Girmama Kaburbura Masu TsarkiMaimaita wannan mummunan al’amari dangane da musulunci yana da matsala fiye da yadda ya faru a sauran addinan da suka gabata. Domin kuwa addinin musulunci addini ne wanda har zuwa ranar tashin kiyama dukkan mutane dole ne su yi biyya a gare shi, ta yadda zasu sadu da haske ta hanyar hakan. Mutanen da zasu zo nan gaba kuwa zasu iya biyayya ga wannan addini yayin da suka kasance sun samu yakini dangane da hakikaninsa. Babu shakka daya daga cikin hanyar kiyaye wannan tabbaci na hakikanin addinin musulunci kuwa shi ne kiyaye abubuwan da suka shafi rayuwar Manzo da sauran shugabannin addinan musulunci. Magabatanmu Allah ya rahamshe su, sun yi hidima mai yawa dangane da al’ummar yanzu, ta yadda suka kiyaye mana abubuwan da suka zo tun farkon zuwan musulunci. Sakamakon haka ne kai tsaye muke kiran sauran al’umma zuwa ga wannan addini wanda yake hakikaninsa bai samu wani canji ba, ta yadda muke cewa: Karni goma sha hudu ne da suka gabata shugaban Bani Hashim ya ta shi da manzanci daga Allah ya kuma kira mutane zuwa ga Tauhidi da kaurace wa bautar gumaka da kafirci, bayan Mu’ujizozin da ya zo da su, sannan ya zo da littafi mai girma wanda ya karya makiyansa da shi, sannan har zuwa yanzu wannan Mu’ujizata har abada tana nan ba tare da wani canji ba. Wanda kafin ya fara bayyana kiransa ya kasance yana tafiya kogon hira domin yin ibada ga Allah madaukaki. Bayan cika shekara arba’in da rayuwarsa ya fara kiransa, wasu mtane daga cikin mutanen Makka suka yi imani da shi, yayin da wasu mafi yawa suka kaurace masa, har ma suka yi nufin su halaka shi, amma Allah da ikonsa ya boye shi a wani kogo da ake kira (Thaur) wanda yake kudancin garin Makka, ta yadda ya tsira da makiya. Bayan nan kuma ya yi hijira zuwa garin Madina, a wannan gari ne mutane Aus da Khazraj (wadanda ake kira da Ansar) suka amsa kiransa suka taimake shi. Manzo a tsawon zamansa a garin Madina ya gwabza yaki mai tsanani tsakaninsa da mushrikai da Yahudawa, Ta wannan hanyar ne ya gabatar da shahidai da dama a tafarkin Allah ta yadda suka ba da jinansu a yakin Uhud, Khaibar da Hunain. Manzo (s.a.w) ta hanyar aika mabiyansa zuwa sassa daban-daban na wannan nahiya ta kasashen larabawa ya samu damar isar da sakonsa zuwa ko’ina a wannan lokaci. A shekara ta 11 ne bayan hijira ya koma zuwa ga ubangijinsa kuma ya yi umarni da rufe shi a cikin dakinsa, bayan wafatinsa mabiyansa suka cigaba da hanyar da ya bari, ta yadda ba tare da bata lokaci ba, ya yada wannan addini tare da al’adun da Kur’ani ya zo da su a dukkan sassan duniya. Wannan shi ne wani yanki na tarihimmu wanda bayan wucewar karni 14 ake Maimaita shi. Saboda haka dole mu yi kokarin wajen kare wannan tarihi na mu da duk abin da ya shafi hakan, ba wai ta hanyar wasu dalilai ba marasa tushe mu ruguza wannan tarihi na mu!. Kmar yadda ya kasance mu shagala game da kiyaye wadannan kayan tarihi, ta yadda babu bambanci a wurin dangane da samuwarsa da rashinsa duk daya yake, (abin da ma ya fi muni shi ne yadda ake ganin cewa rusa wadannan abubuwa yaki ne da yaduwar shirka) Ta yadda acikin kankanen lokaci an manta da wasu abubuwa na tarihin musulunci, don ha ka bayan wani lokaci zai yiwu a fara shakku dangane da wasu abubuwa na hakikanin wannan kira da Manzo ya zo da shi. Ta yadda kamar su Salman Rushdi mai makon canza addini sai ya yi kokarin inkarin addinin da tarihinsa baki daya.
|