Ranakun WaliyyaiRuwayoyi da dama sun zo a kan haka, don haka kawo dukkansu a nan zai sanya mu tsawita, don haka zamu wadatu da wannan. Babu shakka wadanda suke yin bukukuwa a ranar haihuwar Manzo ba su da wata manufa wacce ta wuce nuna soyayyarsu ga Manzo, a hakikanin gaskiya suna amfani da wannan bukukuwa ne don su bayyanar da soyayyarsu ga manzon Allah (s.a.w) Kur’ani yana bayar da umarni a kan cewa musulmai bayan sun yi imani da Manzo wannan bai wadatar ba sai sun nuna girmamawarsu ga Manzo, ga kuma abin da Kur’ani yake cewa: “Wadanda suka yi imani suka kuma girmama shi kuma suka taimake shi, sannan suka bi hasken da aka saukar masa tare da shi, wadannan su ne masu babban raboâ€[5] Wannan aya tana bai wa musulmi umarni guda hudu kamar haka: 1-Su yi imani da Manzo. 2-Su girmama shi. 3-Su taimaki Manzo. 4-Su bi hasken da aka saukar masa tare da shi. Tare da la’akari da wadannan umarni guda hudu, girmama Manzo a ranar haihuwarsa, yana nuna aiki ne da umarni na biyu, wanda ake magana a kan girmama Manzo. Kur’ani yana bayyanar da cewa daya daga cikin ni’imomin da Allah ya yi Manzo shi ne ta yadda ya daukaka shi kamar yadda ayar Kur’ani take cewa: “Shin a mu ne muka yaye maka kirjinka ba, sannan muka cire nauyin da yake kanka, nauyin da yake gab da ya karya maka kashin baya, sannan muka daukaka ambatonkaâ€[6]. Tare da la’akari da abin da Manzo Allah yake cewa dangane da Manzo (s.a.w) ta fuskar daukaka sunansa da ambatonsa a duniya, kuma yana kidaya wannan daya daga cikin ni’imomin da Allah ya yi wa manzonsa, don haka bukukuwa da musulmai suke yi ranar haihuwarsa suna daya daga cikin aiki da abin da wannan aya take umarni da shi. Saboda haka tare da kula da ayoyin da hadisan da aka ambata a sama, idan har muslmai ba su hada wadannan bukukuwa ba ayyukan haram kamar abin da ya shafi kide-kide na haram da wakokin da ba su dace ba, to menene hukuncin wannan? Shin girmama Manzo ne ko kaskantar da shi? Nuna soyayya gare shi ne ko nuna kiyayya? Shin yana daya daga cikin daga sunan Manzo da tunawa da shi ko kuwa ba ya daga ciki?
|