Ja'irci da Zalunci



Mafi zurfi game da haka kuma da suranta haramcin taimakekeniya game da azzalumai shi ne maganar safwan jammal tare da Imam Musa Kazim (A.S.) wanda Shi ya kasance daga cikin mabiyan Imam din ne, masu ruwaito hadisi daga gare shi wadanda aka amince da su Ya ce: kamar Yadda ya ruwaito a littafinsa na Ilimin sanin masu ruwaya kamar yadda yake bayanin rayuwar Safwan:

Na Shiga gare shi sai ya ce mini: "Ya Safwan duk wani abu daga gare ka kyakkyawa ne mai kyau in banda abu guda daya."

Na ce: A sanya ni fansa gare ka, wane abu?

Ya ce: "Ba da hayar rakumanka ga wannan mutumin wato Harunar Rashid.

Na ce: Wallahi ni ban ba shi haya ba ina mai alfahari ko dagawa ko don farauta, ko wasa, sai dai na ba shi haya ne don wannan tafarkin  wato don hanyar Makka kuma ba na daukarsa ni da kaina sai dai ina tura shi da barorina.''

Ya ce: "Ya Safwan kudin hayarka na kansu?"

Na ce: E, a sanya ni fansa gare ka.

Ya ce: "Shin kana so su wanzu har su dawo su biya ka kudin hayarka?"

Na ce: "E".

Ya ce: "To duk wanda ya so wanzuwarsu to yana tare da su, duk wanda ya kasance tare da su to ya kasance mai shiga wuta."

Safwan ya ce: "Sai na tafi na sayar da dukan rakumana baki daya."

Idan har son rayuwar azzalumai da wanzuwarsu a kan wannan matsayin yake, to yaya kuma ga wanda yake hada kai da su a kan zalunci, ko kuma yake taimaka musu a kan ja'irci, kuma yaya halin wanda yake shiga cikin jama'arsu ko kuma yake aikinsu ko kuma yake shiga tawagarsu, ko kuma yake bin umarninsu?

Aiki a hukuma Azzaluma

Idan har taimakekeniya da azzalumai daidai da rabin dibino, kai hatta ma son wanzuwarsu na daga cikin abubuwa masu tsanani da lmamai (A.S.) suka yi gargadi game da su to mene ne kuma halin tarayya da su a cikin hukunci da kuma shiga cikin aikinsu tare da su da amintuwa da ja gorancinsu.

Yaya halin wanda ya kasance daga cikin wadanda suka assasa musu hukumarsu, ko kuma wanda ya kasance daga cikin wadanda su rukunan shugabacinsu ne wadanda suka dulmuye cikin karfafa hukuncinsu kuma wannan saboda karbar shugabancin azzalumi rusa gaskiya ne dukkaninta kuma raya karya ne dukkaninta kuma bayyana zalunci ne da ja'irci da fasadi, Kamar yadda ya zo a hadisi a "Tuhful uku1" daga Imam Sadik (A.S.) Sai dai kuma ya zo daga gare su (A.S.) halaccin yarda da Shugabancin Ja'irai idan a ciki akwai kiyaye adalci, da tsayar da haddin Allah da kyautatawa ga muminai, da yin umarni da mai kyau da hana ayyuka munana, "A kofofin azzalumai Allah na da wadanda Allah Ya haskaka su da hujjoji, ya ba su iko a kasashe, kuma Y'ana kare waliyanSa da su, kuma Yana gyara al'amuran musulmi da su... Su wadannan muminai ne na hakika su wadannan manarorin Allah ne a bayan kasa wadannan hasken Allah ne a cikin ababan kiwonsa..." kamar yadda ya zo a hadisi daga Imam Musa Bin Ja'afar (A.S.)

 A wannan Babin akwai hadisai da dama, wadanda ke bayyana tafarkin da ya kamata shugabanni da masu aiki ya kamata su tafi a kai, kamar abinda ya zo a wasikar Imam Sadik (A.S.) ga Najjasi Shugaban ahwaz (A duba Al- Wasa'il Kitabul Bay'i Babi na 78." 

Hafizu Muhammad Sa’id Kano Nigeria.

 



back 1 2 3