Hakkin Musulmi



Sai na ce masa: A sanya ni fansa gareka! Mecece?

Sai ya ce: Ya Mu’ula ni ina mai tausasa wa gareka, ina tsoron ka tozarta ba za ka kiyaye ba, ko kuma ka sani ba za ka aikata ba.

Na ce: Babu karfi sai da Allah.

Yayin nan sai Imam (A.S) ya ambaci hakkoki bakwai, bayan ya fada game da na farkonsu cewa: “Mafi saukin hakki daga cikinsu shi ne ka so wa dan’uwanka kamar yadda kake so wa kanka, ka kuma ki masa abin da kake ki wa kanka”.

SubhanalLahi! Wannan shi ne hakki mai kankanta, to yaya wannan hakkin mafi kankanta yake a gare mu yau mu musulmi? Kaicon fuskokin da suke da’awar musulunci amma ba sa aiki da mafi kankantar abin da ya wajaba na daga hakkokinsa. Abu mafi ban mamaki kuma shi ne, a dangata wannan rashin ci gaban da ya samu musulmi ga Musulunci, alhalin laifi ba na kowa ba ne sai na wadanda suke kiran kansu musulmi amma ba sa yin aiki da mafi karancin abin da ya wajabta musu da su yi aiki da shi na koyarwar addininsu.

Domin tarihi kawai, kuma don mu san kawukanmu da takaitawarta zamu ambaci wadannan hakkoki bakwai wadanda Imam (A.S) ya bayyana su:

l- Ka so wa dan’uwanka musulmi abin da kake so wa kanka, kuma ka ki masa abin da kake ki wa kanka.

2- Ka nisanci fushinsa, ka bi yardarsa, ka kuma bi umarninsa.

3- Ka taimake shi da kanka, da dukiyarka, da harshenka, da hannunka, da kafarka.

4- Ka zamanto idonsa, dan jagoransa, kuma madubinsa.



back 1 2 3 4 next