Kwace Fadakaalul-bayt
Hadafin Abubakar na Kwace Fadak
Akwai wasu hadafofin da suka sanya Abubakar da Umar su kwace wa sayyida Zahra gonar Fadak, daga ciki:
1- Rusa karfin tattalin arzikin Ahlul-baiti (a.s) da toshe mu su duk wata kafa ta smaun aikin da ake faro shi daga gidan sayyida Zahra (a.s) domin ba wa halifancin Abubakar kariya, domin a lokacin kudin da Fadak take samar wa sun kai kusan Dinare 24 000, a kowace shekara. A ruwayar shaikh Abdullahi bn Hammad Al'ansar a wata ruwayar sun kai 70 000 (Kashful Mahijja 182), kuma Fadak ta bayar da 10 000, a lokacin Umar dan Abdul'aziz (subhil a'asha 4, 291). An ce kuma ya kai ma dinare 40 000 (sunan Abu Dawud, 3, 144, 2972, Babun fi safaya rasulul-Lah).
Don haka kwace wa sayyida Zahra Fadak ya zama yanke tattalin arzikin sayyida Zahra ne baki daya.
A nan ne zamu ga Ibn Abil Hadid Bamu'utazile Bahanife yana kawowa daga Ali dan Taki cewa: Fadak ta kasance tana da girma matukar gaske, kuma tana da dabinon da ya kai na yawna Kufa, kuma ba don komai Abubakar ya kwace mata Fadak ba sai don tsoron ka da Ali ya samu karfafa da abin da take samarwa na duniya ya samu karfin jayayya da halifa.
Wannan shi ne dalilin da ya sanya suka wahalar da Fatima (a.s) da Ali (a.s) da sauran Banu Hashim da Banu Abdulmutallib ta hanyar hana su hakkinsu na Humusi, domin duk wani talaka da ba shi da dukiya to himmarsa kawai shi ne ya samu abin da zai rayu da shi, kuma zai shagaltu ne kawai da neman sana'a da aibn da zai ci, da kawar da kansa da barin neman jagoranci. (Sharhu bn Abil Hadid, 16, 236-237). 2- Ta wani bangare kuwa zamu ga cewa Abubakar ya dage kan hana Fatima (a.s) Fadak da ya kwace mata ne, saboda idan ya gaskata ta kan mas'alar Fadak to lamarin zai shiga lamarin siyasarsa domin zai kai ta kuma ga neman halifanci hakkin Ali (a.s), don haka ne zamu ga Ibn Abil Hadid yana cewa: Na tambayi Ali dna Alfariki malamain makarantar Algarbiyya da ke Bagdad cewa: Shin Fadima ta kasance mai gaskiya ce? Sai ya ce: haka ne. Sai na ce: don me ya sa Abubakar bai ba ta Fadak ba idan ya san tana da gaskiya? Sai ya yi murmushi ya fadi wata magana mai taushi mai kyau duk da girmansa da karancin raharsa, sai ya ce: Da ya ba ta Fadak a yau saboda ta yi da'awar tata ce, da ta zo masa gobe kuma tana da'awar halifanci ga mijinta da kawar da shi daga matsayinsa, kuma ba shi da wani abu da zai bayar da uzuri kansa, domin ya riga ke nan ya yarda da duk wani abu da take nema da ta yi da'awarsa ba tare da bukatar shedu ko rantsuwa ba. Wannan maganarsa tana da inganci duk da ya kawo ta da sigar raha da wasa. (sharhu nahjul balaga, ibn abil hadid, 16, 284). |