Halayen Zahra-2Halayen Sayyida Zahara (s.a) - 2 Ta ruwaito hadisai masu yawan gaske a kowane janibi da ya hada da; siyasa, tattalin arziki, zaman tare, rayuwar al'umma, hakkoki, hukunce-hukunce, ibadoji, da mu'amaloli, da sauransu. Wannan lamari ne da yake bukatar tsawaitawa don haka ba zamu fada cikinsa ba. Sayyida Zahara (a.s) ita ce macen da take cikakkiya ta kowane janibi da dukkan mata ya kamata su dukufa wurin neman saninta, da koyi da ita a dukkan janibobin rayuwarta ta zaman al’umma, da ta cikin gida, da ta waje, da ta mu’amala da mutane, da jagoranci da makamantansu. Matan da suke son zama kammalallun mata masu daraja a duniya to sai su yi koyi da mata masu daukaka kuma su dauki samfurin rayuwar zaman tare daga Imam Ali (a.s) da sayyida Zahara (a.s), ga wani misali daga irin wannan; Wata rana Imam Ali (a.s) ya shiga wajan Fadima (a.s) sai ya tambaye ta ko tana da wani abu. Sai ta ce: “Wallahi kwana uku ke nan ya Dan Ammina ba mu da komaiâ€. Sai ya ce: “Me ya sa ba ki gaya min ba†Sai ta ce: “Manzon Allah ya hana ta tambayarsa, ya gaya mata cewa: Kada ki tambayi Dan Amminki (Imam Ali) komai, idan ya kawo, in ba haka ba, kada ki tambaye shiâ€[1]. Daga Saifu, daga Najmu, daga Abu Ja’afar (a.s) ya ce: “Hakika Fadima (a.s) ta lamunce wa Imam Ali (a.s) aikin gida da kwaba gari da yin gurasa da share gida, shi kuwa ya lamunce mata abin da yake bayan kofa: yin itace, kawo abinci… sai wata rana ya ce da ita: Ya Fadima shin kina da wani abu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama hakkinka ba mu da komai tun tsawon kwana uku ke nan sai dai abin da muka tanadar maka kai kadai, sai ya ce: Me yasa ba ki ba ni labari ba? Sai ta ce: Manzon Allah (s.a.w) ya hana ni in tambaye ka wani abu, ya ce da ni: Kada ki tambayi dan amminki wani abu, in ya zo da shi, shi ke nan, in ba haka ba to kada ki tambaye shiâ€. Yahaya da sanadinsa daga Abi Sa'idul khuduri, ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari sai ya ce da Fadima (a.s): Ya Fadima shin kina da wani abu da zamu ci. Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta babu wani abu da ya kwana gunmu da zamu ciyar da kai shi yau, ba ni da komai kwana biyu ke nan sai abin da na zabe ka a kaina da shi da kuma abin da zabi wadannan biyu –tana nufi Hasan da Husain- a kaina da shi. Sai ya ce: Don me ba ki gaya mini ba sai in samo miki wani abu? Sai ta ce: Ni ina jin kunyar Allah in kallafa maka abin da ba zaka iya ba, kuma ka kasa samu[2]. Daga Abil mufaddal, ya ce[3]: Muhammad dan Ja’afar dan Kais dan Maskana ...da dogon sanadinsa sai a koma wa littafin… daga Abi Sa'idul khuduri ya ce: Wata rana Ali (a.s) ya wayi gari mai yunwa, sai ya ce: Ya Fadima, shin kina da wani abu da zaki ciyar da mu? Sai ta ce: Na rantse da wanda ya girmama babana da annabta, ya girmama ka da wasiyya, babu wani abu da ya wayi gari a wajenmu da zamu ciyar da wani mutum shi tun kwana biyu ke nan sai abin da na fifita ka da kai da Hasan da Husain da shi a kaina. Ya ce: Har da ma yara biyu! Me yasa ba ki sanar da ni ba sai in zo muku da shi? Sai ta ce: Ya Abal Hasan, ina jin kunya daga ubangijina in kallafa maka abin da ba zaka iya baâ€[4]. Duba ki ga irin wannan rayuwa ta gidan Ahlul Bait (a.s) wacce hatta abin da yake wajibi a kan miji ba ta tambaya sai idan ya kawo, saboda haka yana da kyau mata su kamanta daidai gwargwado.
Manzon Allah (s.a.w) ya tarbiyyantar da ita, ya yi mata nasihohi, ya kuma nuna mata hanyar da zata bi domin rabauta duniya da lahira. Sai ta bi dukkan shiriyarsa, sai ta kasance malama, mai sanin duk wata mas’ala, kuma ma’asumiya da ba ta taba yin sabo ba, kuma mai shiryayya mai shiryarwa ga al’umma, da al’umma ta bi ta bayan Manzon Allah (s.a.w) da ba a taba samun wani bata ko jahilci ba cikin duniya. Ta sha wahala matuka a rayuwarta, ba don gudun tsawaitawa ba, da mun kawo da yawa daga cikin hikimomin Manzon rahama (s.a.w) da wasiyyoyin da ya yi mata na juriya kan wahalar da take sha, domin ba ta tarbiyya kan kowane janibi na rayuwa. Sai dai yayin da zata bar duniya sakamakon abin da ya faru mai daci na zalunci a kanta, ta yi wasiyya ita ma ga Imam Ali (a.s) da ya boye janazarta da kabarinta, kuma ya yi aiki da dukkan wasiyyoyinta hatta wadanda suka shafi rayuwarsa bayan wafatinta. Ta yi masa wasiyya da matar da zai aura bayanta, da kuma raba kwana tsakanin matarsa da zai aura da ‘ya’yanta Hasan da Husain (a.s) da sauran wasiyyoyi masu sanya kuka da hawaye Allah ya sanya mu cikin cetonta. An yi wa Fadima (a.s) bazata a wata rana da mutuwar Abu Talib ammin Babanta[5] kuma shugaban Bani Hashim a lokacin ne ta san cewa lallai wani rukuni daga rukunan da Babanta (s.a.w) yakan dogara da su ya rushe saboda haka ta ji muryarsa tana rawa saboda bakin ciki, fukafukin da yakan tashi sama da su guda biyu an cisge dayan musamman saboda tsananin bakin ciki da ya mamaye zuciya da fuska madaukakiya. Sai ta ga Babanta mai daraja (s.a.w) yana kuka a farkon ganin haka a rayuwarta da hawaye masu zafi da ke kwarara a kumatunsa masu albarka a lokacin duk wanda yake wannan duniya ya san cewa lallai akwai zafi da yake tafarfasa a cikin jini da tsuka na Annabin rahama don haka ne ma sai ta motsa da jiki mai haske da albarka ta sanya fararen hannayen nan da suke daga aljanna ne aka gina su, tana mai share masa hawaye masu zafi da fari da ke gudana suna diga kasa kamar ‘ya’yan carbi dunkule-dunkule, wallahi na so a ce suna zuba ne a jikina domin in shafe su a fuskata domin kada ta samu shafa daga shedan har abada da takan kai ga toshe mahangar tunani, na kuma shafa a jikina domin kada ya sami kuna na wuta!. Ta kasance tana mai shafewa da hannayenta masu daraja har ta kwantar da zogin da yake ji ta saukar da tafasar nan ta kunkunar juciyarsa ta kawar da abin da yake ji na rashi mai tsanani. Amma ba a dade ba da ‘yan kwanaki kadan sai ga musiba mafi girma ta sauka ta kasance, alhali ga wancan mikin bai warke ba aka sake tunbuke wa Manzon tsira daya fukafukin da ya rage, alhali da man ya yi rauni da yake zubar jini maras yankewa. Wayyo Allah!! ba a dade ba sai na ji wata kalma da ta fito daga baki mai haske da kamshin da digonsa ya fi karfin almiskin da yake cikin duniya gaba daya, wace kalma ce? Kalma ce mai nauyi daga haske mai baki mai haske da ake cewa da ita Babar Babanta (a.s) tana cewa: Ina Babata!!. Saboda haka jin wannan kalma ta sanya Manzo (s.a.w) ya ji wani suka da ya fi sukan kibiya ciwo domin uwa ce ta hakika take tambayar mata ta hakika da suke da wadancan alakoki biyu da mafi girman halitta (a.s) uwa ce kuma ‘ya amma ba tare da an sami abin da masu ilimin falsafa da suke cewa gewayo ba, wato na farko ya koma na karshe, ga hawaye yana zuba kamar ana mamakon ruwa mai kwarara, kai al’umma ku ji wannan kalma mai nauyi da ke kunshe cikin tambayar uwa ga dan da yake uba gareta da take cewa ina Babata?!!. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya yi kuka kuma duk wanda yake tare da shi a cikin gidan ya yi kuka, Fadima ta rankwafa ta shiga cikin lullubewar uban (s.a.w) kamar yanda ‘ya’yan kaza suke shiga cikin fukafukan babarsu, kalma ce da tafi abin da ya faru ciwo saboda bakin ciki ne ya sami uwa da take tafi uwa kima domin ita uwa ce daga bakin wahayi daga duniya mai tsarki da nisa daga duniyar ‘yan mariskai, da wannan ma’ana ta duniya da ba mai gane hakikanin ma’anarta sai masu ilimi. Ya girman nauyin wannan tambaya a wannan hali mai wahala da bakin ciki daga gareta (a.s)!! Saboda haka sai fiyayyen halitta (s.a.w) ya fada yana mai lallashin halinta da neman kawar da nata bakin cikin da ba bakin cikin da ya kai shi ciwo da zafi, ina iya cewa: bakin cikin da yake ji sai ya ta fi sakamakon ganin halin da take ciki, saboda haka sai hadafinsa ya zama shi ne kokarin kawar da nata bakin cikin yana mai fada da harshe mai laushi da taushin murya domin sanyayawa ga zuciyarta: "'Yata hakika Babarki ta tafi aljanna kuma hakika dan’uwana Jibril (a.s) ya ba ni labari cewa tana nan a wani gida na karau ba wahala ba hayaniya a cikinsa[6]". Haka nan Fadima ta zama marainiya ba uwa, ta samu daci a rayuwa tana ‘yar shekara takwas dacin da ba ta tada samun irinsa ba sai a lokacin wafatin Babanta (a.s). Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com -------------------------------------------------------------------------------- [2] A littafin Sharhin akhbar: alkali Nu’uman almagribi, j 2, shafi 401. [3] A littafin Al’amali, Shaikh Dusi, shafi 615. [4] Biharul anwar, Allama majlisi, j 34, shafi 31, Da kuma: j 41, shafi 197. [5] A lokacin shekara ta goma da aiken manzon Allah (s.a.w) ne, bayan fitowa daga Tsarin na ba jimawa, kuma kusan shekarun sayyida Zahara (a.s) takwas ke nan. [6] Buhari: 9/244. Al'isaba: 4/282. Nuzhatul Majalisi: 2/196. Kashful Gumma: 1/360. |