Halayen Ananbi-4



Halayen Manzon Allah (s.a.w) - 3

Idan aka tambaye shi yin wani abu; idan zai yi sai ya ce; Na'am, amma idan ba zai yi ba sai ya yi shiru, ba ya kallon abin da yake na shagaltuwar duniya domin kada ya shagaltu da shi ko ya dauke masa hankali, kuma idan wani abu ya bata masa rai sai ya shiga yin salla, yana son kebewa shi kadai domin yin ambaton Allah da tunani da lura shi kadai, yana tanadar ruwan sallar darensa, yana tamaka wa matansa ayyukan gida, yana yanka nama, baya kura wa wani ido, yana sanya zoben azurfa a hinsar na dama, yana yin aswaki, yana raka janaza, yana gaida maras lafiya, ba ya tsawaita salla idan wani yana jiran sa sai ya gama salla ya ce masa: Kana da wata bukata ne?

Ya kasance yana fadin gaskiya a fushi ne ko a yarda, yana son miskinai, idan zai yi bacci sai ya yi alwala ya yi salla raka'a biyu gajeru sannan sai ya kwanta, ya ambaci Allah yayin kwanciya ya gode masa yayin tashinsa, yana yin matashi da damansa. Yana son aure yana kwadaitar da yin sa, yana da kishin matansa matuka, da safe kuwa yana shafa kan 'ya'yansa da jikokinsa, yana kyautata sunayen yara da aka haifa yana yi musu akika (ragon suna(, idan talauci ya same su sai ya ce da iyalansa ku tashi mu yi salloli.

Idan ya yi tafiya yana daukar madubi, da kwalli, da miswaki, da mataji, da kwalbar turare, da allura da zare, idan yana tafiya baya girman kai kuma ba ya nuna ragwanta ko kasala ko gajiyawa, idan an zo gangara sai ya yi tasbihi, idan kuwa an zo hawa sai ya kabbara, kuma duk inda ya sauka sai ya yi raka'a biyu tukun, sannan yana kin mutum ya yi tafiya shi kadai.

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance mafi yawan tufafinsa farare ne, kuma yana son koren tufafi, sannan yana kwadaitar da mutane kan yin tsafta. Yana da zobuna da yake sanya su a hannun dama, sannan yana sanya kafar dama kafin hagu a sanya takalminsa, amma yana fara cire hagu kafin dama, yana da tufafi na musamman don sanya su ranar juma’a.

Allah madakaki ya girmama shi da abubuwa, ya sanya yin salati gareshi tare da alayensa a matsayin wajibi addini da ya hau kan musulmi, sannan ya sanya biyayya gareshi da alayensa wajibi ne a kan dukkan mutane baki daya. Zancensa da na alayensa wasiyyansa dukkansa hikima ne kuma hujjar Allah ce kan talikai, kuma tafarkin tsira da shiriya ga duniya baki daya.

Domin hadafin manzon Allah (s.a.w) shi ne tsiratar da duniya gaba daya, don haka ne ya sanya soyayya da kauna su kasance jagorori a cikin al’umma baki daya, sannan ya sanya ‘yan’uwantaka tsakanin musulmi a zamaninsa sai dai ban da gado da hani ya zo a kansa daga baya sai dai ga makusanta na jini. Da haka ne ya kafa wata al’umma mai karfi da ilimi, da son juna, wacce ta dauki nauyin yada wannan addini a duk fadin duniya baki daya.

Ya kasance ba ya tashi ko zama sai bisa ambaton Allah madaukaki, kuma yana zama inda ya samu sarari ne ba ya gwamatsar mutane, ya kasance yana daidaita kowa a bisa girmamawa. Majalisinsa wuri ne na jin kunya, da hakuri, da gaskiya , da amana, da kawaici, da girmama babba, da tausaya wa karami, da biyan bukatun mabukata.

Bai kasance mai kaushin hali ba, ya kasance mai sakin fuska, mai fara’a, mai taushin hali, ba ya aibatawa, ba ya zagi, ba ya alfahasha, kuma yana kau da kai daga abin da yake sha’awa, idan ya yi magana duk sai mutane su sunkuyar da kai kamar dai a kansu akwai tsuntsaye ne, sai dai idan ya yi shiru ne to sais u yi magana, kuma ba sa jayayya gunsa.

Da zai bar duniya ya bar wa al’ummarsa abubuwa biyu day a gaya musu idan sun yi riko das u ba zasu taba bata ba har abada, su ne; Littafin Allah da wasiyyansa alayensa tsarkaka goma sha biyu, hada da mai tsarki uwar alayensa matar wasiyyinsa na farko sayyida Zahara as, Allah ya sanya mu cikin cetonta. Ya wajabta son su kan kowa, da biyayya garesu da taimaka musu, da tsayawa idan suka tsayar da al’umma, sai dai al’umma ta yi watsi da wannan wasiyyar kamar yadda aka yi watsi da wasiyyar sauran annabawa

 

Rufewa:

Yayin da Allah ya halicci mutum yayin nufin alheri da rabautar duniya da ni'imar lahira da aljanna gareshi amma wannan duk ba ya samuwa sai idan mutum ya yi amfani da hankalinsa da kuma abin da ya dace da ruhinsa da jikinsa, wannan kuwa yana bukatara abin da zai dauke wadannan bukatu wadanda ba wanda zai iya samar da dukkan wannan sai mahaliccin mutum din da ya san shi kuma ya san bukatunsa.

Tun da Allah yana son rabauta ne ga mutum shi ya sa halicce shi, don haka ne sai ya samar masa da hanya kamila da zai bi domin samun rabauta ta hanyar wasu amintattun bayi nasa da suke ma'asumai daga dukkan kuskure da mantuwa kuma tsarkaka daga dukkan aibobi da zunubai wadannan su ne annabawa da manzanni.

Don haka ne: Annabi shi mutum ne da Allah ya yi masa wahayi ya zabe shi a cikin mutane kuma sun kasu gida biyu:

Annabi dan sako shi ne wanda aka aiko domin ya tseratar da mutane daga duhu zuwa haske daga barna zuwa gaskiya daga camfi zuwa gaskiya daga jahilci zuwa ilmi.

Annabi ba dan sako ba: shi ne wanda aka yi masa wahayi zuwa ga kansa kuma ba a umarce shi ya isar da sakon ga mutane ba.

Yahudawa suna bin Annabi Musa (a.s) kiristoci kuma Annabi Isa (a.s) musulmi kuma Annabi Muhammad (s.a.w) da sauran annabawa duka. Sai dai musulunci ya shafe sauran addinai da suka rigaya, bai halatta ba ma'abotansu su wanzu a kansu, dole ne a kan kowa ne mutum ya bi koyarwar musuluncici. Ubangiji yana cewa: "wanda ya yi riko da wani addini ba musulunci ba to ba za a karba daga gareshi ba, kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara"[1].

Don haka yahudanci da kiristanci barna ne da aka shafe su, amma musulunci mai wanzuwa ne har zuwa ranar kiyama.

Annabi Muhammad (s.a.w) shi ne karshen annabawa kuma addininsa shi ne musulunci mai shafe duk wani addini kuma shari'arsa zata wanzu har zuwa kiyama kuma ita kadai ce shari'ar da zata arzuta mutum da tabbatar masa da burinsa da amincinsa har zuwa karshen rayuwa duniya da lahira. Kamar yadda shi kadai ne mutum abin koyi ga dukkan duniya baki daya, dukkan mutanen duniya idan suna son alheri ga kawukansu to dole ne su bi tarfarkinsa su yi koyi da kyawawan halyensa (s.a.w) da kuma sanin sashen tarihinsa da ba makawa mu kawo wasu daga siffofinsa (s.a.w):

Shi ne Muhammad dan Abdullah (s.a.w) kuma babarsa ita ce Aminatu 'yar Wahab. An haife shi a Makka ranar juma'a goma sha bakwai ga watan Rabi'ul awwal bayan bollolwar alfijir a shekarar giwa, a zamanin sarki mai adalci Kisra[2]. (wato idan an kwatanta shi da ire-irensa).

An aiko Annabi Muhammad (s.a.w) da sako a 27 ga Rajab bayan yana dan shekara 40 yayin da Jibrilu (a.s) ya sauka gareshi daga wurin Allah (S.W.T) yana kogon Hira wanda yake dutse ne a Makka ya ce masa ka karanta kuma ya saukar masa da ayoyi biyar na surar Alaki[3].

Sai ya zo ya tsaya a kan dutsen Safa a masallaci mai alfarma na Makka a lokcin akwai jama'a masu yawa a wurin da ake taruwa ya isar da sakon Allah na shiryar da mutane zuwa ga imani da shi yana cewa da su: "Ku ce babu abin bauta sai Allah kwa rabauta"[4].

A lokacin tunda mutanen Makka mushrikai ne, kuma suna ganin maslaharsu ita ce shirka kuma suna tsoron maslaharsu sai suka rika yi masa isgili suna yi masa dariya suna cutar da shi. Kuma duk sa'adda ya dage wajen shiryar da su sai su dage wajen cutar da shi har ya ce: "Ba a cutar da wani Annabi ba kamar yadda aka cutar da ni"[5].

Ba wanda suka yi imani da shi sai mutane kalilan, na farkonsu Imam Ali sannan sai matarsa Hadiza (a.s) sannan sai wasu mutane.

Farkon wanda ya yi imani da shi daga maza Imam Ali (a.s) sannan daga mata sai Hadiza (a.s).

Yayin da takurawar mushrikai ta yi yawa sai ya yi hijira zuwa Madina wannan kuwa ita ce hijirar farko a tarihin Musulmi, yayin da suka yi yawa sai karfinsu ya dadu kuma suka samu koyarwa daga Manzon Allah da shari'arsa mai sauki mai hikima, da kuma misali na kyawawan halaye da mutumtaka da wayewa da cigaba a Madina har suka fi dukkan duniya da addini na sama da wadanda ba na sama ba.

Kuma an samu yakoki masu yawa a Madina kuma dukkanninsu sun zama domin kare kai ne daga makiya mushrikai da yahudawa da kiristoci da suke kai hari kan musulmi, kuma Annabi a kowne lokaci yana zabar bangaren sulhu da zaman lafiya ne da rangwame, don haka ne ma adadin wadanda ake kashewa daga bangarorin biyu ba su da yawa a dukkan yakokinsa tamanin da wani abu, wato; wadanda aka kashe na musulmi da kafirai duka ba su kai sama da dubu daya da dari hudu ba.

Tun lokacin da aka aiko Annabi da sako har ya tafi daga duniya wahayi yana sauka gareshi kuma Jibrilu (a.s) shi ne ake aiko masa daga wajen Ubangiji (S.W.T) a hankali a hankali har littafin Kur'ani ya ciki a cikin shekaru ishirin da uku, sai Manzo (s.a.w) ya yi umarni da a hada shi kamar yadda yake a yau din nan.

Manzo (s.a.w) ya kasance yana tsara wa musulmi duniyarsu da addininsu, yana sanar da su littafi da hikima kuma yana yi musu bayanin dokokin ibada da biyayya da mu'amala da zamantakewa da siyasa da tattalin arziki da sauransu.

Bayan cikar addini da kafa Ali dan Abu Dalib (a.s) shugaba na al'umma kuma halifa bayan Annabi (s.a.w) wannan kuwa ya faru a ranar Gadir ne goma sha takwas ga zulhajji a shekarar hajjin bankwana sai Allah ya saukar da ayar: "A yau ne na kammala muku addininku, na cika ni'imata gareku kuma na yardar muku da musulunci shi ne addini"[6]. Sai Annabi ya yi rashin lafiya mai sauki, sai dai ya yi tsanani har sai da ya hadu da Ubangijinsa a 18 ga watan safar na 11H.

Kuma wasiyyinsa halifansa Imam Ali (a.s) shi ne ya yi masa wanka da salla da binne shi a dakinsa a Madina inda kabarinsa yake yanzu.

Ya kansace abin koyi ne shi a rikon amana da ikhlasi da gaskiya da cika alkawari da kyawawan halaye, da girma, da kyawawna dabi'u, da baiwa, da ilmi, da hakuri, da rangawame, da afuwa, da sadaukantaka, da tsentseni, da takawa, da zuhudu, da baiwa, da adalci, da kaskan da kai, da jihadi.

Jikinsa ya kasance kololuwa wajen kyau da kuma daidaito da dacewa, kuma fuskarsa kamar wata ne mai haske da ya cika, kuma zuciyarsa da ruhinsa sun kai matuka wajen kamala, mafi kamalar halaye da ladabi da dabi'a kuma sunnarsa tana haske kamar rana a tsaka-tsakinta.

Atakaice, ya tattara dukkan wata dabi'a mai kyau da girma da daukaka da kuma ilimi da adalci da takawa da kuma iya tafiyar da al'amuran duniya da na lahira, wadanda babu wani mahaluki da yake da irinsu.

Wannan shi ne annabin musulmi kuma wannan shi ne addinin musulunci, kuma addininsa shi ne mafificin addinai, littafinsa shi ne mafifcin littattafai domin shi: "Barna ba ta iya zo masa ta gabansa da ta bayansa, abin saukarwa ne daga mai hikima abin yabo"[7].

Muhimmancin samuwar wannan annabi mai daraja wanda ya kasance hanyar shiriya ga dukkan talikai da suke bayan kasa ne ya sanya musulmi yin murna da bikin ranar haihuwar manzon Allah (s.a.w) da aka fi sani da mauludi.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

--------------------------------------------------------------------------------
[1] Ali imrana: aya: 85.
[2] Duba tarihul alam mujalladi na 1-2. Da Muhammad wal Kur'ani. Da Bakatun adira fi ahwali khatimin nabiyyin. Da siratul fawaha.
[3] Alaki, aya: 1-5.
[4] Manakib, mujalladi 1, shafi na 56.
[5] Kashful gumma, mujalladi 2, shafi: 537, fasali 4, babi 5.
[6] Kashful gumma, mujalladi 2, shafi: 537, fasali 4, babi 5, surar ma'ida: aya: 3.
[7] Fusilat, aya: 42.