Halayen Zamantakewa (A.S)



Tare da cewa wadannan siffofi zai iya yiwuwa a yi la’akari da su da himmancin da imamai suke bayarwa na larurar cikar wadannan siffofi ga mutum mumini kamili, wadanda wannan ruwayoyi suke magana akansu da suka zo daga garesu (A.S) a bahasosin jihadin nafs da horo da kyakkywa da hani ga mummuna da kuma babobin hukuncin zamantakewa da makamantansu, kamar yadda zamu yi nuni da shi a wajaje daban-daban na wannan littafi musamman a tsarin alakar zamantakewa, sai dai wannan yana zuwa a farkon yakini da Allah madaukaki da kuma yarda da ubangiji da kuma kyautata zato dogaro gareshi da lizimtar umarninsa da haninsa.

Iko a kan Kafewa

Iko a kan kafewa da dagewa da kuma daukar nauyi mai girma a wajan bayar da gudummuwa, da kuma ci gaba domin tabbatar da hadafi mafi girma game da al’amarin jagoranci, wannan kuwa ta hanayar kamalar mutumtaka domin gina jama’a ta gari, da kuma kiyaye rai, da kiyaye sirri da hakuri da dogara da Allah da fansa da rai da kuma kyautata zaman tare da mutane, da cika alkawari da bayar da amana, da kuma siffantuwa da dabi’ar musulunci madaukakiya, da kuma wayewa da fahimta ta gari ga al’amuran musulunci.

Wannan siffa suna daga siffofi masu muhimmanci wadanda jama’a ta gari take bukatar ta wajan wanzuwarta da cigaban samuwarta wajan fuskantar tsarkakar jiki, da kuma takurar rai wacce makiya suke aiwatarwa a kan wannan jama’a, haka nan a wajan fuskantar hadakar zamantakewa da kuma canje-canjen siyasa da mushkilolin yau da kullum a zamantakewa, da cigaban daukar nauyin isar da sako ta hannun musulmi a lokutan rayuwa daban-daban.

Daga nan ne zamu samu cewa Ahlul Baiti (A.S) suna sanyawa shi’ar su tsari da dokoki da kuma siffofi domin takiyya da amincin zamantakewa a yanayi daban-daban da zamu yi magana game da shi nan gaba, kamar yadda suka tsara musu yanayin zamantakewa, suna kuma himmantuwa da wannan janibai na kyawawan dabi’u da ruhi da wayewa muhimmanci mai girma, suna kuma sanya tsari da dokoki a wannan janibin da kuma kyawawan dabi’u da siffofi na larura wacce wajibi ne ga jama’ar da take danganta kanta da wannan jama’a na daga shi’arsu su siffantu da su, suna ganin kiyayewa wadannan dokoki yana daya daga cikin jarabawoyi ne ga dan Shi’a, kuma siffofi ne kebantattu nasa.

Daga misalin wannan muna iya nuni zuwa ga wannan siffa wacce da sannu karin bayani game da ita zai zo:

Hakika Ibn Sadaka ya rawaito daga Abu Abdullahi (A.S) ya ce: “Ku gano shi’armu yayin lokutan salla yaya suke kiyayewa a kanta, da kuma sirrinmu yaya suke kiyaye shi gun makiyanmu, da kuma dokiyoyinsu yaya suke taimakon â€کyan’uwansu da itaâ€‌[40].

A wata ruwaya daga Abu Rabi’i Asshami ya ce: “Na shiga wajan Abu Abdillah (A.S) gida ya cika makil da mutane, a cikin gidan akwai Hurasani da Shami da kma mutane daban-daban daga sasanni, ban sami wajan da zan zauna ba a ciki, sai Abu Abdillahi (A.S) ya zauna ya kasance yana kishingide sannan ya ce: Ya shi’ar alyayen Muhammad (S.A.W) ku sani ba ya daga cikinmu wanda bai mallaki kansa yayin fushi ba, haka ma wanda bai kyautata abotakar wanda ya abotakance shi ba, da zamantakewar wanda ya zauna da shi, da abotakar wanda ya yi abota da shi, da makwabatakar wanda ya yi makwabtaka da shiâ€‌[41].

A wata ruwaya daga Muyassar ya ce; “Abu Ja’afar (A.S) ya ce: Ya Muyassar ba na baka labarin shi’armum ba? Sai na ce: Ina fansarkak da raina. Sai ya ce: Su katangu ne masu kamewa, kuma kiraza amintattu, kuma hankula masu kaifi, ba sa daga cikin masu yada magana mara kan gado, ba kuma masu kaushi ko masu riya ba, masu ibadar dare, zakuna da ranaâ€‌[42].

A wata ruyawa daga Abu Ja’afa (A.S): “Shi’armu su ne masu bayar da komai saboda wilayarmu, masu so a cikin kaunarmu, masu ziyartar juna a wajan raya al’amarinmu, wadanda idan suka yi fushi ba zasu yi zalunci ba, idan suka yarda ba sa barna, masu albarka ga wanda suka fake gunsu, masu aminci gun wanda ya yi mu’amala da suâ€‌[43].

Hakika mun karanta a hadisin da ya rigaya kamar sauran hadisai da suke karfafa bayar da amana, yana bayyana a wannan tsari bayyana mai kayatarwa ta hanyar hadisai masu yawa kawarai da suka zo daga garesu a wajan ladabtar da shi’ansu da tarbiyyatar da su a kan dabi’a ta gari, kamar yadda muka samu a wannan tattararrun hadisai, musamman a babin zamantakewa da horo da kyakkyawa. Hakika na wallafa littafi na musamman a cikin wannan. kuma da sannu karin bayani zai zo a wannan janibi na ruhi da tsarin alakar zamantakewa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 next