Soyayya Don Allah



1 / 4

Sababin Karbar Imani

356. Daga Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: da na yi azumin ranakuna ban sha ba, kuma na yi sallar dare ban taba bari ba, kuma na ciyar da dukiyata a tafarkin Allah loto loto, sannan kuma sai ya kasance a zuciyata babu soyayya ga masoya Allah, kuma babu kiyayya ga makiyansa, to da wannan bai amfanar da ni komai ba[7].

1 / 5

Mafificin Ayyuka

357. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: mafifitan ayyuka su ne so don Allah da kuma ki don Allah[8].

358. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: Allah ya yi wahayi ga wani Annabi daga annabawa ka gaya wa wane mai ibada cewa: amma kin duniyarka to gaggauta hutu ne ga kanka, amma yankewarka zuwa gareni, to ka samu izza da ni ne, to me ka yi kenan wanda yake nawa ne a kanka? Sai ya ce: ya Ubangiji mene ne kake da shi a kaina? Sai ya ce: shin ka ki wani makiyina, kuma ka so wani masoyina?![9].

1 / 6

Neman Taimakon Allah A Son Wanda Yake Sonsa

359. Daga Manzon Allah (S.A.W) ya ce: ya Ubangiji ka sanya mu cikin masu shiryarwa shiryayyu, ba batattu masu batarwa ba, aminci ga masoyanka, gaba ga makiyanka, muna son wanda ya yi so da sonka, muna kin wanda ya saba maka da kinka[10].

360. Daga Imam Zainul abidin (A.S) ya ce: -a cikin munajatin nan da ake ce masa sugura- ya Ubangiji ka yi tsira ga Muhammad da alayen Muhammad… ka sanya mu masu neman hidimarka ga bayi da zababbu a cikin sasanninta, kuma ka sanya mu sahabbai ga kebantattu daga zababbun bayinka, kuma masoya ga masu nufinka masu rataya (damfaruwa) da kofarka[11].

1 / 7

Soyayya Saboda Allah Bisa Jahilta

361. Daga Imam Muhammad Bakir (A.S) ya ce: Da wani mutm ya so wani saboda Allah, da Allah ya saka masa da alheri saboda sonsa da ya yi, ko da kuwa wanda ake so ya kasance dan wuta ne a wajen Allah (S.W.T), da wani mutum ya ki wani mutum saboda Allah (S.W.T) da Allah ya saka masa saboda kinsa da ya yi koda kuwa wanda ake ki ya kasance dan aljanna ne a wurin Allah (S.W.T)[12].



back 1 2 3 next