Hakkin Hajji



Hakkin Hajji
Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Kuma hakkin hajji shi ne ka san cewa shi zuwa ne ga ubangijinka, kuma gudu ne daga zunubanka, kuma da shi ne za a karbi tubanka, da sauke nauyin wajibi da Allah ya wajabata maka shi a kanka".
Hajji ibada ce mai sirri matuka, kuma ya hada dukkan wani abu day a shafi ibadar allah madaukaki kamar salla, ambaton allah madaukaki, da 'yan'uwantaka tsakanin musulmi, da sadaukar da kai da dukiya, da taimakon bayin allah, kuma taro ne da yake nuna wa musulmi makomarsu ta shekara, da tattauna matsalolin da suke fama da su domin magance su.
Sai dai mafi girma a nan shi ne hajji mahada ce domin ganawar musulmi da imamansu na shiriya, kuma wannan shi ne babban kololuwar ma'anar hajji da dalilin da ya sanya wajbta shi a kan mutane gaba daya, musulminsu da kafiransu.
Ruwayoyi masu yawa sun zo suna masu tunatar da al'ummar musulmi cewa daga cikin cikar hajjinsu shi ne su ziyarci imaminsu su gana das hi, a lokacin manzon allah saw shi ne wannan imamin nasu wanda yake shi annabi ne, a lokacin wasiyyansa tun daga imam ali as har zuwa imam mahadi as kowanne a zamaninsa shi ne makomar al'umma bayan hajji domin su san umarni da sakon shekara daga gareshi.
Sai dai kaico! Sai mutum ya tausaya wa al'ummar musulmi domin da yawa sun je hajji amma sai suka yi hajijiya ba su san me ye sirrin da yake cikinsa ba, sai suka dauka sun je kallon makka ne da ka'aba da duwatsun da suke kasashenmu.
Sau da yawa nag a mutane wadanda suke yawo a titinan makka amma idan ka tambaye sub a su san hadafin yin hajji ba, bas u san sirrin rayuwarsu ta dan wannan lokacin ba, bas u san komai na hukuncinsa ba, sannan masu kula da sha'aninsu bas u damu das u ba, kais u ma bas u san komai ba game da wadannan mas'alolin.
A hajjin shekarar 1426 na yi jawabi game da hajji a kusa da masaukin alhazan kano da zamfara, sai wani bawan allah daga cikin muminai bayan na fadi sirrin yanka da dawafi da safa da marwa sai yake cewa da ni; na zo hajji lokuta masu yawa, amma sai yanzu na fahimci me ake nufi da hajji.
Sirrorin da suke cikin dawafi, da safa da marwa, da yanka layya, da taron al'umma, da ambaton allah, da sanayya tsakanin juna, da taron mutane masu launuka iri-iri dukkan wannan yana nuna mana hikimar allah a wannan taro. Taro ne wanda ya yi kama da na lahira a wani lokaci, daya daga cikin abin da nake tunawa shi ne yayin da na ga malamina da kaya ya yin barin masha'ar sai na so in karba, amma sai na kasa karba domin idan na karba sai dai idan zan jefar da nawa ne, sai wannan ya tuna mini lahira da cewa kowa zai shagaltu da abin day a dame shi ne.
Hajji wuri ne da yake nuna mana kaskan da kai, da yarda dukkan wata mummunar dabi'a, da jefar da bambancin kabilanci, da wurgi da kimar duniya ta sarauta sai ga allah kawai, da kawar da dukkan sabo. Wuri ne da ake nuna godiya ga allah day a hada mu kan addini Ibrahimi wanda ya karkace daga dukkan addini na bata sai dai na gaskiya.
Shagaltuwar mutum da kansa ta nuna cewa duk da kuwa akwai mata da maza a cakude amma babu wani wanda yake kula da cewa yana kusa da dayan ne. namiji bay a kula da na kusa da shi mace ce, kamar yadda ita ma bat a kula da na kusa da ita namiji ne.
Taro ne wanda yak tuna mana sadaukarwar Isma'il da Hajar a wannan sahara a kusan shekaru dubu hudu zuwa biyar da suka wuce, sai mutum ya tuna sadaukarwar da suka yi. Sannan kuma ya sadaukar da kansa ga allah kamar yadda Isma'il as ya mika wuyansa ga allah domin a yi layya das hi, ya sadaukar da kansa da juriya kamar yadda Hajar ta jurewa kishirwa a wannan duwatsu masu zafi tsakanin safa da marwa domin neman yardar allah madaukaki.
Sai a yawaita ambaton allah a hadu da juna ana masu tausaya wa juna da neman sanin juna domin hada zumuncin musulunci kamar yadda Adam as da Hawwa suka hadu a duwatsun Arfa. Sai a yawaita addu'a musamman addu'ar imam Husain a wannan dutse kafin ya fita daga makka saboda tsoron sharri azzaluman yaran 'yan barandan Yazid.
Sannan kowane gewaye a gefen ka'aba guda bakwai yana daukaka mu ne zuwa ga allah kamar matattakalai ne na hawa sammai har guda bakwai, sannan sai a nufi makamu Ibrahim as domin yin salla da gudiya da addu'a da neman a wurin ubangiji mai duka.
Hajji wuri ne da ake kauce wa sha'awar duniya da nutsewa cikin kogin ganawa da allah madakaki, da ninkayo cikin tekun ambaton allah domin nemo lu'ulu'un zaman samuwar duniya don keta haske zuwa ga rayuwar daukaka mai dawwama. Don haka ne mai hajji yake kasancewa kamar mutum ne wanda yake rayuwa tsakanin duniya da lahira, yana samun kansa tsakanin zahiri da badinin samuwarsa, ba shi da komai sai kyallaye biyu kawai masu kama da likkafani!.
Sai aka haramta masa wasu abubuwan da ba don hajji ba su halal ne gareshi, domin kawai ya dulmuya cikin kogin jin dadin ganawa da allah sai aka haramta masa auren mace ko kusantar mace mafi dadin abin rayuwar duniya, aka hana shi turare da dukkan kayan adon duniya na more rayuwa masu sanya shi annashuwa, kuma aka hana shi cutar da komai, aka hana shi kawar da gashin kansa da jikinsa da sauran dokoki da iyakoki masu kangewa.
Amma teburin tattaunawa tsakanin musulmi domin warware matsalolin duniyarsu da lahirarsu, da taimakon junansu, wannan kofa ce da su musulmi suka to she ta, ta yiwu babu mai iya bude ta sai bayyanar imam mahadi as. Tausaya wa juna kuwa tuni aka yi wurgi da shi a kwandon sharer tarihin musulunci, hakika na yi kuka a wurin jifan shedan da wurin dawafi yayin da na ga al'ummar musulmi kowa yana ta kansa, babu mai tausaya wa waninsa, babu rahama a tsakaninmu, sai dai kawai Kaina! Kaina! magana kan hajji tana da yawa matuka, sai dai zamu dakata a nan, da fatan allah ya ba mu katari da dacewa, da ikon sauke wannan farali mai daraja.
Aikin hajji wa wannan zamani yana daga cikin abubuwan da suke da matukar muhimmanci a zaman tare na al'umma da tattalin arziki, da alkar siyasa tsakanin al'ummu da kasashe, wuri ne mai muhimmnci domin haduwar al'ummar musulmi da tattauna matsalolin rayuwa da suke addabar su. Sai dai kash! abin takaici al'amarin ba haka yake ba, domin duniyar musulmi bayan ta bar wasiyyar annabi (s.a.w) ta yin riko da littafin Allah da alayensa wasiyyansa kamar yadda ya zo a ruwaya mutawatira, sai suka kasa maye wannan da wani abu makamancinsa domin babu shi, don haka sai kaskanci ya mamaye su, marasa kishinsu suka maye gurbin jagoranci wadanda babu tausayin al'ummar a zukatansu, kuma suka riki jahilai a matsayin malamai kamar yadda wasu ruwayoyi suka yi nuni da karshen zamani da abin da zai faru.
Don haka sai dimuwa da rikirkicewa suka mamaye su, tsoro ya lullube su, rashin hadin kai da rashin tausaya wa juna ya shige su, sai suka fada cikin faganniya da ba wanda ya san karshenta sai Allah madaukaki. Alamomi suna nuna fushin Allah da wannan al'umma sakamakon kaskancin da ya fada mata, wannan kaskancin kuwa ya zo ne domin ta bar hanyarsa, kuma ba shirye take ta koma kana bin da yake so ba, sai son Allah ya kasance abin da al'umma take ki, kin Allah kuwa ya kasance abin da al'umma take so, Allah kuwa ba ya canja wa mutane abu sai sun canja wa kansu.
Babu wata hanya da Allah ya toshe mana domin samun sauki da shiriya, sai dai su mutane ne suka toshe ta da kansu, sai dai Allah ya yi mana ludufin cewa idan muna son koma wa wannan hanya tasa kofarsa a bude take, wannan shi ne babban buri da falala da ni'imar da Allah ya yi mana a rayuwarmu. Babban hadafin hajji shi ne al'umma bayan ta gama dukkan abin da take yi na aikin hajji sai ta koma wurin imaminta jagoranta wanda Allah ya sanya mata domin sanin mene ne aikin da zasu yi a wannan shekarar. Sai dai al'ummar nan ta yi watsi da wadannan jagorori har ta sanya boyuwar na karshensu saboda tsoron kisa daga su kansu musulmin, Imam Mahadi (a.s) ya boyu kuma ba zai bayyana ba har sai ranar da umarnin Allah ya zo na hikimarsa sai ya bayyanar da shi domin cika wannan duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.
Aikin hajji wuri ne da jagoran al'ummar musulmi a duniya zai ba su umarni da matakai da zasu dauka a duk fadin duniya, wadannan matakan suna iya yiwuwa na alaka da wasu kasashe ne, ko kuma na kasuwanci, ko na tsaro, ko na ilmantarwa, ko na sha'anin makomarsu ta lahira, da sauran matakai da zasu dauka. Sai dai kaucewa wannan hanya ta wasiyyar annabi da makomar da al'umma zata koma ya sanya su kara zube babu wani wanda zasu koma zuwa gareshi a bayan hajji domin sanin wannan.
Jahilcin da aka jefa al'umma game da addininsu ya sanya miliyoyinsu ba su san hikimar hajji ba, sai masu jagorantar su zuwa hajji suka kasance tamkar makafi ne da suke jan makafi. Wannan lamarin na fahimce ne sosai sakamakon wata lacca da na yi game da hikimar yin hajji a 1426 kusa da kamp din alhajan Kano da Zamfara a kwanakin Mina da suke kusa da garin Makka mai girma.
Na yi bayani game da hadafin sanya hajji ga mutane kamar yadda sayyida zahara (a.s) ta kawo a hudubarta, da kuma hikimar yin safa da marwa, da yin layya, da zuwanmu mina, da jifan shedan, da sanya tufafi irin wadannan, da yadda wurin yake kama da lahira. A nan ne wani alhaji ya yi godiya, ya ce mana ya yi hajji sau da yawa a rayuwarsa, amma bai taba fahimtar hikimar yin hajji ba sai a yau.
Alhazan Nigeria suna daga cikin alhazawan da babu wani wanda ya kai su rashin tsari sakamakon babu wata makoma ta gari da zasu koma mata domin sanin abin da ya dace su yi, a cikin abin da na gani a shekarun 1426, da 1429, zamu ga muna da abin takaici idan aka kwatanta da wasu kasashe tun daga nau'in wurin zama da gidajen da muke rayuwa a matsayin alhazan Nigeria, har zuwa kayan rayuwa da jin dadi da ake tanadar mana, da kuma motocin da zasu taimaka mana zirga-zirga, da ma adreshin wurin da ake ajiye alhazan Nigeria.
Magana kan wannan lamari tana bukatar littattafai masu yawa, domin idan ana son fayyace abubuwan da suke faruwa to zai bukaci littattafai masu yawa. Ina tuna wahalhalu kawai da muka sha domin kai mutanen da suka bata wurinsu saboda Allah ba don aikin an dora mana shi ba, to wannan kawai ya ishe mu yin littafi. Sai ka ga alhaji ko hajiya sun bata amma abin takaicin shi ne a jikin hannunsu abin da aka sanya musu na adreshin ba adreshin wurin zaman su ba ne, adreshin wurin masu kula da alhazawan ne, sai kuma ka kai su can sai a yi maka wani irin kwatancen wurinsu mai nisa daga nan ofishin. Allah dai ya sawwake wa alhajin Nigeria!.
Alhajin Nigeria bai samu girmamawa daga masu kula da shi ba, balle mu yi tunanin ma'aikatan hajji na saudiyya su kula da shi yadda ya dace. Wanda akan wulakanta alhaji daya na Nigeria kawai ya kamata a yanke alaka da kasar saudiyya har sai ta bayar da hakuri, kuma a yanke zuwa hajji har sai sun yarda da mutanta al'ummarmu. Amma sai rashin kimanta alhaji ya fara daga gida, don haka yaya kake tsammanin na waje ya girmama shi. dan Nigeria yana ganin motar Nigeria komai wahalar da ya sha ba zata dauke shi sai idan dan wani ne wanda yake mai matsayi da mukami ko wani ma'aikaci da zai yi masa hanya, dan Nigeria ba zai ga wani abin more rayuwa daga gwamnatinsa ba kamar yadda yake ga sauran kasashe. Mafi muhimmanci shi ne kare mutuncinsa da kimarsa, wani abin mamaki hatta da kotun saudiyya idan ta kama kowane dan kasa da laifi tana jiran sai dole kasarsa ta daukar masa lauya ta tabbatar da ya yi laifi sannan a iya hukunta shi, amma ban da maras gada da kima wanda hukumarsa ba ta san mutuncinsa ba kamar dan Nigeria. Kuma gwamnatin saudiyya ta taba fuskantar fushin niger saboda ta yi hattara da taba wani dan niger ba da yardarta ba.
Babu wani abin da ya ba ni mamaki sai abin da na gani a 1429 na wulakanta kai da rashin hadin kai daga su kansu 'yan Nigeria a mash'ar, yayin da wata budurwa 'yar Kano mazauniya Saudiyya mai suna hawwa da wani mutum dan niger yake son ta amma ta ki shi, sai kawarta ta ce da ita ki yi hattara kin san dan niger ne, sai ya yi miki wulakanci ya yi miki duka a banza. Da na ga alamar tsoron hakan tare da ita sai na ce me ye na jin tsoro haka? Sai ta ce: Malam kai ba saudiyya kake ba? Sai na ce: Na zo aikin hajji ne. Sai ta ce: Lallai ai mu muna jin tsoron dan niger, saboda sai su taru su yi maka duka ko kai ke da gaskiya idan ka yi fada da dayansu, kuma 'yan Nigeria suna kallo sai dai a kashe ka!.
Wani wulakanta kai mai cin rai da na gani a 1426 shi ne yawan masu bara, dukkaninsu ko kusan kashe 95 % daga Nigeria suke. Sai dai na ji dadi matuka da na shafa ban gan su ba a 1429, sai wani yake ba mu labari gwamnatin Nigeria da ta Saudiyya ce suka yi hadin gwiwa domin kwashe su gaba daya. Amma a shekarar 1426 mun sha kunya wurin abokanmu na sauran kasashe da muka je yin aikin hajji tare da su. Sai dai ba kawai a Saudiyya ba, kamar yadda gwamnatin Nigeria ta yi wannan kokarin a saudiyya, muna fatan nan da 'yan shekaru wannan mummunar dabi'ar ta bara mu ga ta kau daga arewacin Nigeria. Bara ba addini ne ba ne kaskanci ne, amma sai ga dan kudu ya dauka addini ne, har ma yana iya yi wa dan arewa isgili da shi, kuma mafi muni sai aka samu wasu jahilai masu kiran kansu malamai suka ba shi halacci, sai wannan mummunan kaskanci ya ki kawuwa.
Babu abin da ya sanya ni yin kuka a wurin jifan shedan sai irin wulakanta juna da nake ganin yana faruwa daga musulmi, sai duniyar musulmi suna wulakanta juna, kowa yana dauka da zafi kamar ya zo fada ne ba aikin ibada da nuna tausayi da kauna ga juna ba, ta yadda a jikin ka'aba sai a yi fada da zage-zage tsakanin wani musulmi da wani, idan ba ka sanya hakurinka ya wuce 100 % to lallai kana iya bugawa da wani musamman idan kana jin yarurruka daban-daban, sai ka ga babu rahama tsakanin juna, babu tausayin juna. Idan kana son magana kan yankin gabas ta tsakiya musamman da ya hada Indiyawa, da Pakistanawa, da Iraniyawa, da Turkawa fadi abin da ka ga dama, magana a nan ne take tsawaita. Sai dai kowane mutane suna da ta su matsalolin, mutanen Afrika suna da nasu matsaloli, wadancan yankuna suna da nasu.
Wasu mutanen kasashe suna wulakanta dan Afrika da Ba'indiye ne saboda suna ganin su kazamai ne, domin mutane ne idan ka je yankunansu sai ka daure saboda rashin tsafta. Wani baturke ya yi da'awar cewa Afrikawa ba su da hankali da kunya saboda kawai ya ga wasu suna kashi da fitsari a bakin titi suna masu fuskanto da al'aurarsu wurin mutane babu ko kunya!.
Muna hada gwamnatocinmu da Allah da kada su bari wani ya ketara aikin hajji sai sun yi masa bayanin wayarwa (orientation) kafin ya wuce kasa mai daraja domin aikin hajji, da yawa na ga wanda ya yi safa da marwa sau 14 maimakon 7, domin ya dauka zuwa da dawowa ne daya. Na ga wasu Fulani da suka ki yin dawafi wai yana da wahala za a kashe su ko a matse su. Don haka yana da kyau duk mutane kamar arba'in ya kasance akwai mutum daya masani, wayayye, mai tausayi, mai juriya da hakuri, mai iya mu'amala da mutane wanda zai gan su a matsayin 'yan'uwansa, wanda zai rika yi musu bayanin al'amuransu kullum, ya rika koma masu kullum domin amsa tambayoyinsu da binciken abubuwan da suke damun su.
Koyarwa da wayarwa ga alhazawan Nigeria amana ce da take wuyan gwamntocinmu, kuma wannan amana ce da zata ci duk wanda aka dora wa ita kuma ya yi sakaci da ita, sannan mu sani akwai hisabi kan dukkan wanda ya fada cikin wannan barna da sabon. Sannan su kuma al'umma yana da kyau su san cewa suna da hakkin kan hukumarsu da duk wanda aka sanya shi a matsayin mai kula da hakkinsu sannan ya ci amanarsu, don haka suna da hakkin neman sa da hkkokinsu idan bai kiyaye ba koda kuwa ta hanyar kotu ce.
Sannan akwai wata mas'ala da na so yin nuni da ita wacce ta shafi alhazawa da suke zuwa umara duk shekara alhali ga makotansu cikin yunwa ko takalmi ba sa iya saya musu! Mu sani da mutum ya je umara kowace shekara gwara ya taimaka wa talakawan da suke gefensa kowace shekara, ko ya taimaka wurin gina makarantu da wannan arziki da Allah ya yi masa. Ko da yake da zai hada biyun da ya fi kyau, sai dai ba mu ga haka ba a wurin mafi yawan mutane, ta yadda akwai wanda ba shi da abincin da zai ci a wuni, amma dan'uwansa ya tafi umara ko kwanon hatsi bai iya ba shi ba, tare da kuwa ya san halin da yake ciki!.
Idan muka juya game da kimar alhazawan Nigeria a Saudiyya, sai mu yi nuni da cewa; hakki ne da ya rataya kan gwamnati ta tabbatar da hakkin alhazawanta. Mafi muni shi ne yadda zamu ga duk shekara alhazawanmu suna zaman kwanakin Mina a cikin karsen Muzdalifa ne, wannan kuwa yana tasiri kan aikin hajjinsu, domin duk wanda bai yi kwanakinsa a Mina ba, to dole ya yi yankan FIDIYA, sai dai waye zai lurasshe da alhazawanmu kan hakan, gwamnati ba ta yi, malamai ba su yi ba!
Don haka hakki ne da ya rataya kan malamai su wayar da kan alhazawanmu, ita kuwa gwamnati ta kwatar musu hakkinsu, ta tabbatar da duk wani abu da ake yi wa alhazawan sauran kasashe na hakkinsu an ba su shi, sannan idan wani daga ciki ya fada wani hali, ko kuma aka kama shi a matsayin mai laifi a Saudiyya to dole ne ta daukar masa Lauyansa domin kare 'yancinsa har sai ta bayyana cewa ya yi laifin. Idan kuwa aka sake a zartar masa da hukunci ba tare da sanin ta ba, to a kan mutum daya yana da kyau ta nuna fushinta ko da kuwa ta hanyar yanke alaka ne da huldar jakadanci!.
Hafiz Muhammad Sa'id
www.hikima.org
hfazah@yahoo.com
Monday, January 03, 2011