Mutum na Gari




Da Sunan Allah
Daga littafin Ihtijaj na Dabarasi, Mansur Ahmad dan Abi Dalib Addabrasi , da sanadinsa zuwa Imam Hasan al'Askari (a.s) daga Imam Ridha (a.s) ya ce: Aliyyu dan Husain (a.s) ya ce:

Yaudara da Ci da Addini a Zahiri
Idan kuka ga mutum yanayinsa da basirarsa sun kyautata, yana kaikaice maganarsa, da nuna kaskantar da motsinsa, to ku yi a hankali kada ya rude ku, sau da yawa a kan samu wanda samun duniya da hawa kan haram yake yi masa wahala saboda raunin niyyarsa, da wulakantuwarsa da tsoron zuciyarsa, sai ya nuna addini a matsayin tarkonsa, shi ba ya gushewa yana yaudarar mutane da zahirinsa, idan kuma ya samu damar aikata yin haram sai ya fada masa.

Dukiya da Mata
Idan  kuwa kuka same shi yana kamewa daga haram to (har yanzu dai) ku yi a hankali kada ya rude ku, domin lallai sha'awowin halittu suna sassabawa, sau da yawa wani wanda yake nisantar dukiyar haram komai yawanta, (amma) kuma (da zai samu dama, da) ya dora kansa (ya hau) kan wata mummunar mata mai muni (duk muninta) sai ya aikata haram (na zina) tare da ita.

Samuwar Hankali
Idan  kuwa kuka same shi yana kamewa daga wannan (zina) to (har yanzu dai) ku yi hankali da shi kada ya yaudare ku har sai kun duba hankalinsa, sau da yawa wani ya bar wannan duka amma ba shi da wani hankali mai karfi, sai ya kasance abin da yake batawa da jahilcinsa ya fi abin da yake gyarawa da hankalinsa.

Son Zuciya
 Amma idan kuka sami hankalinsa mai karfi ne, to (har yanzu dai ku yi hattara da shi) ku yi hattara dai kada ya yaudare ku har sai kun ga shin yana tare da son ransa a kan (watsi da) hankalinsa, ko kuma yana tare da hankalinsa ne a kan (watsi da) son ransa.

Son Shugabanci Barnatacce
Sannan yaya sonsa yake ga shugabanci na barna da nisantarsa gareshi. Hakika a cikin mutane akwai wanda ya rasa duniya da lahira, yana barin duniya don duniya, yana ganin dadin jagorancin barna ya fi dadin dukiyoyi da ni'imar halal da aka halatta, sai ya bar wannan duka don neman jagoranci har sai idan aka gaya masa cewa ka ji tsoron Allah, sai girman kai ya kwashe shi da barna, to wutar jahannama ta wadatar masa, kuma tir da makoma .
Yana mai gangara kawararo gaba gadi, farkon barna tana jansa zuwa ga mafi nisan matukar tabewa, kuma ubangijinsa yana mai barinsa da kansa bayan nemansa ga abin da ba zai iya masa ba a cikin taurin kansa, shi yana mai halatta abin da Allah ya haramta, yana mai haramta abin da Allah ya halatta, ba ruwansa da abin da ya kubuce masa na addininsa idan dai shugabancin da ya tabe saboda shi ya kubuta, wadannan su ne wadanda Allah ya yi fushi da su ya la'ance su kuma ya tanadar musu da azaba mai wulakanci .

Mutumin Kwarai
Sai dai mutum cikakken mutum, madalla da mutumin da yake sanya son ransa kan biyayya ga umarnin Allah madaukaki, kuma karfinsa ya kasance ya bayar da shi cikin yardar Allah, yana ganin kaskanci tare da gaskiya shi ya fi kusanci zuwa ga daukakar har abada a kan daukaka cikin barna.
Kuma ya san cewa mafi karancin abin da zai iya jurewa na cutuwarta (duniya) zai kai shi ga dawwamar ni'ima ne a gidan da ba ya rasuwa ba ya karewa (lahira), kuma mafi yawan abin da yake samun sa na farin cikinta (duniya) idan ya bi son ransa zai kai shi ga azabar da babu yankewa gareshi babu gushewa (a lahira), to wannan mutumin madalla da shi (ya cika) mutum, da shi ne zaku yi riko, kuma ku yi koyi da sunnarsa (aikinsa), kuma ku yi tawassali da shi zuwa ga ubangijinku, domin shi ba a mayar masa da addu'a, kuma ba a hana shi abin da ya nema.
Hafiz Muhammad Sa'id
hfazah@yahoo.com
www.hikima.org
Tuesday, May 24, 2011