Yammacin duniya



Daganan sai shugabanna Jamus ya bayyana cewashi bai san Musulunci yaddaya kamata ba sai bayanda ya karanta littafan wannan Mustashrika mai adalci (wato Shamel) saiya ce:­

"Tsinkayata ga irin wannan babban nau'ina fuskance-fuskancecikin tarihin Musulunci da hakikaninsa a halin yanzu bai faraba sai tahanyar littafan Anamari Shamel, akwai kyakkyawan zaton kuma cewawasu irina ma sun fuskanci irin wannangwaji hakika muna bukatar musanyaabin da ya kuke mana nafahimtar sashinmu ga sashi".

Sannan sai shugaban na Jamus yayi kira da a fahimci Musulunci don shata wani matsayi game da shi koma bayan matsayinda ya ginu a kan jahiltar sa yana mai cewa:­

"Ina yin ikirari da cewa a gabanmu babu wanizabi face kara samun masaniya game da duniyar Musulmi matukar muna nufinyin aiki don kare hakkin dan Adam da Dimokuradiyya".

Sai kuma ya kara da cewa:­

"Babban dalilin son sanin Musulunci da fahimtar wadatacciyar wayewar nan ta shi ya samo asali ne daga kasancewarmu cikin wata wayewa da ba shi ba. Hakika kuwa uwargida Shamel ta fadaka da wannan bukata ta rai, ina fata kuma wannan ya zama shi ne yadda wasuna masu yawa ke ji..".

"kuma Uwargida Anamari Shamel ta share mana fagen haduwa da Musulunci."

Haka  wannan rikici na bayar da kyautar zaman lafiya a kasar Jamus ga masaniyar kasashe da al'adun Musulmi (Shamel) a shekara ta 1995 ya kasance, tare da yardar `yan siyasa da wayayyu daga ma'abuta tunani, shehunnan malamai, Turawa masana kasashen Musulmi da al’adun Musulunci, ma'abuta fanni da adabi a kasar Jamus, wadda ake dauka daga cikin manyan daulolin duniya a tarihin wannan zamani namu da nasarar bangaren Shamel wato masu kira zuwa a fahimci Musulunci a bisa hakikaninsa don shata matsaya.

Daga cikin wadanda ke sahun gaba kuwa har da manazarta da 'yan siyasa, a cikin su har da shugaban kasar Jamus wanda muka karanta muhimman zantuttukansa  duk yana nuna mana wani abu ne mai girma daga abubuwan da ke wuyan Musulmi marubuci, manazarci kuma ma'abucin fanni da adabi kamar yadda ya ke wuyan cibiyoyi da malaman addini, wannan kuwa shi ne nauyin yin bayanin Musulunci a bisa hakikaninsa wanda yake tafiya tare da hankali ta hanyar aiki da tafarkin nan na AIkur'ani wajen kira zuwa ga Allah Madaukaki.

Nasarar masu kira zuwa ga fahimtar Musulunci yana tabbatar mana da girman Musulunci da shirin da dan Adam ke da shi na fahimta da karbar Musulunci duk kuwa yadda ya kai da isa. Wannan ka'ida ce da AIKur'ani ya tabbatar da ita da fadarsa:­

"Ku tafi zuwa ga Fir'auna don kuwa hakika ya yi tsaurin kai. Sannan ku gaya masa magana mai taushi, ko watakila zai karbi gargadi ko kuma ya ji tsoron (azabar Allah)".          Surar Daha, 20:43-44.

 Daga nan za mu fahimci cewa Alkur'ani na horon masu kira zuwa ga Musulunci da su kare tunanin imani kuma su yi magana ta Musulunci hatta ga wadanda suka fi kowa adawa da tsanantawa da kin imani kuma kar su fada tarkon yanke kauna har su rufe kofar yin muhawara ta tunani domin yanayi da halayen da ba a karbar zantukan Musulunci a cikinsu suna da sabani daga wata marhala zuwa wata kuma daga wani yanayi na zamantakewa, al'adu, da tarihi zuwa wani, domin da saudayawa  abin da aka ki karba a yau aka karbe shi a gobe  kuma abin da aka ki yarda da shi ta wannan hanya ana yarda da shi ta wata hanyar.

Hafizu Muhammad Sa’id Kano geria.

 



back 1 2