Hukunce - HukunceA: Idan har ya tabbata ga baligi cewa shi mujtahidi ne da ya cika sharudda, to babu wata matsala ga hakan. T6: Shin yin taklidi ga malamai (mujtahidai) na wasu kasashe na waje ya halatta ko da kuwa saduwa da su ba zai yiwu ba? A: Ba sharadi ba ne ga mujtahidin da ake masa taklidi ya kasance kasa daya ko gari daya da mai yi masa taklidi (mukallafi). T7: Bisa ga ra'ayin Imam khumaini (r.a) na cewa dole ne marjain da za'a yi masa takalidi ya kasance masani ne kan al'amurran siyasa, tattalin arziRi, aikin soja, zamantakewa da shugabanci baki daya da kasancewarsa masani kan hukunce-hukuncen ibadu da mu;amaloli, to mu a halin yanzu bayan mun kasance muna taklidi da Imam Khumaini (r.a) sai muka ga ya zama wajibi- bisa la'akari da irin shiryarwar da muka samu daga wajen wasu manyan malaman kana kuma da abin da muka gani da kanmu mu koma gare ka don yin taldid, ta yadda zai zamanto kenan mun hada shugabanci da kuma marjiiyya, to shin mene ne kake gani? A: Sharuddan cancantar marja'in da za'a masa taklid suna nan an yi cikakken bayaninsu a cikin littafan Tahrirul wasila da sauran littattafa. To amma al'amarin gano wadannan sharudda da kuma zaben wanda ya dace dan yi
|