Hakkin Zahara



Hujjar Zahra kan Lamarin Fadak

 

Tambaya:

Yayin da suka hana Zahra (a.s) hakkinta, sun nemi ta kawo shedu cewa Fadak tata ce, babu wani da take da su sai Hasan da Husain da Imam Ali (a.s), sai dai mutanen ba su yarda da su a matsayin shedu ba tun da mijinta da 'ya'yanta ne, yaya raddinku game da wannan lamarin yake?

 

Amsa:

Tun farko yana da kyau mu san cewa shin annabi (s.a.w) ya ba wa Fatima (a.s) fadaki ko kuwa?.

An ruwaito daga Ibn Abbas, da Abu Sa'id alKhudri cewa yayin da ayar nan ta sauka ta "... kuma ka ba wa ma'abocin kusanci hakkinsa ...." Isra: 26. Sai manzon Allah (s.a.w) ya kira Fatima (a.s) sai ya ba ta Fadak da Awali, sannan ya ce: Wannan kaso ne da Allah ya ba ki da ke da 'ya'yanki har ranar kiyama. (Durrul mansur na Siyuti 5/273. Ruhul Ma'ani na Alusi: 15/36. Kanzul Ummal: 3/767. Mizanul I'itidal: 2282. Ibn Kasir: 3/36. Siratul Halbiyya: 3/36.

Haka nan Haskan daga malaman karni na biyar hijira ya kawo shi daga Abu Sa'id alKhuduri kamar yadda ya gabata da wata hanya a ruwayar Ibn Abbas (shawahidut tanzil: 1/34, 238, 443.

Kuma Buhari ya ruwaito a littafinsa daga A'isha cewa: Fatima da Abbas sun zo wurin Abubakar suna neman gadonsu na wurin annabi (s.a.w) da kuma Fadak, da rabok Khaibar, sai Abubakar ya ce musu: Na ji manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Ba a gadon mu abin da muka bari sadaka ne, kawai alayen Muhammad suna ci daga wannan dukiyar ne. Sai Abubakar ya ce: wallahi ni ba zan bar wani lamari da na ga manzon Allah (s.a.w) yana yin sa ba sai na yi shi. Ya ce: sai Fatima (a.s) ta kaurace masa ba ta sake yi masa magana ba.

Ruwayar ta fito fili ta yi bayani cewa sun zo suna nemna Fadak, ba ta yi maganar rabonsu ba, kuma ta yi nuni da cewa Abubakar ya hana su ya mamaye ta. Ya kafa hujja da labarin mutum daya wanda babu wanda ya sani sai shi, yayin da babu wani daga cikin masu gadon annabi (s.a.w) da yake da wannan labarin, alhalin Fatima (a.s) ita ce mai daraja ta farko cikin masu gado daga annabi (s.a.w).

Haka nan Abbas da yake mataki na biyu cikin masu gadon annabi (s.a.w) shi ma ba shi da wani labari.

Sannan idan Fadak ta kasance hannun sayyida Zahra (a.s) to Abubakar ba shi da wani hakkin kwace ta hannunta ko neman shedu gunta, domin hujja ita ce wanda abu yake hannunsa. Kuma Imam Ali ya kafa hujja ga Abubakar kan wannan mas'alar, har ma yake gaya masa yanzu kana hukunci gare mu da sabanin abin da Allah ya yi hukunci da shi?

Har inda Imam Ali yake ce masa: Yanzu idan wani abu yana hannun wani musulmi sai na yi da'awar cewa nawa ne, wa zaka tambaya ya kawo shedu? Sai Abubakar ya ce: Kai ne. Sai Imam Ali (a.s) ya ce: Yanzu idan musulmi suna da wani abu sai na yi da'awarsa kana tambayata shedu a kansa hakan, yaya ke nan kake kiran in kawo shedu kan abin da yake nawa da yana hannuna tun lokacin annabi (s.a.w) alhalin ba ka tambayi musulmi su kawo shedu kan abin da ni na yi da'awarsa sai ka nemi in kawo shedu kan abin da na yi da'awarsa!. (Tafsirul Kummi: 2 / 156).

Tare da cewa dukkan musulmi tun daga sahabbai zuwa tabi'ai da wadanda suka zo bayansu sun yi hukunci da shedu da rantsuwa a dukiyoyi, kuma Abubakar kansa an nakalto wannan daga gare shi, to don me Abubakar bai nemi wannan ga sayyida Zahra (a.s) ba?!.

Sannan zamu ga lokacin da suka dage kan sai ta kawo shedu sai ta kawo kusan mutum bakwai ba mutum uku ba, da suka hada da Imam Ali, Ummu Aiman, Rabah yaron annabi, Asma'u 'yar Umais, Hasan, Husain, Ummu Kulsum.

Ga wanda ya koma wa littattafan Futuhul Buldan, Siratul Halbiyya, biharul Anwar, Nahjul balaga, Tafsir Fakhrur Razi.

Sai muka ga an kawo wasu bayanai masu yawa don raddin wannan lamari kamar yadda zamu ga cewa sun kawo amsoshi mabambanta game da amsar da Abubakar ya gaya wa sayyida Zahra (a.s) kamar haka:

Cewa dukiyar ba ta annabi ba ce, kawai dukiya ce ta musulmi.

Wannan lamari ne da bai halatta a samu shedar namiji da mace biyu a cikinsa ba.

Cewa Abubakar ya kawo Umar da Abdurrahma bn Auf sai suka shaida cewa annabi yana raba ta ne.

Cewa shaidar akwai 'ya'yanta a ciki don haka sheda ce mai jawo amfani ba a aiki da ita.

Sai dai muna iya cewa lamarin ya samu yawa ne saboda duk sa'adda sayyida Zahra (a.s) ta kawo wata hujja, sai Abubakar ya kawo mata wani dalilin da zai sanya shi hana ta Fadak (gonarta), don haka ne sai lamarin ya faru da yawa. Don haka ne lokacin da ya ki shedar 'ya'yanta da mijinta, sai ta zo da waninsu, sai ya kira su namiji da mace biyu. Kuma duk abin da ta zo da shi sa su yi musu har dai ta zo da shedu da suka kammala tare da mai hidima ga annabi (s.a.w), sai kuma daga karshe suka bayar da amsar cewa wannan dukiyar ta annabi (s.a.w) ce, kuma Umar da Abdurrahman dan Auf suka bayar da sheda kan hakan.

A nan ne muke cewa duk wata da'awar cewa duk wanda yake da wata sheda da zata kai ga amfani ga kansa ba hujja ba ce cewa shin wannan wani Hadisi ne da babu wanda ya ji shi sai Abubakar kawai, ko kuwa hukunci ne da annabi (s.a.w) ya yi shi da babu wani wanda ya san shi!!

Tare da cewa masu ruwaya da malamai sun yi raddin wannan lamarin. A hadisin nan na A'isha da suka ruwaito shi cewa (sheda ba ta halatta... sai hadisin ya kawo har da wanda ya yi sheda ga amfanin mutanen gidansu ko mai kusanci gare su....) sai Tirmizi ya ce: Wannan hadisin bako ne, ba mu san shi ba sai daga hadisin Yazid dan Ziyad Dimishki, wanda shi kuwa mai rauni ne, kuma ba a san wannan hadisin daga hadisan Zuhri ba sai daga gare shi. Da sauran bayanai da ya gabatar sai a koma wa (sunan Tirmizi 4: 545).

 Sannan sai ga shi suna hukunci da cewa ya halatta mutum ya yi sheda ga na kusa da shi musamman miji ga mata, ban da mata ga miji, suka kafa dalili da shedar Imam Ali ga matarsa Zahra a gaban Abubakar kuma Abubakar ya karbi hakan. Sarakhsi ya kawo wannan daga littafin Mabsut, daga Sufyan Sauri. Yana mai dogara da shedar Ali da Abubakar ya karba ga matarsa sayyida Zahra (a.s) game da da'awar Fadak. (Almabsut: 16: 124).

Tare da cewa zaka iya tambaya cewa: Da shedar miji ga matarsa ba ta halatta ba, don me ya sa Ali (a.s) ya yi, alhalin yana daga masu ilimi!.

Wannan shi ne abin da ruwaya ta zo da shi ba tare da mun kai ga wata natija ba, don haka zai bayyana a fili cewa mai tunani da hankali zai tambaya cewa: shin Abubakar ya yi amfani da dokar shari'a me don ya hana Fatima hakkinta ko kuwa lamarin siyasa ne ya sanya saba wa shari'a da take dokarta don cimma wani hadafi da masu siyasa suke ganin shi ya faye musu maslaha fiye da kiyaye shari'a.