Yan’uwantaka Don Allah



Muminai ‘Yan’uwa Ne kamar Jiki Daya

364. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: kana ganin muminai a cikin tausayawarsu da kuma kaunarsu da tausasawarsu kamar jiki daya ne; idan wata gaba ta yi zogi, sai sauran jiki ya amsa masa da rashin baccin dare da kuma zazzabi[6].

365. Daga Imam Ja’afar Sadik (S.A.W) ya ce: mumini dan’uwan mumini ne kamar jiki daya ne; idan wani abu daga gareshi ya ji ciwo sai a samu wannan ciwon a sauran jikinsa. kuma ruhinsu daga rai daya ce, kuma hakika rayukan muminai sun fi tsananin haduwa da ruhin Ubangiji fiye da yadda hasken rana ya hadu da ita[7].

2 / 3

Falalar ‘Yan’uwantaka Saboda Allah

366. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: wani mutum musulmi bai taba amfanuwa da wata fa’ida -bayan fa’idar musulunci- kamar fa’idar samun dan’uwa a addinin Allah ba[8].

367. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: wanda ya yi ‘yan’uwantaka saboda Allah to ya rabauta, wanda kuma ya yi ‘yan’uwantaka saboda duniya to ya tabe[9].

368. Daga Imam Ali (A.S) ya ce: da ‘yan’uwantaka saboda Allah ne ake samun sakamakon ‘yan’uwantaka (kyakkyawa)[10].

369. Daga Imam Ja’afar Sadik (S.A.W) ya ce: son mutum ga ‘yan’uwansa yana daga fifikonsa gun Allah [11].

370. Al’kafi, daga hafs dan al’bukhtari: Na kasance gun Abu Abdullahi (A.S) sai wani mutm ya shiga wajensa, sai ya ce da ni: kana son sa? Sai na ce: E. sai ya ce da ni: me kuwa zai hana maka sonsa alhalin shi dan’uwanka ne, kuma abokin tarayyarka a addininka, kuma mai taimakonka a kan makiyinka, kuma arzikinsa yana kan waninka![12].

2 / 4

‘Yan’uwantaka Tsakanin Sahabban Annabi (S.A.W)

371. Daga Masnad Abu Ya’ala, daga Anas; Daga Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana sanya ‘yan’uwantaka tsakanin mutane biyu daga sahabbansa, sai dare ya tsawaita ga dayansu har sai ya (yi kokari ya) hadu da dan’uwansa, sai ya hadu da shi da soyayya da tausasawa, sai ya ce: yaya ka kasance bayana? Amma sauran mutane ba mai zuwa wajen dan’uwansa har kwana uku, bai ma san abin da dan’uwansa yake ciki ba[13].



back 1 2 3 next