AnnabciBayani Game Da Annabci
Mun yi imani da cewa annabci aiki ne na Allah kuma jakadanci ne na ubangiji (S.W.T) da yake bayar da shi ga wanda ya so ya kuma zaba daga bayinsa na gari da masoyansa kammalallu a mutumtakarsu, sai ya aika su zuwa ga sauran mutane domin shiryar da su ga abin da yake da amfani da maslaha garesu duniya da lahira, tare kuma da nufin tsaftace su da tsarkake su daga daudar miyagun dabi’u, da munanan al’adu, da koya musu hikima, da ilimi, da bayyana musu hanyoyin rabauta da alheri, domin ‘yan adamtaka ta kai ga kamalarta da ta dace da ita, ta daukaka zuwa ga daraja madaukakiya a gidajen duniya da lahira. Kuma mun yi Imani cewa ka’idar tausasawa -kamar yadda bayaninta zai zo- ta wajaba ga Allah mahalicci mai ludufi ga bayinsa, ya aiko manzanninsa ne domin su shiryar da dan Adam, da kuma isar da sakon kawo gyara, kuma su zamanto jakadun Allah kuma halifofinSa. Kamar yadda muka yi imani da cewa Allah madaukakin sarki bai ba wa mutane hakkin ayyana Annabi ba ko tsayar da shi -takara- ko zabensa. Ba su da wani zabi a kan haka, domin al’amarin dukkan wannan yana hannun Allah ne, domin “Shi ne mafi sanin inda zai sanya sakonSaâ€. Surar An’am Aya ta 124. Kuma ba su da wani hukunci a kan wanda Allah zai aiko shi a matsayin mai shiryarwa, mai albishir ko mai gargadi, ko kuma su yi hukunci kan abin da ya zo da shi na daga hukunce-hukunce, da sunnoni, da shari’a. Annabci Tausasawa Ne
Mutum halitta ne mai iyakoki mai ban al’ajabi, mai sarkafaffun gabobi a halittarsa, da dabi’arsa, da ruhinsa, da kuma hankalinsa, kai hatta ma a kowane daya daga cikin mutane, dabi’ar fizguwa zuwa ga fasadi sun tattara a cikinsa, kamar yadda dabi’ar motsarwa zuwa ga aikata alheri da gyara suka tattara a cikinsa[1], ta wata fuskar kuma an halitta shi a kan dabi’u[2] daban-daban kamar son fifita wani a kansa, da sha’awa, kuma an halitta shi a kan son rinjaya da mamayar waninsa, da kwadayin rayuwar dauniya, da adonta, da kawarta, da tarkacenta, kamar yadda Madaukakin sarki yake cewa: “Hakika mutum yana cikin hasaraâ€. Surar Asri: 2. “Hakika mutum yana dagawa. Don kawai ganin ya wadataâ€. Surar Kalam:6-7. “Hakika rai mai umarni da mummuna ceâ€. Surar Yusuf: 53. Da sauran ayoyi makamantan wadannan da suke bayyanawa a sarari da nuni ga irin yadda ran mutum yake kunshe da dabi’u da kuma sha’awa. A wani bangaren, Ubangiji madaukaki ya halitta masa hankali mai shiryarwa da yake shiryar da shi zuwa ga gyara da ayyukan alheri, da kuma zuciya mai gargadi da take hana shi aikata mummuna da zalunci, tare da aibata shi a kan aikata abin da yake mummuna abin zargi. Husumar cikin zuciya da take cikin ran mutum ba ta gushewa tsakanin hanakali da dabi’u, duk wanda hankalinsa ya yi galaba a kan dabi’arsa to yana daga cikin mafi kololuwar matsayi masu shiryarwa a ‘yan adamtakarsu, kuma su ne kammalallu a ruhinsu. Amma wandanda kuwa dabi’arsu ta rinjaye su, to lalle suna daga cikin masu hasarar matsayi, masu ci baya a ‘yan Adamtaka, masu gangarawa zuwa ga matsayin dabbobi. Mafi tsananin abokan gabar rai su ne zuciya da rundunarta, saboda haka ne muke samun mafi yawancin mutane sun dulmuye a cikin bata, suna nesa da shiriya ta hanyar bin sha’awace-sha’awace da amsa kiran zuciya: “Kuma mafi yawan mutane ba zasu zama muminai ba koda kuwa ka yi kwadayin hakaâ€. Surar Yusuf: 103. Saboda gazawar mutum da rashin tsinkayonsa game da abubuwan da suke kewaye da shi, da asiran abubuwan da suke kewaye da shi, da ma wadanda suke bullowa daga cikinsa shi kansa, ba zai iya sanin dukkan abin da zai cutar da shi ko ya amfane shi ba shi da kansa, kuma ba zai iya sanin abin da zai kai shi ga samun sa’ada ko tsiyacewa ba, shin a kan abin da ya kebantu da shi ne shi kadai, ko kuwa wanda ya shafi ‘yan Adam baki daya da kuma al’ummar da take kewaye da shi. Shi bai gushe ba yana jahiltar kansa kuma yana kara jahilci ko kuma kara gane jahilcinsa duk yayin da iliminsa game da halittu na dabi’a da sauran samammu na binciken ilimi ya karu ba. Saboda haka mutum a tsananin bukatarsa ta son kai wa ga darajar sa’ada yana bukatar wanda zai dora shi a kan hanya mikakkiya bayyananniya zuwa ga shiriya, domin rundunar hankali ta karfafa da hakan, kuma ya iya yin galaba a kan abokin gabarsa yayin da ya shiga fagen faman gwabzawa tsakanin rundunar hankali da na zuciya. Saudayawa bukatar wanda zai kama hannunsa zuwa ga alheri da gyara tana kara tsananta ne yayin da zuciya take yaudarar sa ta hanyar nuna masa kyawun fandarewarsa, sai ta nuna masa abin da yake mummuna cewa kyakkyawa ne ko kuma kyakkyawa cewa mummuna ne, ta kuma rikita wa hankali tafarkinsa zuwa ga gyara, da sa’ada, da ni’ima, a lokacin da shi ba shi da masaniyar da zai bambance dukkan abin da yake mai kyau mai amfani da kuma wanda yake mummuna mai cutarwa. Koma kowane mutum ya sani cewa yana cikin wadannan gwagwarmayar dauki-ba-dadi ko ya sani ko bai sani ba sai dai wanda Allah ya kare shi.
|