Alamomin Soyayya Don Allah



Wanzuwar Soyayya Zuwa Ranar Kiyama

Littafi:

“Masoya a wannan ranar sashensu makiya ne ga sashe, sai masu takawa”[6].

Hadisai:

377. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Idan ya kasance ranar kiyama duk wata zumunta zata yanke, kuma nasaba ta yi karanci, kuma ‘yan’uwantaka ta tafi sai ‘yan’uwantakar da take saboda Allah, wannan ne fadinsa madaukaki: “Masoya a wannan ranar sashensu makiya ne ga sashe, sai masu takawa”[7].

378. Tafsirin kummi, daga haris, Daga Imam Ali (A.S) ya fada game da abokai biyu muminai da kuma abokai biyu kafira…: amma abokai biyu muninai sai suka yi abotaka a rayuwarsu a cikin bin Allah, kuma suka kashe rayuwarsu a kanta, kuma suka yi soyayya a kanta, sai dayansu ya mutu kafin dayan, sai Allah ya nuna masa matsayinsa a aljanna yana mai ceton abokinsa, sai ya ce: ya Ubangiji abokina wane ya kasance yana umarta ta da bin ka, kuma yana taimako na, yana hana ni sabonka, ka tabbatar da shi a kan abin da ka tabbatar da ni a kansa na shiriya har sai ka nuna masa abin da ka nuna mini. Sai Allah ya amsa masa game da shi, har sai ya hadu da shi wajen Allah sai kowanne ya ce da abokinsa: Allah ya saka maka da alheri madalla da abokin kirki, ka kasance kana umarta ta da bin Allah, kana hana ni sabon Allah.

Amma kafirai biyu sai suka yi soyayya a kan sabon Allah, kuma suka bayar da rayuwarsu a kan hakan, sai dayansu ya mutu kafin dayan, sai Allah madaukaki ya nuna masa matsayinsa a wuta, sai ya ce; ya Ubangiji abokina wane ya kasance yana umarta ta da saba maka, kuma yana hana ni biyayyarka, ka tabbatar da shi a kan abin da ka tabbatar da ni a kansa na sabo har sai ka nuna masa abin da ka nuna mini na azaba. Sai su hadu gun Allah ranar kiyama kowanne yana cewa da sahibinsa: Allah ya yi wadaranka abokin banza, ka kasance kana umarta ta da sabon Allah kuma kana hana ni biyayyar Allah. Ya ce: sannan sai Imam Ali (A.S) ya karanta wannan ayar: “Masoya a wannan ranar sashensu makiya ne ga sashe sai masu takawa”[8].

3 / 5

Ceton Daga Manzon Allah (S.A.W)

379. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Ni mai ceto ne ga dukkan mutane biyu da suka yi ‘yan’uwantaka saboda Allah tun daga ranar aiko ni har zuwa ranar kiyama[9].

3 / 6

Yawan masu Ceto

Littafi: “Ba mu da masu ceto; Ko wani aboki masoyi;”[10].



back 1 2 3 4 5 next