Halayen Zahra-1



Halayen Sayyida Zahara (s.a) - 1

Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da halayen Sayyida Zahara (s.a) da rayuwarta.

Iyalan gidan manzon Allah (s.a.w) wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.

Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da suke kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

Sayyida Zahara (a.s) ta kasance babban misali abin koyi ga duk wanda yake son tsayawa kyam kan gaskiya da kare hakkinsa da kuma hakkin al’umma yayin da bayan wafatin babanta (s.a.w) ta tsaya ta dage wurin ganin ta kwaci hakkinta da gadonta, da kuma hakkin mijinta na jagorancin al’umma, da hakkokin al’umma na ganin sun samu mai shiryarwa zuwa ga tafarkin gaskiya da hasken shiriya da shari’ar Allah (s.w.t).

Ta kasance farkon wanda ya yi shahada kan kariya ga wilayar Imam Ali (a.s) da zuriyarta, da kuma wilayar manzon rahama (s.a.w), da kuma kana bin da ya shafi neman hakkinta wanda yake na dukiyarta ne da annabin rahama (s.a.w) ya ba ta shi kyauta tun lokacin yana da rai, sannan kuma da abin da ya shafi gadonta. Da wannan ne zamu ga ta kasance mutum na farko da ya fara nuna wa duniyar musulmi jajircewa a kan kwatar hakkinsu komai tsanani da wahala.

 Mafi tsananin lamari garta shi ne lamarin da ya shafi jagorancin al’umma bayan manzon Allah (s.a.w) al’amarin da ya sanya ta jaula da gewayawa gidajen ansar domin su ba ta gudummuwa amma ba ta samu wannan ba daga ko da mutum guda. Lamarin ya kai ta ga tattaunawa da halifan farko kan ya ba su hakkinsu amma abin ya ci tura, don haka ne ma aka samu jan daga mai wuyar gaske da musayan kalamai na magana kan wannan lamari tsakanin gidan Annabi (s.a.w) da kuma kuraishawa.

Sayyid Zahara (a.s) ta so ta nuna wa al’umma munin wannan lamarin na canja wasiyyar Annabi (s.a.w) da kawar da jagoranci daga cikin alayensa zuwa ga waninsu, da sakamakon da zai samu al’ummar musulmi na kauce wa koyarwar musulunci ta asali ta asasi. Amma al’umma ba ta amsa mata ba, saboda jahiltar sakamakon abin da ta tsoratar da su, da yawan mutane sun dauka cewa lamarin mulki ne kawai, sai dai abin ya fi karfin hakan kamar yadda ta yi nuni, don sai ga shi al’ummar musulmi ta kasu gida-gida sakamakon sabani kan mene ne gaskiyar hakikanin musulunci, kowa yana bin nasa son ran a matsayin shi ne gaskiya, aka jefar da alayen Annabi (s.a.w) a gefe babu wani mai biyayya ga tafarkinsu sai ‘yan kalilan, wani abin mamaki da takaici ma sai aka bi su da bita-da-kulli da kisa, sannan mai bin tafarkin da suka shata ya zama abin kyama a cikin al’umma.

Fadima (a.s) ta kafa hujja kuma ta yanke duk wani hanzari ga wannan al’ummar yayin da ta nemi su bi ta suka ki, kuma ta nuna musu sakamakon da a yau al’ummar musulmi suke cikinsa na kasakanci, da rarraba, da son rai, da rashin kima da daraja. Ta yi fushi da al’umma amma duk da haka al’ummar ba ta fadaka ba, don haka ne ma ta yi wasiyya da kada wanda ya halarci janazarta sai Imam Ali (a.s) da ‘ya’yanta da wasu kalilan da aka boye sunayensu don gudu kada a tilasta su nuna inda aka binne ta, don haka ne ma ya kasance abin kunya har yau ga duniyar musulmi domin ba su san kabarinta ba!.

Ta kasance mafi muhimmancin mutum da yake misalta mai hamayya da shugabancin Abubakar da duk wanda yake goyon bayansa, sannan kuma mutum mai kwarjini da kowa yake shayi, wasu masu tarihi sun kawo cewa Imam Ali (a.s) ya samu sauki a rayuwarta daga cutarwar masu jagoranci har sai bayan mutuwarta ne aka tilasta masa, aka takura rayuwarsa da kuntatawa mai tsanani!, har ma suna kawo cewa duk tilascin da aka yi masa bai yi bai’a ba sai bayan rasuwarta da ya kasance ba shi da wani mai ba shi kariyar siyasa!.

Ta kasance ita ce ta fi kowace mace kamewa a tarihin matan duniya, don haka ne ta tarbiyyantar da kanta da matan zamaninta cewa; abin da ya fi musu kyawu shi ne su lizimci gidansu sai dai gun lalura. Kamewarta ta kasance hatta da makaho tana sanya masa hijabi domin ita tana ganinsa idan shi ba ya ganinta!.

Ita ce tsokar jikin Manzon Allah (s.a.w), don haka ne dukkan halayensa su ne halayen sayyida Zahara (a.s), kuma hatta da tafiyarsa da maganarsa ba su da bambanci da yadda Manzon Allah (s.a.w) yake yin nasa.

Ta kasance ita ce ta fi kowa ibada bayan babanta da mijinta, domin tana tashi har sai kafafunta sun tsattsage, har ma tana kwana tana ibaba ba ta komai sai ambaton Allah da yi wa makota da al’ummar musulmi addu’o’I, hatta da danta Hassan (a.s) yana cewa: “Ya baba! Kin kwana kina salla amma ban ji kin yi wa kanki addu’a ba sai dai makota? Sai ta ce masa: Ya dana; Makoci sannan gida!.

Wannan ita ce Fadima (a.s) mai ibada da zuhudu, da kin zalunci, da tsoron Allah, da kame kai, da kuma kariya ga al’umma, da neman kafa adalci, da yin tsaye gaban duk wani zalunci.

Salman Muhammadi ya ga faci goma sha biyu a jikin kayanta na gashin tumaki sai ya fashe da kuka yana cewa: ‘Ya’yan sarkin Rum da na Farisa suna cikin alhariri da sundus, amma ‘yar Muhammad annabin Allah (s.a.w) tana cikin tufafi masu kaushi kuma da fashi goma sha biyu!?

Ta kasance tana yin nika da hannunta har sai suna kumbura suna yin ruwa, kuma tana shayar da ‘ya’yanta da kanta, tana sanya tufafin da aka yi da fatar rakuma, babanta mai tsira da aminci ya gan ta a wannan halin sai ya ce: Ya ‘yata ki gaggauta dacin duniya da zakin lahira. Sai ta ce: Ya Manzon Allah, godiya ta tabbata ga Allah kan ni’imominsa da gode masa a kan baiwowinsa.

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana fara tafiyarsa da yin bankwana da ita ne, kuma idan ya dawo yana fara shigowa cikin madina da zuwa wurinta ne. Wata rana saboda tarbarsa ta taba sanya wani tufari na Khaibar domin tarbar babanta da mijinta. Yayin da Manzon Allah (s.a.w) ya ga hana sai bai ji dadi ba, da ta fahimci haka, sai ta cire sarkarta da dan kunnenta, da kayan da ta sanya ta aika masa da shi ta ce; ya sanya shi a cikin tafarkin Allah. Yayin da ya ga haka sai ya tausaya mata ya ce: Ta yi abin da ya fi kyawu, babanta fansa ne gareta har sau uku, sannan ya ce: Babu ruwan alayen Muhammad da duniya, domin su an halicce su ne don lahira, an kuma halicci duniya don su ne. A wata ruwayar akwai karin ya ce kuma: Wadannan su ne alayena, ba na son su ci mai dadinsu tun a rayuwarsu ta duniya.

Fadima (a.s) ta kasance matukar gaya wajen ilimi, ta kasance tana amsa tambayoyi cikin sauki, hatta da tambayar da Manzon Allah (s.a.w) ya tambayi sahabbansa game da cewa “mene ne ya fi cancanta ga mace” wata rana suka kasa amsawa sai ita ce ta gaya wa mijinta amsa cikin sauki, shi kuwa ya zo ya gaya wa Manzon Allah (s.a.w) abin da ta ce.

Ta kasance makoma gun mata da maza kan mas’alolin addini, don haka ne ba ta da iyaka ga dukkan mai koma mata don neman amsar tambayarsa. Sannan an ruwaito hadisai masu yawa daga gareta tsira da amincin Allah su tabbata gareta.

 Wata mata ta taba zuwa wurinta ta tambaye ta mas’aloli goma ita kuma tana amsawa, sai matar ta ji kunyar ci gaba da tambaya tana ganin kamar ta tsawaita mata, matar ta ce: Bana son in wahalar da ke da takurawa. Sai Fadima Zahara (a.s) ta ce: Ki tambayi duk abin da kike so, ki sani, ni na ji babana (s.a.w) yana cewa: “Hakika malaman al’ummata ana tayar da su, sai a rika ba su girma daidai gwargwadon yawan iliminsu, da kokarinsu na shiryar da bayin Allah”.

Ta kasance mai tsananin fasaha matuka, A’isha tana cewa: Ban taba ganin wani wanda ya fi kowa kama da Manzon Allah (s.a.w) a magana da zance ba da ya kai Fadima (a.s). Duk wani wanda ya san hikima ya duba hudubarta to zai san kimarta da kimar maganganunta.

Hudubarta mai fasaha da balaga da hikimomi da babu kamarsu ta shahara matuka, alhalin a lokacin ba ta wuce shekaru goma sha takwas ba, amma ta zo da hikimomin da suka dimautar da masu hankula da masu sauraro har a nade duniya, da wannan ne ta cancanci kasancewa kwafi ce ta babanta (a.s).

Kuma ba mamaki gareta domin ita ‘yar babanta ce, kuma matar mijinta, wadanda duniya ba ta haifi kamarsu ba a cikin fasaha da magana ba. Don haka ne maganarta ta kasance mashaya ce da ta bubbugo daga wadannan manyan koguna guda biyu marasa gaba da iyaka, sai ta fesa wannan hasken na hikima da ya mamaye sasannin dukkan ‘ya’yanta tsarkaka tun daga kan Imam Hassan (a.s) har zuwa kan Imam Mahadi (a.s).

Sannan zamu ga abin da ta zo wa duniya da shi na rahama wanda har yanzu kowa yana cin albarkacinsa, yayin da ta nemi a ba ta ‘yar hidima daga cikin bayin da aka kawo da zata taimaka mata a aiki, sai aka ba ta zabi ko tasbihi ko ‘yan aiki, sai ta zabi tasbihi wanda dukkan al’umma zasu amfana da shi har alkiyama ta tashi. Don haka ne bayan salla aka so kowane mai salla ya yi wannan tasbihi, da fara da kabbara 34, da hamdala 33, da tasbihi 33, ga Allah madaukaki wanna kuwa ana kiran sa da tasbihin Zahara (a.s).

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com