Neman Tabarruki2



Neman Tabarruki Da Manzo Da Abin Da Ya Bari 2

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Abin Da Yake Janyo A Nemi Tabarruki

Abin da yake janyo a nemi tabarruki daya daga cikin abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Kwararowar ni’imar Ubangiji wacce wani lokaci take samuwa ta hanyar da ba ita aka saba da ita ba, dangane da wannan mun kawo misalai a baya.

2-Soyayya da kaunar iyalan gidan manzanci, da sahabban Manzo, wannan kuwa yana daga cikin umurnin Kur’ani mai girma, babu shakka kuwa so da kauna suna bukatar inda za a bayyanar da su, wurin da za a bayyanar da wannan soyayya kuwa a wurinsu yayin da suke a raye, kamar yadda ya kasance wasu mabiyasu na gaskiya sun aikata hakan. Amma lokacin da ba su raye tare da mu kuwa akwai wuraren da ya kamata a nuna wannan soyayya gare su, kamar tunawa ta ranar haihuwarsu, sannan yin bakin ciki da tuna ranar wafatinsu, sannan yayin da mutum ya je a kaburburansu ya sumbaci bangaye da kofofin kabarinsu, dukkan yana samun tushe ne daga soyayya gare su, wacce take tun tsawon tarihi a cikin zukatan musulmai. A hakikanin gaskiya wannan gungun mutane wadanda suke sumbatar kabarin annabi da nuna kauna ga duk wani abu da ya shafe shi, wannan duk suna nuna soyayyarsu ne ga shi kansa Manzo, amma yanzu hannunsu ba zai iya isa zuwa gare shi ba, saboda haka ne suke nuna soyayyarsu ga duk abin da ya bari ko kuma a ka jingina shi zuwa gare shi.

Wuraren zayara duk da cewa a zahiri bai wuce dutse da katakai ba, amma soyayyarmu garesu tana nuna tsananin yadda muke son wanda yake a ciki wato manzon Allah (s.a.w) da A’immatu Ahlul bait (a.s) kuma jingina wadannan duwatsu ga annabi ko imamai ya sanya suka samu wata daraja da tsarki na musamman. Lokacin da zuciya ta zama gidan soyayyar wani masoyi, ma’abucin wannan zuciya yana farin ciki da jin sunan ko ya ga, tufafi, hankici, takalmi, garin masoyi ko tunawa da duk wani abin da ya shafi wannan masoyi na shi, sannan kuma yana ganin wannan masoyin cikin wadannan abubuwan.



1 2 3 4 next