Halayen Annabi-1



 

Halayen Manzon Allah (s.a.w) - 1

Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da halayen manzon Allah Muhammad dan Abdullah (a.s) da rayuwarsa.

Manzon Allah (s.a.w) da iyalan gidansa wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.

Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da suke kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

 

Ya zo a babin ci da shan manzon Allah (s.a.w) cewa: "Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana cin dukkan nau'o'in abinci, tare da iyalansa da masu yi masa hidima, kuma yana ci tare da wadanda ya kira su na musulmi a kasa, kuma a kan abin da suka ci da kuma daga abin da suka ci, sai dai idan bako ya zo masa to sai ya ci tare da bakonsa".

Ba mu taba samun wani mutum mai kamala a tarihi kamar manzon rahama (s.a.w) ba, irin daukakar da yake da ita wurin Allah da babu wani mahaluki da ya taka sawunsa balle ma ya hango kurarsa, amma sai ga shi ba mu samu wani wanda ya kai shi kaskan da kai ga mutane ba.

Wani abin da yake nuna mana haka a fili shi ne abubuwan da suka zo a cikin babin cinsa da shansa, akan siffanta shi da cewa yana cin dukkan nau'in abin ci ba tare da ya aibata wani daga abin ci ba, domin dukkaninsu ni'imomin Allah ne da ya bayar da su ga bayinsa domin su gode masa, wannan siffa ta gode wa ni'imomin Allah ta bayyana cikin ayyukansa da zantuttukansa hatta ga abin ci ko sha.

Sannan yana ci tare da iyalansa da masu yi masa hidima, idan muka ce mutum yana ci da iyalansa ta yiwu mutane su ga zai yiwu saboda kusancinsa da su, sai dai ba mu samu al'adun hausa suna yin haka ba, an dauka cewa mace ba ta da wani aiki sai dahuwa da kwanciya, kamar dai wata na'ura ce ta dafa abinci kawai, amma a zauna tare da ita a ci abinci wannan bai ta so ba, haka ma ba a san yin hira da ita ba.

Sai dai tayiwu a samu canji ga mutanenmu na yau sakamakon shigowar al'adu da wayewa da a yau ta fi na mutanenmu na gargajiya, da kuma wayewa da ilimi a yau da suka fi da yawa, ta yadda a yau idan ka dauki matarka kun tafi yawo babu mai ganin hakan a matsayin sabon abu.

Amma cinsa tare da masu yi masa hidima shi ne mafi girman lamarin da ya kamata mu lura da shi sosai, domin masu aikin gida kamar masu wanke-wanke, da masu cefane, da masu yi wa mutumm gadi a cikin al'ummu ba a daukar su da kima, hasali ma mutane sukan iya yi musu tsawa, wasu ma har da duka, kuma tayiwu saboda wani abu ne kankani da suka manta da shi ko suka gafala ba su yi ba.

Sai dai manzon rahama mafi kamalar dan Adam yana daukarsu a matsayin mutane kamar kowa, don haka yana cin abinci tare da su ba tare da wani kyama ba, kuma yana fifita su a kansa, domin su ji cewa su ma al'umma ce mai daraja kuma mutane ne masu kima a cikin al'umma.

Bai taba zagi ko duka ko daka tsawa ga dayansu ba, har ma ya kasance ana cewa yakan ce da su da an yi abu kaza da shi ya fi, tsira da amincin Allah su tabbata gareshi, sai Allah ya siffanta shi da cewa shi ne mafi daukakar bayi a kyawawan halaye. Tawali'unsa ya kai ga balaraben kauye yakan shigo birni sai ya zo majalisin annabi (s.a.w) amma sai ya tambaya ya ce: "Waye Muhammad a cikinku?.

A kasashenmu na kasa da shugaban ba ya iya ganin sa, kuma tayiwu idan ya ce zai gan shi ya kasnace ya yi shekaru bai samu wannan ba, ko kuma ya kasance ana shakkunsa koda kuwa yana son su gaisa ne kawai. Sannan yawanci kallon da shugaban zai yi masa bai wuce kallon wani wanda yake da rashin kima ba, ko kuma ya kalle shi a matsayin wani kayan cimma burin siyasarsa kawai.

Wannan lamarin ne ya sanya hatta da samari ana raba musu kayan shaye-shaye kuma a raba musu makamai domin su kashe junansu, kuma a nesanta su daga ilimi da hankali, don haka ne ake ba su kayan maye. Yayin da shi mai ba su din ba zai yarda ba daya daga cikin kannensa su shiga wannan aikin balle 'ya'yansa kuma, amma ya dauki al'ummarsa abin gwaji domin cimma nasa hadafi ba nasu hadafin ba.

Balle kuma su samu matsayin da zasu je su zauna da shi domin su ci abinci a teburi daya, su gaya masa matsalolinsu, ya share masu hawayensu. Amma sai ga wanda duk wani abu da aka halitta yana kasan darajarsa, wanda shi ne ya samu feshin ilimin Allah na farko da kuma siffofinsa madaukaka, sai ya kasance mai rahama da jin kai, sai ga shi yana zama da wadanda suka zo wurinsa suna cin abinci tare.

Yana ci tare da wadanda suka zo wurinsa na daga musulmi, kuma a kan kasa, wannan halayen na fiyayyen halitta da an samu shugabannin duniya sun kwatanta kashi 10% na wannan halaye masu daraja da an samu ci gaban dan Adam. A kasarmu akwai shahararren malami guda miloniya ne domin yana da kudi da gidaje da ba sa kirguwa, amma babu wani wanda zai ce ya taba zuwa gidansa ya samu wani abin sha koda kuwa ruwa ne balle kuma abinci.

Kai tir da masu sanya rigar sunan musulunci balle malanta amma suna da dabi'un da ko fir'auna ya fi kyautatawa ga mabiyansa. Ba komai ya sanya ni fadin haka ba sai domin fir'auna yana jiyar da mai biyayya gareshi na daga kabilarsa ta kibdawa dadi, yana kaskantar da wasu kabilu ne na Banu Isra'il da yake ganin sun zo bakin haure sun mamaye musu wuri wadanda a ganinsa sun zo sun bata masu addini da gargarjiya ne tun lokacin annabi Yusuf (a.s).

Kuma ayar Kur'ani mai daraja ta yi nuni da wani lamari mai muhimmanci yayin da ta yi wa wasu daga sahabban annabi (s.a.w) fadar cewa idan sun ci abinci a gidansa sai su fita, ba sai ya yi musu nuni ba da cewa su fita. Wato manzon Allah (s.a.w) mai tsananin kawaici da kunya ba ya iya gaya musu cewa idan an ci abinci a fita daga gidansa, sai da ubangiji mai tsananin kishi gareshi ya yi musu fada da abin da suke yi bai dace ba.

Sannan kaskan da kansa ya sanya shi ci a kasa, ba tare da kallon kansa da matsayinsa wurin Allah ba, sai ya kalli kansa a matsayin cewa shi daga kasa yake, kuma cikinta zai koma bayan mutuwarsa, don haka sai ya kasance mai daukakar kaskan da kai, bai kalli turbayar sama ba wacce tasa ta bambanta da ta sauran sahabbansa wanda da ya ga dama da ya yi hakan, amma sai ya kalli turbayar kasa domin ya daidaita kansa da sauran, sai ya bar musu darasi yayin da zasu kasance shugabanin al'umma bayan wucewarsa.

Sai ya ci abin da suke ci, kuma ya sha abin da suke sha, bai ware nasa kwanon daban ba a matsayin kwanon annabi, ko cokalin annabi, ko kofin shan ruwan annabi. Sai ya yarda ya yi tarayya da sauran kan dukkan abin da yake amfani da shi, kamar yadda ya yarda ya ci daga dukkan abin da suke ci.

Bai yarda da ware wani nau'in abinci mai maiko a matsayin nasa daban ba, kuma wannan mummunar dabi'ar da annabi ya yaka mun same ta hatta tsakanin masu da'awar su ne masu kishin addini a duniya, sai a ware wa shugaban wani abinci da talakan da ake tare da shi ba zai iya cin sa ba.

Lallai baban Kasim (s.a.w) duk wanda ya yi da'awar yana kan halayenka daga mutanen duniya da suke raye in banda halifanka na goma sha biyu Imam Mahadi (a.s), ko waye kuwa to wallahi ya yi karya, wanda duk ya yi da'awar ya kiyaye sunnarka kamar yadda kake ya yi jafa'i ga Allah mahalicci kuma ya yi isgili da dukkan kyawawan halaye.

Ba kawai manzon Allah (s.a.w) hatta da Imam khomain wanda bai kai darajar kurar da manzon Allah (s.a.w) ya taka ba, amma sai ga shi Fedal Kasto na Cuba da ya ga gidan da yake rayuwa yana cewa: "Idan dai kwaminisanci yana nufin mu rayu iri daya da babu bambanci tsakanin talaka da jagora to lallai Imam Khomain ya fi mu kwaminisanci", wannan ga malamin gaskiya mai imani da tsoron Allah da yake kokarin ya kwantanta rayuwar manzon Allah (s.a.w) ke nan, ina ga a ce Fedal Kasto ya ga annabin ne kansa.

Sannan kuma yana ci da bakonsa wannan ma wani abu ne mai muhimmanci wanda ya kamata duniya ta yi rubuce rubuce a kansa, domin mafificin al'ummar duniya amma yana ci da baki, kuma yawancinsu mun san mutane ne da suke zo masa daga kauyuka. Don haka mai ji da sarauta ko takamar yana da dukiya ko matsayi ya duba matsayin gaskiya na mafificin halitta, ya yi koyi da shi, ya sauke rawanin tsiya da ya sanya a kansa, domin samun mafi tsira a lahira, da soyayyar Allah madaukaki da bayinsa a duniya.

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana tuna Allah (s.w.t) a kowane abu, don haka zamu ga idan aka ajiye abinci a gabansa sai ya ambaci sunan Ubangiji madaukaki, idan kuwa ya gama sai ya gode masa, kuma bai taba gafala ba ko sau daya ko mantuwa da yin hakan, hatta da sahur da shan ruwa.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com