Kwace Fadakal-shia.orgHadafin Abubakar na Kwace Fadak Akwai
wasu hadafofin da suka sanya Abubakar da Umar su kwace wa sayyida Zahra gonar
Fadak, daga ciki: 1-
Rusa karfin tattalin arzikin Ahlul-baiti (a.s) da toshe mu su duk wata kafa ta
smaun aikin da ake faro shi daga gidan sayyida Zahra (a.s) domin ba wa
halifancin Abubakar kariya, domin a lokacin kudin da Fadak take samar wa sun
kai kusan Dinare 24 000, a kowace shekara. A ruwayar shaikh Abdullahi bn Hammad
Al'ansar a wata ruwayar sun kai 70 000 (Kashful Mahijja 182), kuma Fadak ta
bayar da 10 000, a lokacin Umar dan Abdul'aziz (subhil a'asha 4, 291). An ce
kuma ya kai ma dinare 40 000 (sunan Abu Dawud, 3, 144, 2972, Babun fi safaya
rasulul-Lah). Don
haka kwace wa sayyida Zahra Fadak ya zama yanke tattalin arzikin sayyida Zahra
ne baki daya. A nan ne zamu ga Ibn Abil Hadid Bamu'utazile Bahanife yana kawowa
daga Ali dan Taki cewa: Fadak ta kasance tana da girma matukar gaske, kuma tana
da dabinon da ya kai na yawna Kufa, kuma ba don komai Abubakar ya kwace mata Fadak
ba sai don tsoron ka da Ali ya samu karfafa da abin da take samarwa na duniya
ya samu karfin jayayya da halifa. Wannan shi ne dalilin da ya sanya suka wahalar da Fatima (a.s) da
Ali (a.s) da sauran Banu Hashim da Banu Abdulmutallib ta hanyar hana su hakkinsu
na Humusi, domin duk wani talaka da ba shi da dukiya to himmarsa kawai shi ne
ya samu abin da zai rayu da shi, kuma zai shagaltu ne kawai da neman sana'a da
aibn da zai ci, da kawar da kansa da barin neman jagoranci. (Sharhu bn Abil
Hadid, 16, 236-237). |