Hukunce - Hukunce



hukuncin l(asa ta musulunci hakana fatawarsa ita ce abin bi cikin ababen da suka game musulmai duka amma lamurran

da suka shafi daidaikun mutane, to kowane baligi zai iya tuntuBar marja'insa a kansu.

T41: Misali idan na kasance ina takalidi wa wani marja'i, sai "waliyu amril muslimin" ya ba da umumin fita

yaki dan fuskantar karirai azzalumai ko kuma ya wajabta jihadi, to amma marja'in da nake masa takalidi bai ba ni izinin shiga yakin ba, to shin zan bi ra'ayinsa ne ko kuma a'a?

A: Wajibi ne yin biyayya ga umamin wali amril muslimin cikin al'amurran da suka game musulmai wanda kare addinin musulunci da musulmai yana daga cikin wadannan lamurra, domin kare su daga kafirai da azzalumai da suka kawo hari ma musulmai.

BABIN WILAYATUL FAKIH DA KUMA HUKUNCIN SHUGABA (JAGORA)

T42: Shin za'a iya  daukar mutumin da bai yarda da' wilayatui fakih na mutlaki ba cewa shi musulmi ne hakika?

A: Rashin yarda da wilayatui fakih na mutlaki a zamanin gaibar Imam Mahdi (A.F), bai sa mutum ya yi ridda kuma bai fitar da mutum daga musulunci sawa'un ijtihadinsa ne ya kai shi shi ga haka, ko kuma taklidinsa.

T43: Shin umarnin waliyul fakih suna wajaba kan dukkan musulmai ne ko kuma wajibcinsa kawai kan masu yi masa takalidi ne ? kana shin wajibi ne ga wanda yake takalid ga wanda bai yarda da wilayatui fakih na mutlaki ba ya yi biyayya ga waliyul fakih ko kuma a'a?

A: A bisa fikihun shia wajibi ne ga kowane musulmi ya yi biyayya ga umarnin da suka fito daga waliyu amril muslimin, da kuma mika wuya ga umami da hane-hanensa hatta ga sauran manyan malamai (maraji'ai) to ina ga masu yi musu takalidi! Mu ba ma ganin biyayya ga wilayatui fakih wani abu ne da yake da bambanci da yin biyayya ga addinin  musulunci  da kuma jagoranci  na  Imamai ma’asumai (A.S)



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 next