Jazirar LarabawaJazirarLarabawa Kafin Musulunci Idan muna son fahimtar musulunci da sanin girman annabin rahama mai shiryarwa Muhammad (S.A.W) Wanda da ikon Allah ya iya tseratar da dan Adam, ya sanya shi a “Hakika wannan kur’ani yana ambaton lokacin zamanin larabawa da yake tukewa har zuwa bayyyanar musulunci a lokacin jahiliyya, ba komai ba ne sai nuni daga gareshi zuwa cewa; abinda yake hukunci a cikinsu a wannan zamani shi ne jahilci ba ilimi ba, kuma abin da ya mamaye su a cikin kowane al’amari nasu ba komai ba ne sai varna ba gaskiya ba[1], sun kasance a kan hakan kamar yadda kur’ani ya ke ba mu labarinsu yana mai cewa: “Suna tsammani ga Allah abin da yake ba gaskiya ba zato na jahiliyya suna masu cewa shin mu na da wani makami na wani abuâ€‌. Ali imran: 154. Ubangiji madaukaki ya ce: “Shin hukuncin jahliyya suke so waye yafi kyautata hunkunci fiye da Allah ga mutane masu yakiniâ€‌. Al-ma’ida: 50. Ya ce: “Yayin da wadanda suka kafirta suka sanya gaba a zuciyarsu irin gaban nan ta jahiliyya, sai Allah ya saukar da nutsuwarsa a kan manzonsa da kuma a kan muminai ya kuma lizimta musu kalmar takawa, kuma da man sun kasance su ne mafi cancanta da ita kuma su ne ma’abotanta, kuma Allah ya kasance masani da kowane abuâ€‌. Al-fath:26. Ya ce: “Ku tabbata a gidajenku kada ku yi fita irin fitar jahiliyya ta farko, ku tsayar da salla, ku bayar da zakka, ku bi Allah da manzonsaâ€‌. Ahzab: 33. Wannan ayoyi su ne mafificin madubi da yake nuna halin da larabawa da yanayinsu ya kasance, al’ummar larabawa musamman yankin hijaz ba ta da wata wayewa, kuma babu wani abu na wayewa da cigaba da ya rage a cikinta kafin bayyanar musulunci, kuma ga al’adu iri-iri da koyi da iyaye da ya yadu a cikinta da mafi shahararsu su ne: 1- Shirka da Allah a ibada, ta hanyar bauta ga gumaka da taurari. 2- Musun tashin kiyama, wato komawar mutum zuwa rayuwa a wata duniyar bayan mutuwarsa. 3- Yaduwar surkulle da kauce wa tafarki madaidaci da camfi, abubuwan da suke dakushe hankulan mutane, wadannan al’adu ne da suka yi karfi a suka kafu a cikinsu, kuma suka kasance dalili mai karfi na ci bayansu, kuma suka zama hani mai karfi a tafarkin cigaban da’war musulunci daga baya, abin da ya sanya annabi (S.A.W) yake aiki da dukkan karfinsa da kokarinsa wajan kawar da wadannan al’adu na jahiliyya, da gurvatattun akidu.
|