin abin ki wanda imani da shi Ya munana, kuma marubutansu a ilimin sanin maruwaitan hadisai suna kirga imani da raja a  matsayin suka ga mai ruwaya da kuma abin kiyayya gare shi wadda ke wajabata kore ruwayarsa da watsi da ita, kuma ya bayyana cewa suna kirga ta a matsayin kafirci da shirka, har ma tafi muni don haka wannan na daga cikin mafi girman abubuwan da suke sukan Shi'a Imamiyya da shi da kiyayya da su a kansa.

Babu  shakka wannan duk wata mafaka ce kawai da bangarorin kungiyoyin musulunci da can suka kasance suna riko da ita don sassansu su soki sashe da shi, kuma alal hakika mu ba mu ga wani abu da zai halatta wannan mafakar ba domin imani da raja'a ba ya soke imani da tauhidi kuma ba ya soke imani da Annabci bilhasali ma kara inganta abu biyun yake yi domin raja'a dalili ne a kan kudurar Allah cikakkiya tamkar dai tashin alkiyama da tayar da mamata. shi alkiyama da tayar da mamata suna daga cikin abubuwan da suka saba wa al'ada wadanda ya inganta ta Mu'ujiza ga Annabinmu Muhammadu (SAW) da zuriyar gidansa. Kuma ita raja'a tamkar mu'ujizar raya matattu ce wadda ta kasance ga Annabi Isa (A.S.)  sai dai tafi ta cika a nan domin wannan za ta zo ne bayan mamata sun zama rididdigaggu.

"Ya cewane ne zai raya kasusuwa alhali sun zama rididdigaggu? Ka ce zai raya su wannan da ya fare su karon farko kuma shi game da dukan halitta masani ne." Surar Yasin:79-87.

Amma wandaYa soki raja'a kuwa da dalilin cewa tana daga shafewa batacciya to lalle bai fahimci bambanci tsakanin "tanasuhi'" da kuma ainihin tayar da mamata da ainihin jikinsu ba. ita raja'a wani nau"i ne na tayar da mamata da ainihin jikinsu domin ma'anar tanasuhi ita ce kauratar da rai daga wani jiki zuwa wani jikin daban da ba na farko ba, ma'anar tayar da matattu da ainihin jikkunansu kuwa ba haka take nufi ba, ma'anarsa ita ce komo da ainihin jikin da ainihin abubuwan ransa da suka kebantu da shi, haka nan ma raja'a take.

Idan kuwa har aka ce "Raja'a" "Tanasuhi" ce to raya mamata da Annabi Isa (A.S.) ma ya kasance yana yi "tanasuhi" ce to tayar da mamata da komo da ainihin jikkunan mamata ma '`tanasuhi'' ne ke nan, saboda haka babu abinda ya saura illa Muhawara ta fuska biyu game da "Raja'a".

(1) Na farko: Korarriya ce sam ba za ta auku ba.



1 2 next