Hakkokin Allah
Hakkokin Allah Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: “Amma hakkin Allah mafi girma, shi ne ka bauta masa, ba ka yi tarayya da shi da wani abu, idan ka yi haka da ihlasi, to Allah ya daukar maka alkawari a kansa cewa zai isar maka lamarin duniya da lahira, kuma ya kiyaye maka abin da kake so daga cikinsuâ€‌. Imam Sajjad (a.s) ya nuna mana mafi girman hakkin Allah (s.w.t) da cewa shi ne a bauta masa da ikhlasi, wannan kuwa yana nuni ga haramcin yin shirka da wani tare da shi a cikin ibada. Idan mun duba a nan zamu ga kalmar hakki tana nufin wani abu da yake mallakin wani ko wasu. Da kalmar Allah da take nufin sunan mahaliccin bayi. Da kuma bauta da take nufin rusuna wa wani da imani da cewa shi ne ubangiji wanda yake sama da komai. Kadaita Allah (s.w.t) wani abu ne wanda yake hakki ne nasa , kuma ma’anar kadaita shi tana nufin kore imani da duk wani abu wanda zai kasance tsaransa a kowane abu, kamar a zatinsa da siffarsa, ko a aikinsa da ibadarsa. Sannan yana da hakkin yi masa ibada shi kadai, wannan ibadar ta hada da bin umarninsa, da nisantar haninsa, da Salla, da Zakka , da Azumi, da hajji, da son abin da yake so, da kin abin da yake ki, da tsayawa kan iyakarsa. Amma ba zai yiwu a bauta wa wanda ake jahilta ba, don haka ne ya kasance wani nauyi na wajibi a kan kowane mai hankali ya san shi. Sai dai saninsa yana da hanyoyinsa da shari’a ta karfafa wacce take ita ce hanyar dogaro da hankali wurin tunani domin sanin mahalicci madaukaki. Don haka ne ma ba a yarda da bin hanyar ji kawai, ba tare da sanya hankali ba a mahallin imani da Allah, da sanin zatinsa, da siffofinsa. Bai halatta ba a dogara da gado ko fatawa a kan imani da samuwar Allah ko kadaita shi , wajibi ne a akida a yi imani da hakan a zuciya tare da gasgatawa da hakan bisa dalili na hankali, wannan kuwa ba ya dogara bisa fatawar malami. Da wani malami zai ce da kai: Ka yi sallar Jumma’a da Azahar tare wajibi ne, wato Juma’a ba ta isarwa sai ka hada da Azahar, wannan Malami kuma da shi kake koyi, a nan sai ka yi biyayya gareshi domin fatawa ta hukuncin shari’a furu’a ce da take kama da aikin likita ne a Asibiti da kake koma wa wanda ya fi kwarewa domin magani ko tiyata. Amma a Akida da wani malami zai ce: Ya gano Allah biyu ne, ko ya gano shi ya halicce halittu, ko ya halatta bauta wa wani gunki!, a nan sai a sanya hankali da Allah ya hore mana cewa ba yadda za a yi karfi biyu su hadu a matsayin ubangiji domin wannan yana nufin rushewa da wargajewa, da rasa halitta baki daya, ko kuturin ita ce ya zama ubangijin da za a bautawa. Domin samuwar karfi maras iyaka guda biyu yana nufin sun samu iyaka ke nan, wato duk inda dayan ya tuke, to a nan ne dayar zai fara, wannan kuwa yana nuna rashin kamalarsu, don haka ke nan a cikinsu babu wanda yake shi ne Ubangiji, don haka sai mu nemi ubangijinmu. An tambayi Imam Ali (a.s) game da Kadaita Allah (s.w.t) da Adalci, sai ya ce: "Kadaita Allah shi ne kada ka sanya shi a saken zuci, Adalci kuwa kada ka tuhume shi" . Rashin sanin Allah ya sanya jahiltarsa, jahiltarsa kuwa ta sanya jahiltar kawuka, sai ta sanya rashin sanin kawuka , rashin sanin kawuka kuwa ya kai ga rashin girmama juna. Wannan ne ya sanya marasa sanin Allah ba zaka samu wani daga cikinsu yana girmama ra’ayin dan’uwansa ba har a siyasar duniya, wannan lamarin ya haifar da gaba mai tsananin gaske a yankunanmu. Kuma ya tumbatsa har cikin lamurran addini, sai ga shi an dauki lamarin addini cikin jahilci ana jifan juna da kafirci, ana kafirta juna alhalin babu wani dalili na shari’a da zai hana ma’abota mazhabobi kasancewa tare, da fahimtar juna. Rashin sanin Allah ya sanya ana iya yi wa mutane fashin tunani wanda ya fi fashin kaya da rayuka muni da hadari, har al’umma ta koma jayayya kan abin da bai kamata ya kai ga sabani ba. An jefa rikici cikin al’ummu game da lamurran siyasar duniya da rikin kungiyanci da jam’iyyanci, saboda jahiltar kawuka. Har ma cikin Addini kamar sabani a rikicin â€کyan kabalu da â€کyan sadalu da aka yi a kasashenmu, da rikicin shin Annabi ya san gaibi ko bai sani ba? Sau da yawa da zaka tambayi masu rikicin mene ne ma’anar gaibi da ka samu maganganu masu karo da juna, amma ana iya kashe juna a kan irin wadannan. Nisantar tunani ingantacce mai kyau ya kai ga yin fada a kan Bushanci da Sadamanci, har da kashe juna a lokacin Yakin Gabas Ta Tsakiya Na Biyu. Haka nan a wannan lokaci wasu makiya wannan al'ummar suke tayar da rikice-rikicen da aka dade ana hura masa wuta domin tarwatsa wannan al'ummar kamar rikicin Shi'a da Sunna. Bambancin fahimta ba matasla ba ne matukar Allah daya, manzo daya, Littafi daya, kasancewar wannan mabiyin Ahlul-baiti (a.s) ne, wancan kuma mabiyin hanafiyya ne, ko shafi’iyya, ko malikiyya, ko kuma wancan Sufi ne ko Arifi, bai kamata ya cutar ko ya jawo rigima da fitina ba. Ba ma tsakanin musulmi ba, har ma tsakaninsu da wasunsu bai kamata ba a samu sabani da rigima!. Sani shi ne yin ilimi, shi kuwa yin ilimi shi ne yake samar da kamalar hankali domin yakan zama fitila ne ga hankali, ita kuwa kamalar hankali tana cikin sanin Allah ne, kuma Allah yana saka wa mutane da ladan aiki gwargwadon saninsu da shi ne. Idan mun duba zamu ga misalin Annabi Nuhu (a.s) duk da ya dade yana shan wahala, an ce tun yana shekara arba’in yake kira ga Allah (s.w.t) kuma ya rayu kusan shekara 2500 amma bai kai darajar Annabi Muhammad ba, domin ya fi shi sanin Allah (s.w.t), shi kuwa Allah yana sakawa gwargwadon saninsa ne ga masu aiki na gari a cikin bayinsa. Da wannan ne zamu ga cewa bauta ke nan tana bukatar sani kafin ta kasance karbabbiya cikakkiya, a kan haka ne zamu ga misali a wannan kissa mai kayatarwa. Wata rana wani Mala’ika ya yi mamakin karancin ladan wani mutum mai yawan bauta ga Allah, sai yake cewa da Ubangiji: Ya Ubangiji yaya wannan bawa yana bauta mai yawa amma ladansa kadan ne? Sai Allah ya ce da shi: Ina sakawa gwargawdon sanina ne amma tafi wajansa ka gani, sai Mala’ika ya tafi wajansa, da safiya ta yi suna maganar ciyawa da take fitowa lokacin damuna ta mutu lokacin rani sai mai bauta ya ce da Mala’ika: Ai da Ubangijinka yana da jaki da ciyawan nan ba ta lalace a banza ba, da yana da jaki da mun kiwata shi. Haka nan Mala’ika ya ga karancin hankalin wanann bawan shi ya jawo masa karancin lada: don haka ne wanda ya fi sanin Allah ibadarsa daya ta fi ta jahili sau saba'in. Ga kissar kamar yadda take a ruwaya: Wata rana wani Mala’ika yana yawo sai ya wuce wani tsibiri da wani mai bauta yake rayuwa a ciki sai ya tambayi Allah ya nuna masa ladan wannan mai bauta, sai Allah ya nuna masa, sai Mala’ika ya karanta ladansa, sai Allah ya ce da shi: Ka zama tare da shi, sai Mala’ika ya zo masa a surar mutum, sai ya tambayi Mala’ika: Wane ne kai? Sai Mala’ika ya ce: Ni wani mai bautar Allah ne na ji labarinka ne da ibadarka sai na zo don in kasance tare da kai, sai ya zauna da mai bauta wuni daya, da safiya sai Mala’ika ya ce: Wannan wuri yana da shuke-shuke bai dace da komai ba sai ibada. Sai mai bauta ya ce: Ai wurin yana da aibi. Mala’ika ya ce: Mene ne aibin? Sai ya ce: Ubangijinmu ba shi da dabbobi, da Ubangijinmu yana da jaki da mun kiwata shi a nan, ga ciyawa nan tana lalacewa a banza. Sai Mala’ika ya ce: Shin Ubangijinka ba shi da jaki ne? Sai ya ce: Ai da yana da jaki da wannan ciyawa ba ta lalace ba! Sai Allah ya yi wa Mala’ika wahayi da cewa ni ina saka masa daidai gwargwadon hankalinsa ne . A bisa dabi’ar dan Adam da ya gada daga nau'in halittarsa, kuma ta samu karfafuwa a tafarkin annabawa (a.s) ilimi shi ne yake bayar da kima da daukaka, kuma saba wa dabi’ar haka tana nufin rushewar dan Adam. Wannan al’amari na saba wa dabi’ar dan Adam shi ne ya sanya rushewar tsarin gurguzu, shi tsari ne da ya shahara da yakar dabi’ar dan Adam musamman a abin da ya shafi mallaka. A tunanin Gurguzu aiki shi ne yake bayar da kima ko mallaka, saboda haka a misali mai kaya idan ya kai zinarensa wajan makeri don ya yi masa dan kunne da shi, idan ya kera ba zai ba shi dankunne ba sai ya ba shi kudin zinarinsa, domin aikin kira da ya yi shi ne yake bayar da kima da mallaka, wannan kuwa al’amari ne da ya saba wa dabi’ar dan Adam, a sakamakon haka ne ba su je ko’ina ba suka rushe. Yanzu ta kai ga cewa hatta Akidun da suka dasa na rashin samuwar mahallicci sun rushe, har a ranar 1 ga Disamba 2002 Gidan Rediyo/Telebijin na IRNA ya shelanta cewa: A yanzu kashi sittin cikin dari na mutanen Rasha sun yarda akwai Allah, al’amarin da su Lenin suke ganin haka a matsayin rashin hankali ne sakamakon maye na banju da Duniyar dan Adam ta sha ta fada cikin dimuwa. Kwatanta aikin Lebura da Purincipal, haka nan kwatanta aikin Manajan banki da na Masinja, da na Saje da Janar, me ya sa albashin aikin na sama na rana daya ya fi albashin aikin dayan da tazara mai yawa, wannan ba domin komai ba ne sai bambancin sani da tunani da na sama yake amfani da shi fiye da na kasa. Sanin Allah madaukaki ya dogara da samar da yanyi mai inganci da zai bayar da damar hakan ta yadda masu koyarwa da ilmantarwa zasu kasance annabawa ko wasiyyansu, sai dai ba a bari annabawa (a.s) sun kafa Daular Allah ba, hatta lokacin Manzo (s.a.w) ya sha matsala da munafukai, amma duk da haka annabawa (a.s) sun kafa ci gaban da ba kamarsa a Duniya. A dukkan hukumomin musulmi hatta da wadanda suke aiwatar da shari'ar musulunci a hukumance har yanzu babu wanda ya kai kashi hamsin cikin dari sakamakon yanayi. Ya zo a ruwayoyi cewa; Imam Mahadi (a.s) ne kawai zai samu ikon kafa hukumar Allah mai aiki da cikakkiyar shari’a , shi kuwa zai samu wannan ne saboda Allah zai ba shi damar hukunci da hakikanin yadda abu yake ne ba da zahiri kawai ba . Imam Ja'afar Sadik (a.s) yana cewa: Idan imam Mahadi (a.s) ya shugabanci mutane zai yi hukunci tsakanin mutane da hukuncin Dawud (a.s), ba ya bukatar sheda ko rantsuwa, a kowane hukunci Allah yana yi masa ilhamar hakikanin abin da ya wakana, kuma da dogaro da wannan ilimin nasa ne zai yi hukunci . Sai ga wasu wadanda suke kiran kansu musulmi ba sa son a san Allah, suna kokarin hana sanin Allah ta kowane hali, da kokarin toshe duk wani kokarin fahimtar addininsa da hakkokinsa a kanmu. Sai ga Addini ana wasa da shi kowa ya fiye bangaranci da mazhabanci sai ga rarraba, sai ga jifan juna da kafirci. Da mutane sun san Allah hakikanin sani kuma suka bi umarninsa, da sun ci arzikinsa mai yalwa, da duniya ta yalwata gunsu. Rashin saninsa ya sabbaba rashin sanin yadda za a bauta masa da gode masa, domin su malam tsutsa sun shiga cikin goro sun hana shi sakat, wannan ya sanya aka kasa aiwatar da abin da Allah ya zo da shi ta hannun Annabawansa. Don haka ne ya bar wasiyyan Annabi su ci gaba da shiryar da mutane bayansa (a.s), amma duka an kashe su ne daya bayan daya . Ba kawai sanin Allah (s.w.t) mahalicci ba har ma furu’a kamar siyasa, da hukunce-hukunce, da zamantakewar dan Adam, da dokoki, da tsarin musulunci, duk an jahilci da yawansu a kasashen musulmi. Amma matsalar yammacin Duniya ta bambanta da ta sauran kasashen musulmi ta wani banbare, domin su wannan hasken da yake hannunmu da ba a aiki da shi su ba su da shi. Kamar yadda Turai suka yi mummunar fahimta da jahiltar musulunci, haka su kansu musulmi suka yi masa mummunar fahimta suka jahilce shi. Da zaka ambaci kalmar shari’a a cikin musulmi sai mutane su yi tunanin fille kai, da jefewa, da gutsure hannaye da kafafu. Da zaka tambayi wanda ba musulmi ba a sabanin da makiyan kasarmu na ciki ko na waje suka haifar kan batun shari’a a Arewa me yake nufi da ba shari’a? Zai ce: Ba gutsure hannu, ba fille kai. Haka nan amsar da musulmi zai iya ba ka ke nan idan yana maganar shari’a. Wannan yana nuna wajabcin tashi don kawar da jahilci da miyagun hannayensa masu guba da suke tafiyar da tunanin mutane game da musulunci har aka kai ga fadawa cikin irin wannan dimuwa. Musulunci yana da fadi ba babi daya ba ne, ya kamata a nemi saninsa daga masanansa na ainihi. Babbar matsala a cikin al’ummarmu ita ce kauracewa Ilimin sanin Allah da shagaltuwa da furu’a kawai, wannan kuwa ya tauye tunanin mutane game da saninsa (s.w.t). Ash’arawa sukan takaita a kan Littafin Kawa’idi ne da mafi yawan mutane ba sa ma fahimtarsa, wanda ya yi zurfi shi ne wanda ya kai ga Sharhi Ummul Barahin, da kyar zaka sami wanda ya wuce hakan sai daidaiku. Ba a ma san Al’makalat da Al’ibana na Al’ash’ari shi kansa mai mazhabar Ash’ariyya ba, yawanci ba a san wanda ake bi a mazhaba ko Akida ba. Sai sanin Allah ya yi nesa da mutane suka yi nisa da shi, haka ma al’amarin tarihin musulunci da ba a karanta shi wai akwai rigima a ciki da ba a so a sani, wai idan aka yi fada da uwa da uba shin ka so ka sani? Sai dai wannan tunanin kuskure ne babba, domin rikicin iyaye bai shafi makomar Lahira ba, kuma a ciki babu batun sanin waye Manzo (s.a.w) ya bari tsakaninsu wanda bin sa ya zama hujja a kanka. Amma na tarihin musulunci ya shafe ka, domin zai gaya maka makomarka ne, da abin da Manzo (s.a.w) ya bar maka a matsayin tsiranka a duniya da lahira. Kuma ana bukatar ma’aunin waye maganarsa ta fi zama hujja don ka yi aiki da ita, wannan duk ya shafi makomarka ne. Haka aka haramta wa al’ummarmu sanin Akidu da ilimomi har ka san mene ne gasakiya ka bi, mene ne ba daidai ba ka bari, sai aka dogara da koyi a cikin jiga-jigan addini. Koda yake wasu malamai sun tafi a kan cewa wanda ya fadaka, ya yarda har a zuciyarsa, ya yi imani da samuwar Allah da kadaita shi a bisa sahihiyar Akidar musulunci, duk da tun yana yaro ya yi koyi da malamai ne ko iyaye, to irin wannan imanin yana isarwa gare shi. Sannan sanin tsarin Allah wani abu ne da ya hau kan dukkan musulmi, tsarin musulunci ya doru kan sanin Allah mai tsari da mulki mai sanya dokoki da ba wa kowane mutum hakkinsa da ya hada mace, namiji, mai kudi, talaka, mai mulki, da wanda ake mulka, da yaro, da babba. Ba zalunci, ba zalunta, ba take hakkin juna, babu yakar dabi’ar halittar dan Adam, ba bambanci ko fifiko sai da takawa. Musulunci tsari ne cikakke bai zo da tsari irin na demokradiyya ba, ya zo ne da AsalatusShura. Wato yin shawara tsakanin musulmi kan wani al’amari, a sani yin shawara a nan da sharadin bai fita daga asasin dokokin Musulunci ba. Malamai sun yi nuni da hanyoyi masu yawa domin tabbatar da samuwar Allah madaukaki wanda zamu iya yin ishara da wasu daga ciki da suka hada da samuwar halitta da kuwa samuwar tsarin da take a kansa, wadanda suke nuni da samuwar mai halitta su da zamu yi nuni da wasu daga ciki. Imam Sadik (a.s) ya yi nuni da wannan lamarin mai muhimmanci yayin da Disani (shi wani mutum ne da bai yi imani da samuwar Ubangiji ba) ya tambaye shi a wata ruwaya mai tsayi da zamu kawo ta kamar haka: Daga Ali bn Ibrahim, daga muhamad dan Ishak al'khafifi, ko daga babansa, daga Muhammad dan Ishak ya ce: Abdullahi Disani ya tambayi Hisham dan Hakam sai ya ce masa: Shin kana da Ubangiji? Sai ya ce: haka ne. Ya ce: Shin shi mai iko ne? Ya ce: E, mai iko ne. Sai ya ce: Shin zai iya shiga da duniya dukanta cikin kwai ba tare da ya kirmama kwai ba, ko ya kankanta duniya? Sai Hisham ya ce: Jira ni. Sai ya ce: Zan jira ka shekara. Sannan sai Hisham ya fita daga wurinsa zuwa ga Abu Abdullahi Imam Ja'afar Sadik (a.s), sai ya nemi izinin shigowa, sai ya yi masa izini. Sai ya ce masa: Ya dan manzon Allah (s.a.w) Abdullahi Disani ya zo mini da wata mas'ala ta babu wani madogara gareta sai dai Allah da kuma kai, sai imam Sadik (a.s) ya ce masa: Me ya tambaye ka. Sai ya ce: Kaza da kaza, sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce: Ya Hisham! Mariskanka nawa ne? sai ya ce: Biyar. Sai ya ce: Wanne ne ya fi karanta? Sai ya ce: Mai gani. Sai ya ce masa: Yaya girman mai ganin? Sai ya ce: Kamar girman wake ko kasa da hakan. Sai ya ce masa: Ya kai Hisham! Duba gabanka da samanka kuma ka gaya mini me kake gani? Sai ya ce: Ina ganin sama da kasa, da gidaje, da binaye, da filaye da duwatsu, da koramu. Sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce: To wannan da ya sanya kamar gwargwadon kwayar wake ko kasa da ita ta ga haka, yana da ikon ya sanya duniya dukkaninta a cikin kwai ba tare da ya kankanta duniya ba, ko ya girmama kwai. Sai Hisham ya fadi yana sumbuntar hannayensa, da kansa, da kafafunsa. Ya ce: ya ishe ni ya dan manzon Allah (s.a.w), sannan ya koma gidansa. Washe gari Disani ya zo masa, sai ya ce masa na zo maka mai musulunta ne, ba na zo maka mai neman jawabi ba. Sai Disani ya fita daga wajensa har sai da ya zo kofar gidan imam Sadik (a.s) sannan ya nemi izini, shi kuwa imam (a.s) ya yi masa izini. Yayin da ya zauna a gabansa sai ya ce: Ya kai Ja'afar dan Muhammad (a.s) nuna mini Abin bautata -Ubangijina-? Sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce masa: Yaya sunanka? Sai ya fita bai gaya masa sunansa ba. sai abokansa suka ce masa, me ya sanya ka ba ka gaya masa sunanka ba? Sai ya ce: Da na ce masa Abdullah, to da ya ce: Wane ne wannan da kake bawansa. Sai suka ce masa: Koma ka ce ya gaya maka Ubangijinka amma kada ya tambaye ka sunanka? Sai ya koma ya ce: Ya Ja'afar dan Muhammad (a.s) nuna mini ubangijina amma kada ka tambaye ni sunan? Sai Imam Sadik (a.s) ya ce masa: Zauna. Sai ga wani yaronsa karami a hannunsa akwai kwai yana wasa da shi, sai Abu Abdullahi (a.s) ya ce masa: Ba ni kwan nan ya kai yaro, sai ya mika masa. Sai Abu Abdullahi ya ce masa: "Wannan wata katanga ce rufaffiya tana da fata mai kauri, kuma a karshita akwai wata fata siririya, kuma akwai wani ruwan zinare da na azurfa karkashin siririyar fatar, sannan wannan ruwan zinariyar ba ya cakuda da ruwan azurfar, kuma na azurfa ba ya cakuda da na zinare, suna yadda suke, babu wani mai gyara da ya fito daga ciki balle ya bayar da labarin daidaitar su, kuma wani mai barna bai shiga cikin su ba, balle ya bayar da labarin lalacewarsu, ba a sani ba shin an halitta ne don namiji ko mace, yana tsagewa ga misalin Dawisu, shin kana ganin akwai mai shirya hakan? Ya ce: Sai ya sunkuyar da kai tsawon lokaci, sannan sai ya ce: Na shaida babu ubangiji sai Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya gareshi, kuma na shaida cewa Muhammad bawansa ne kuma manzonsa, kuma kai ne imami hujja daga Allah a kan halittarsa, kuma ni na tuba daga abin da nake a kansa . A wata ruwayar akwai karin cewa: Sai Disani ya ce: Mu ba ma imani sai da abin da muka riska da idonmu, ko ji, ko shaka, ko dandano, ko tabawa. Sai imam Sadik (a.s) ya ce masa: Ka ambaci mariskai, su kuwa ba sa amfanar komai sai da hankali . Sannan akwai dalilin da yake nuni da cewa dole ne a samu wani wanda dukkan halitta ta tuke zuwa gareshi, wanda babu wani wanda yake samansa, wanda daga gareshi ne dukkan samammu suka gangaro, wannan kuwa shi ne Allah mahalicci. Don haka babu ma'ana wani ya tambayi cewa waye ya yi ubangiji, domin shi ne karshen wanda samuwa take tukewa zuwa gareshi. A irin wannan ne masu hikima suka kawo wani labari na wani dalibi mai hikima da ya ba wa wani masanin kwayoyin halitta amsa game da samuwar Allah madaukaki kamar haka: Wannan masanin kwayar halittar ya tambayi dalibin ilimin addini game da cewa: Waye ya yi Ubangiji? -sai wannan dalibin ya ga babu ma'ana wani ya tambayi waye wanda samuwar komai daga gareshi take, don haka- Sai ya amsa masa da cewa wani Ubangiji ne da yake sama da shi. Sai ya ce masa: Waye ya yi wannan Ubangijin? Sai ya ce masa: Wani Ubangijin ne da yake sama da shi kuma. Sai ya sake tambayarsa ta uku, sai ya ba shi wannan amsar. Sai ya ce masa: Dole ne ke nan a samu wani Ubangiji da babu wani samansa, wanda yake sama komai. Sai ya ce masa wannan shi ne Allah ke nan. Ta haka ne ya iya isar masa da muradinsa, domin kowace rayi tana furuci a cikin zuciyarta da cewa akwai wani wanda shi ne ya yi ta, kuma ya yi komai, kuma shi babu wani rashi da ya gabace shi, domin shi samamme ne tun fil azal . Don haka da za a sawwala wani ubangiji a tunani bayan Allah madaukaki, da samuwarsa ta kasance daga Allah take, sai ya kasance ke nan bawa ne daga cikin bayin Allah (s.w.t), sai ya kasance ke nan ba ubangijin ba ne, wannan shi ne abin da wannan dalibi ya lurasshe da wancan masanin ilimin halitta. Sannan akwai wasu hanyoyi uku da malamai suka tafi a kan cewa su ne hanyoyin da ake sanin Allah madaukaki kamar haka: 1- Hanyar Dalilin Fidirar Halitta: Wannan hanyar tana tare da dukkan wani abin halitta, domin nau'in halitta ce da Allah (s.w.t) ya dora kowane mai rayi a kanta. Wannan hanyar tana nuna wa dukkan wani mai hankali cewa idan ya duba kansa zai san ba shi ya samar da kansa ba, kuma ba wani mai kama da shi ne ya samar da shi ba. Don haka ne ba ya ganin babansa ko shugabansa a matsayin wanda ya samar da shi, kamar yadda ba ya ganin wani abin halitta kamarsa ne ya samar da shi. Da wannan ne zai kai ga natijar cewa akwai wani wanda ya samar da shi wanda yake babu wani wanda ya yi shi. Da irin wannan ne ake yawaita misali kan cewa idan mutum ya ga kashin rakumi sai ya samu yakini cewa da akwai rakumi, idan ya ga sawun tafiya, sai ya tabbatar da cewa akwai wanda ya yi tafiya, kuma idan ya ga wani aiki sai ya samu yakini cewa akwai wanda ya yi wannan aikin. Daga cikin muhimmancin wannan dalilin shi ne cewar kowane mai hankali zai iya amfana daga gareshi, don haka a nan babu bambanci tsakanin jahili da malami, ko tsakanin babba da karami, ko tsakanin adilin mutum da fasikin mutum. 2- Hanyar dalilin hankali: Wannan hanyar ita ce ta dalilin hankali wacce take iya kai mu ga sakamakon cewa akwai Allah madaukaki ta hanyar kafa hujja da kwakkwaran dalili na hankali da aka fi sani da Burhan. Masu ilimin akida suna amfani da ita domin kafa dalilin samuwar Allah, sai dai sukan bi ta sanin siffofinsa domin su kafa hujjar samuwarsa bayan sun dogara da dalilan addini da suka zo daga wahayi. Su kuwa masu ilimin Falsafa suna kafa hujja da wannan hanya kan samuwar Allah amma ta hanyar lizimtar samuwarsa. Don haka ne wannan hanya ta kebanta da ma'abota nazari da ilimi, masu karfin ikon tunani da kafa hujja ta hankali. 3- Sai dai akwai wata hanyar ta masana Allah (s.w.t) da aka fi sani da Arifai, su ne wadanda suke sanin Allah (s.w.t) ta hanyar tsarkake zukata daga dukkan wata dauda, da kuma yi mata ado da dukkan tsarki. Sai a fitar da dukkan wani sabo daga cikin tunani da aiki, sannan sai a siffantu da dukkan aikin kwarai a cikin tunani da aiki, idan zukata suka tsarkaka sai hasken Allah ya haskaka su da saninsa, sai su kasance kamar gilasai ne da haske yake haskakawa, bayan da can sun kasance kamar bango ne da koda kuwa rana ta haskaka shi amma yana kare shigar hasken cikinta. Haka nan dalilai suke a bisa matakai hawa-hawa, da akwai dalilin da yake ana bin sanin fararre domin sanin sababinsa, amma mafi daukakar ilimi shi ne a bi hanyar sanin sababi sannan sai a san fararrensa. Don haka ne ma aka tambayi imam Ali (a.s) game da sanin manzon rahama (s.a.w) aka ce masa: Shin kasan Allah ta hanyar Muhammad ne ko kuwa ka san Muhammad ta hanyar sanin Allah ne? Sai ya ce: Na san dai Muhammad ta hanyar sanin Allah ne. (Sharhin Risalatul Hukuk: s; 35). Domin sanin Allah hakikanin sani muna bukatar taimakon Allah da ludufinsa, sannan kuma ta namu bangaren sai mu yi motsi domin neman saninsa, Allah mai tausayi ya yi mana nasa ludufin da hankali da ya ba mu, da kuma shari'a da ya saukar, don haka sai ya rage ga bayinsa su tashi domin kusantar ludufin.
Domin sanin waye Allah Ubangiji madaukaki zan so kawo wadannan bayanai a takaice kamar haka:
Allah Madaukaki Kalmar “Allahâ€‌ suna ne madaukaki na mahallici wanda wasu suka tafi a kan cewa shi ne suna mafi girma. Allah yana da siffofi da ayyuka, wadannan siffofin nasa su ba irin na sauran samammu ba ne, domin shi siffofinsa azali ne wadanda suke tare da shi tun azal, amma sauran halittu siffofinsu suna bujuro musu ne. Sai dai tun farko yana da kyau mu sani cewa sanin Allah madaukaki yana bukatar ayyana hanyar saninsa ga mai rubutu, domin wani yakan yi bayanin Sanin Ubangiji madaukaki ta hanyar Falsafa, wani kuma ta hanyar Irfani, da makamantansu. Amma mu a nan muna son yin wani gajeren bayani game da Allah madaukaki ta hanyar hankali da shara’a ne. Da farko dai mu sani cewa Allah ya yi mana baiwar da babu wani mai rayuwar a doron kasa da ya same ta. Ya yi mana falalar da baiwar karfin tunani da kyautar hankali, don haka ne ma ya umarce mu da mu yi tunani a kan halittarsa mu kuma yi duba a cikin a alamomin ayyukansa, mu yi la’akari a cikin hikimarsa da kuma kyautata tafiyar da al’amuranSa a ayoyinsa a cikin duniya baki daya da kuma a kawukanmu, Allah Madaukaki yana cewa: “Zamu nuna musu ayoyinmu a sasannin duniya da kuma a kawukansu har sai ya bayyana gare su cewa hakika Shi gaskiya neâ€‌. Surar Fussilat: 53. Kuma Ya zargi masu bin iyayensu -a akida- da fadinsa: “Suka ce mu dai kawai muna bin abin da muka samu iyayenmu a kai ne, ashe koda ma iyayen nasu sun kasance ba su san komai baâ€‌. (Surar Bakara: 170). Kamar kuma yadda ya zargi wadanda suke bin zato kawai da shaci-fadi cikin duhu da cewa: “Ba komai suke bi ba sai zatoâ€‌. Surar An’am: 116. Wannan ni’imar ta hankali ita ce ta wajabta mana yin bincike domin sanin Allah madaukaki, ta yadda muna iya cewa dokokin hankali suna tilasta mana hakan. Don haka ne abin da ya zo a cikin Kur’ani na kwadaitarwa a bisa tuntuntuni da bin ilimi da sani ya zo ne don karfafa wannan `yanci na dabi’ar halitta ta hankali. Kuma babban kuskure ne ga wani mutum ya ya yi wa kansa saki-na-dafe a kan al’amuran Akida, ko kuma ya dogara da wasu mutane, ya wajaba ne a kansa ya karfafa kan yin bincike ya yi tunani ya yi nazari ya yi bincike a kan asasin shika-shikan Akidarsa, ya san ubangijinsa . Don haka a kanmu akwai nauyin wajabcin bincike da neman sani a kan shika-shikan akida, bai halatta ba a yi koyi da wani a cikinsu ba, kuma na farko shi ne ubangiji madaukaki. Wannan wajabcin saninsa bai samo asali daga nassosin addini ba duk da ya inganta a karfafe shi da su bayan hankali ya tabbatar da shi. Sau da yawa marubuta sukan kawo sunayen Allah da siffofinsa kamar haka: Allah madaukaki daya ne makadaici, babu wani abu kamarsa, magabaci ne, bai gushe ba kuma ba ya gushewa. Shi ne na farko kuma Shi ne na karshe, Masani, Mai hikima, Adali, Rayayye, Mai iko, Mawadaci, Mai ji, Mai gani. Ba a siffanta Shi da abin da ake siffanta halittu da shi, shi ba jiki ba ne, kuma ba sura ba ne, ba Shi da nauyi ko sako-sako, ba Shi da motsi ko sandarewa, ba Shi da guri ba Shi da zamani, kuma ba a nuni zuwa gare Shi, kamar yadda babu tamka gare Shi, sannan ba a iya riskarsa da wasu mariskai. Duk wanda ya ce ana kamanta shi da halittarsa, kamar ya suranta fuska gare Shi da hannu da idaniya, ko cewar Yana saukowa zuwa saman duniya, ko yana bayyana ga â€کyan aljanna kamar wata ko kuma makamantan wannan, to yana matsayin jahilci hakikanin mahaliccin da ya tsarkaka daga nakasa, kai dukkan abin da muka bambance shi da tunanin kwakwalwarmu da sake-saken zukatanmu a mafi zurfin ma’anarsa, to shi abin halitta ne kamarmu, mai komawa ne zuwa gare mu, kamar yadda ya zo daga Imam Bakir (a.s). Mafi girman siffar da take fara zuwa a jerin sunayensa ita ce kadaitawa, domin ya wajaba a kadaita Allah ta kowace fuska kamar yadda ya wajaba a kadaita shi a zatinSa, da samuwarsa, da siffofinsa da cewa siffofinsa su ne ainihin zatinsa kamar yadda bayani zai zo game da hakan. Haka nan wajibi ne a kadaita Shi a bauta, bai halatta a bauta wa waninsa ba ta kowace fuska, kamar yadda bai halatta ba a hada Shi da wani abu a nau’o’in ibada, wajiba ce ko wadda ba wajiba ba, a salla ne ko kuma waninta na daga ibadoji. Duk wanda ya yi shirka ya hada wani da Shi a ibada to Shi Mushiriki ne, kamar wanda yake riya a ibadarsa yake neman kusanci zuwa ga wanin Allah (s.w.t), hukuncinsa da wanda yake bauta wa gumaka daya ne babu bambanci a tsakaninsu. Wasu mutanen sun so su kore musulunci daga dukkan wanda yake ziyarar kaburbura, da tawassuli da waliyyan Allah, da da’awar cewa shirka ne. sai dai lamarin ba haka yake ba, domin ziyartar kaburbura da gudanar da bukukuwa ba sa daga cikin nau’in neman kusanci da wanin Allah a ibada. Wadannan ba komai ba ne sai wani nau’i na aiki domin samun kusanci zuwa ga Allah (s.w.t) ta hanyar kyawawan ayyuka, kamar neman kusanci gare shi ta hanyar gaishe da maras lafiya, da kai jana’iza, da ziyartar â€کyan’uwa, da taimakon talaka. Don zuwa gaishe da maras lafiya Shi a kan kansa kyakkyawan aiki ne wanda mutum kan samu kusanci da Allah ta hanyarsa, ba neman kusanci da maras lafiyar ba ne da zai sanya aikinsa ya zama bauta ga wanin Allah (s.w.t) ko kuma shirka a bautarSa, haka nan sauran ayyukan ibada. Dukkan wadannan ayyukan ba komai ake nufi da su ba sai rayar da al’amuran Allah da waliyyansa, da sabunta tunawa da su, da kuma girmama alamomin Addinin Allah a tare da su “Wannan, duk wanda ya girmama alamomin addinin Allah to lalle wannan yana daga cikin ayyukan takawar zukataâ€‌. Surar Hajj: 32. Daya daga cikin mafi girman lamari a bahasin sanin Allah madaukaki shi ne na siffofinsa tsarakaka; da farko dai ana kasa wadannan siffofi zuwa siffofi tabbatattu na kamala da (jamal) kamar ilimi, da iko, da wadata, da nufi, da rayuwa, wadanda suke su ne ainihin zatinSa. Wasu sun dauka wadannan siffofin su daban ne, kuma kari ne kan samuwar zatin Allah, ta yadda su ma suna da tasu samuwar ta daban. Sai dai mu muna cewa wadannan siffofi ba kari suke ba a kan zatinSa, kuma ba komai ne samuwarsu ba sai samuwar zatin Allah, kudurarsa ta fuskacin rayuwarsa ita ce ainihin rayuwarsa, rayuwarsa ita ce kudurarsa, Shi mai kudura ne ta fuskacin kasancewarsa rayayye, kuma rayayye ta fuskacin kasancewarsa mai kudura, babu tagwayantaka (biyuntaka) a siffofinSa da samuwarsa, haka nan yake a sauran siffofinsa na kamala. Amma wadannan siffofin sun sassaba a ma’anoni, ba a hakikanin samuwarsu ba, domin da sun kasance sun sassaba a samuwarsu, da an sami kididdigar Ubangiji, kuma da ba a sami kadaitaka ta hakika ga Ubangiji ba, wannan kuwa ya saba wa Akidar Tauhidi. Sannan akwai wasu siffofi masu nuna aikin ubangiji kamar halittawa, arzutawa, gabatuwa, da kuma samarwa. Wadannan, duk suna komawa ne a bisa hakika zuwa ga siffa guda ta hakika, wato siffar nan ta tsayuwa da al’amuran halittarsa, ita siffa ce guda daya wacce ake fahimtar irin wadannan siffofi daga gareta gwargwadon tasirori da ayyukansa ga bayinsa. Amma siffofin da ake kira salbiyya wato korarru; da aka fi saninsu da siffofin Jalal, dukkansu suna komawa ne zuwa kore abu daya, wato kore nakasa daga ubangiji ko duk wata tawaya kamar jiki, sura, fuska, motsi, da rashin motsi, nauyi, da rashin nauyi, da sauransu. Shugabanmu Amirul Muminin (a.s) ya yi nuni ga hakikanin siffofin Allah madaukaki yana mai cewa: Cikar tsarkake wa gareshi kuwa shi ne kore siffofi (n halitta) gare Shi , saboda shaidawar dukkan abin siffantawa cewa ba shi ne siffar ba, da kuma shaidawar kowace siffa cewar ba ita ce abin siffantawar ba, don haka duk wanda ya siffanta Allah (da irin wadancan siffofi) to ya gwama Shi, wanda ya gwama Shi kuwa ya tagwaita Shi, wanda ya tagwaita Shi kuwa ya sanya Shi sassa-sassa, wanda ya sanya shi sassa-sassa kuwa to lalle ya jahilce Shi, wanda kuwa ya jahilce shi zai yi nuni gareshi, duk wanda kuwa ya nuna shi ya iyakance shi, wanda kuwa ya iyakance shi to ya kididdiga shi, wanda ya ce: A cikin me yake? To ya tattaro shi a wani wuri, wanda ya ce: A kan me yake? To ya sanya shi ba ya wani wurin . Daya daga cikin siffar Allah da aka yi ta ja-inja a kanta ita ce Adalcin Allah, amma mu a takaice a nan zamu ce: Duk wani nau’in zalunci ya koru ga Allah, domin dukkan hanyoyi hudu da za a iya yin zalunci sun koru daga gareshi kamar haka: 1- Ya kasance ya jahilci al’amarin bai san cewa zalunci ba ne. 2- Ko kuma ya kasance ya san da shi amma an tilas ta shi a kan aikata shi, ya kuma kasa barin aikata shi. 3- Ko kuma ya kasance yana sane da shi ba a kuma tilasta shi ya aikata shi ba, bai kuma kasa barin sa ba, sai dai yana bukatar aikatawa. 4- Ko kuma ya kasance yana sane da shi, ba a kuma tilasta shi ba, ba ya kuma bukata gareshi, sai al’amarin ya kasance ya yi zalunci ne kawai don sha’awa da wasa. Dukkan wadannan siffofi sun koru ga Allah domin suna tabbatar da nakasa gare shi, alhali Shi tsantsar kamala ne, saboda haka wajibi ne mu hukunta cewa shi tsarkakke ne daga zalunci da kuma aikata abin da yake mummuna. Sannan haka nan Allah ba ya tilasta wa bayi aikin da ba zasu iya yin sa ba, kamar yadda ba ya kallafa wa bayinsa aiki sai bayan ya tabbatar musu da hujja a kansu, kuma ba ya kallafa musu sai abin da zasu iya aikatawa, da abin da zasu iya masa, da abin da suka sani, domin yana daga zalunci kallafa aiki ga ajizi, da jahili maras takaitawa wajan neman sani. Amma shi kuwa Jahili mai takaitawa wajan neman sanin hukunce-hukunce, shi wannan abin tambaya ne wajan Allah, kuma abin yi wa azaba ne a kan takaitawarsa da sakacinsa, domin ya wajaba a kan kowane mutum ya nemi sanin abin da yake bukata gareshi a sanin hukunce-hukuncen shari’a. Babban nauyin da yake kan baligi shi ne wajabcin ya san Allah madaukaki, bai halatta ba ya bi wani a kan haka ba koda kuwa babansa ne, dole ya yarda Allah daya ne, ta yadda da babansa ko malaminsa zai ce Allah sabanin haka ne, to ba zai bi ba. Ludufin Allah (s.w.t) ya hukunta samar da ni'imarsa ga dan Adam domin ya kusantar da shi zuwa ga saninsa da bautarsa, sai ya aiko masa annabawa (a.s) suna masu bin juna, kuma bai bar wata al'umma ba sai da ya aiko mata da sako, sannan sai ya bi annabawan da wasiyyai a kowane zamani, domin dai kada dan Adam ya rasa shiriyar sanin Allah, kuma kada kofar sanin bautarsa ta toshe masa. Domin dan Adam ya samu kamala yana da tambayoyi masu yawa da suke yawo a tunaninsa wadanda Allah ya ba shi amsarsu kamar haka: Daga ina muke kuma meye asalinmu? A yanzu inda muke me ye abin yi? Daga nan kuma ina zamu, kuma yaya yake?. Sai kur'ani madaukaki a amsa masa wannan tambayoyi, Allah (s.w.t) bai taba barin duniya babu hujjarsa ba, koda a zahiri kamar lokacin imam Ali (a.s) da sauran wasiyyan manzon Allah (s.a.w), ko kuma boyaye kamar imam Mahadi (a.s). Annabawa (a.s) sun zo ne domin motsa hankali ya yi tunani da imani da samuwar Allah, da kadaita shi a ibada, da zatinsa, da siffofinsa, da ayyukansa, da yarda da annabawan da ya aiko da riko da sakonnin da suka zo da su. Annabawa ba su ce a bi su ba tare da dalili ba, wannan lamari ne ya sanya Allah yake ba su mu’ujiza da take dalili ce a kan cewa sakon da suke dauke da shi daga gareshi ne, wannan kuwa zai samar da nutsuwa a zukata har mutane su karbi sakon. Amma hukuncin rassan addini an sanya su bisa biyayya da maslaha ne wacce ba kasafai aka santa ba sai dai a bi umarnin Allah a ciki, don haka ne Allah yake sanya wa kowane Annabi (a.s) wasiyyi da zai yi wa mutane bayanin abin da sakon ya kunsa bayan wafatinsa, kamar yadda annabin rahama (s.a.w) ya yi wasiyya ga wannan al’umma da imam Ali (a.s) da goma sha daya daga zuriyarsa a bayansa. Matsalolin da wasiyyan Annabi suka fuskanta na kawar da su daga fagen jagorancin al’umma da kisa sun sanya Allah (s.w.t) ya boye na karshensu imam Mahadi (a.s) domin kada a kashe shi, domin ya zo a karshen duniya ya cika ta da adalci bayan an cika ta da zalunci. Shi kuwa imam Mahadi (a.s) kafin ya boyu ya yi wasiyya da riko da malamai na gari, ya ayyana mana siffofinsu, don haka duk wanda ya kai matakin Ijtihadi da daukaka cikin al’umma a ilimin sanin hukuncin shari'a, ya cika siffofi na gari kamar takawa, da adalci, da kamala, da tsentseni, kuma ya kasance dan halal ne, to ya zama dole ne a bi shi a umarninsa. Sai dai idan ya rasa daya daga irin wadannan sharudda, kamar ya dulmuya cikin tara duniya da rashin tsentseni, ko ya kasance ba shi ne ya fi kowa ilimin shari’a ba, ko ya kasance yana zalunci ko wasu ayyukan da suke haram, ko son ransa ya fito karara a cikin ayyukansa da zantukansa, to daga nan babu sauran kuma biyayya ga umarninsa. Don haka ne dole a yi hatta da mayaudaran mutane masu da’awar su ne malamai ko mataimaka Imam Mahadi (a.s) alhalin suna jahiltar waye shi da tafarkinsa. Haka nan ruwayoyi masu yawa sun yi nuni da cewa duk wanda ya yi da’awar lokacin bayyanar Imam Mahadi (a.s) ko ya yi da’awar yana ganin sa, ko yana karbo sako daga gunsa, da sauran kalamai na barna irin wadannan, to shi makaryaci ne a guje shi. Sanin Imamin lokacinmu yana daga cikin hakkokin Allah a kanmu, domin duk wanda ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba ya yi mutuwar Jahiliyya , haka nan ya zo a Kur’ani mai girma cewa a Ranar Lahira kowace al’umma za a kira ta tare da imaminta . Wadannan imamai Allah bai bar mu mun zabe su da kanmu ba sai da ya shelanta su ta hannun manzonsa (s.a.w) wanda ya sanar da mu cewa su goma sha biyu ne: Na farkonsu Ali (a.s) na karshensu Mahadi (a.s) wanda yake shi ne imamin wannan zamanin. Sanin Imami ya hada da bin sa, da koyi da abin da ya bari na wasiyyarsa, da bin koyarwarsa, da biyayya ga malaman da suke shiryarwa zuwa ga abin da ya bari wadanda suka cika sharuddansa, da kin makiyansa . Kuma hatta da salla da azumi da duk wata ibada idan babu mika wuya ga Imami Allah ba ya karba; Manzon tsira (s.a.w) ya ce: “Wanda ya mutu bai san Imaminsa ba ya yi mutuwar Jahiliyyaâ€‌ . Domin zai tashi a Ranar Lahira kamar wanda ya yi zamani kafin a aiko Annabi ba shi da komai da Allah (s.w.t) ya karba daga gare shi. Littafin Allah ludufi ne nasa ga bayinsa domin su samu wani kundin tsarin rayuwar duniya da lahira, sannan an sanya lada mai yawa da karanta shi da aiki da shi. Kuma yana dauke da dukkan abin da muke bukata a maslahar rayuwar duniya da lahira. Karanta littafin Allah da saninsa suna daga cikin hakkokinsa a kanmu, amma sanin littafin ba yana nufin mu san sunansa ba kawai domin hakan ko kadan ba shi da wata ma’ana, amma abin nufi shi ne ya zama mun siffantu da Kur’anin a aikace. Idan ba haka ba a ranar lahira akwai kara da zai shigar a kotun Allah wacce ba a zalunci a nan kuma ba a iya boye gaskiya. Kuma a bi shi kamar yadda Manzo da wasiyyansa goma sha biyu daga Alayensa suka fassara domin su ne ya ce: “Idan an yi riko da su ba za a taba bata ba har abadaâ€‌. Kuma: “Da Su da Littafin Allah ba sa rabuwa har sai sun riske shi a tafkiâ€‌ . Haka nan al’amarin yake a matsayin al’umma, dole ne Littafin Allah ya yi iko da rayuwarmu a matsayin al’umma, in ba haka ba, ba mu sauke nauyin da yake kanmu ba. Kuma idan ba mu siffantu da shi ba, to yana da hakkin karar cewa musulmi sun bijire masa. Sannan masu tafsirin Kur'ani su sani cewa kowace kalma a cikinsa tana da ma'ana, kuma manzon Allah (s.a.w) ya yi bayanin ta, don haka yana da hadari su fassara Kur'ani da ma'anar kalmomin lugga kawai. Ya hau kan dukkan mafassarin Kur'ani ya duba abin da manzon rahama (s.a.w) ya ayyana game da manufar kowace aya ba kawai ma'anarta ta lugga ba. Manzon Allah (s.a.w) ya bayyana wadanda ake nufi da Ahlul-baiti da cewa su ne Ali, Zahara, Hasan, Husain , ya bayyana wadanda ake nufi da al'umma a fadin Allah madaukaki kun kasance mafificiyar al'umma da aka fitar wa mutane da ma'anar wasiyyoyinsa . Kuma kowace aya sai da manzon Allah (s.a.w) ya nuna wadanda ake nufi da ita domin kada al'ummarsa ta halaka da fassara shi da ra'ayinta. Don haka ne ya zo cewa; Masu fassara kur'ani da ra'ayinsu, su tanadi mazauninsu a wuta. Da farko dole mu nemi yaya Manzon Allah (s.a.w) da wasiyyansa suka fassara Kur’ani a ruwayoyi, idan muka rasa sannan sai mu koma zuwa ga karina da siyakin aya, da ayoyin da suke tare da ita, idan ba mu samu ba, sannan sai mu koma zuwa ga shawahid daga wasu ayoyin Kur’ani da suka yi magana kan wannan lamarin, idan ba mu samu ba, sannan sai mu kai ga neman littattafan lugga. Amma sai aka samu wasu â€کyan kayi-nayi suka hau fassara Kur’ani da ra’ayinsu, da sun ga aya sai su dauka â€کyar luggar da suka sani ta wadatar da su, sai suka fassara Kur’ani da ra’ayinsu suka bata, suka batar da wasu. Da zamu bayar da misali da mun kawo daruruwansu, sai dai wannan dan karamin littafin ba zai dauki wadannan dogayen bayanai ba. Amma misali daya shi ne a ayar Mubahala Manzon Allah (s.a.w) ya fassara matansa a aikace, zai ya zo da â€کyarsa sayyida Zahara (a.s), kuma ya zo da Ali (a.s) a matsayin kansa, ya zo da Hasan da Husain (a.s) a matsayinsa â€کya’yasa, wanda a lugga duk babu wani abu da ya yi daidai da wannan. Da luga ce zata yi mana fassarar da sai ya zo da kansa kawai, ya zo da matansa, ya zo da â€کyarsa sayyida Zahara (a.s). Haka nan a fassarar Ahlul-baiti (a.s) ya fassara su da Ali da Fadima, da Hasan da Husain, wasu ruwayoyin suka yi nuni da tara daga zuriyar Husain (a.s). Da mun bi lugga da sai mu sanya matansa da duk wani wanda yake daga zuriyarsa da sun kasance miliyoyin ko biliyoyi, domin sharifai suna da yawa. Amma sai Manzon Allah (s.a.w) ya fassara cewa ga wadanda ake nufi da su. Kuma su ne wajibi a bi har alkiyama ta tashi su goma sha biyu ne, hada da â€کyarsa ta goma sha ukunsu. Muna ganin yadda hatta da wasu wadanda suka yi zamani da Manzon Allah (s.a.w) idan suka yi tafsiri ba kasafai suke da cewa ba, balle wadanda suka yi nesa da zamaninsa. A nan ne zamu ga duk da girma irin na Zaid dan Arkam amma sai ya cakuda ma’anar Ahlul-baiti (a.s) da kuma wadanda aka hana cin zakka da sadakar mutane wato sharifai, don haka ne ma shi sai ya fassara su da alayen Ali (a.s) da na Ja'afar, da na Akil, da na Abbas, alhalin Manzon rahama (s.a.w) a ruwayoyin Sunna da Shi’a duka shi ba haka ya fassara ba. An karbo daga sahabban imamai (a.s) game da hanin kiyasi da fassara kur'ani da ra'ayi kamar haka : Abuhanifa yana cewa: Na zo wurin wani mai aski sai ya ce da ni: Ka kusanto da bangaren daman kanka, ka fuskanci alkibla, ka ambaci sunan Allah. Ya ce: Sai na san wadannan mas'aloli uku daga wurinsa. Sai na tambaye shi: Ko kai bawa ne ko da? Sai ya ce da ni: Shi bawa ne. Na ce: Bawan waye kai. Sai ya ce: Bawan Ja'afar dan Muhammad (a.s) Sai na ce: Yana nan ko ba ya nan. Sai ya ce: Yana nan. Don haka sai na tafi kofarsa na nemi izini amma sai bai yi mini izini ba. Sai ga mutanen Kufa sun zo, sai aka yi musu izinin shiga, sai na shiga tare da su. Sai na ce wa Imam Ja'afar Sadik (a.s), ya kai dan Manzon Allah (s.a.w), da ka aika zuwa ga mutane Kufa da su daina zagin sahabban Manzon Allah (s.a.w), domin ni bar mutane kusan sama da dubu goma a can suna zagin su. Sai Imam Sadik (a.s) ya ce: Babu mai jin maganata. Sai na ce masa: Waye ba zai ji maganarka ba, alhalin kai ne dan Manzon Allah (s.a.w)?! Sai ya ce da ni: Kai ne farkon wanda ba ya jin maganata, ka shiga gidana babu izinina, ka yi magana a nan ba tare da ra'ayina ba, kuma labari ya zo mini cewa kai kana yin kiyasi. Sai na ce masa: Haka ne. Sai ya ce: Kaiconka ya Nu'uman (Abuhanifa)! farkon wanda ya yi kiyasi shi ne shedan yayin da Allah ya umrace shi da yin sujada ga Adam (a.s), sai ya ki. Ya ce: Ka halicce shi da wuta ni kuwa ka yi ni da tabo. Ya kai Nu'uman (Abuhanifa)! Kisa ya fi muni ko yin zina? Sai na ce: Kisa. Sai ya ce: Me ya sa Allah ya sanya shedu biyu ga kisa, amma a zina sai guda hudu! Shin zaka iya kiyasata wannan. Sai ya ce: A'a. Sai ya sake ce mini: Wanne ne ya fi muni fitsari ko mani? Sai ya ce: Fitsari. Sai ya ce: To me ya sa Allah ya sanya alwala ga bawani, amma ya sanya wanka ga mini. Shin zaka iya kiyasta wannan! Sai na ce: A'a. Me ya fi girma salla ko azumi? Sai na ce: Salla. Sai ya ce: Me ya sanya ya wajbta wa mai haila rama azumi ban da salla. Shin zaka iya kiyasta wannan! Sai na ce: A'a. Ya ce mini: Waye ya fi rauni, namiji ko mace? Sai na ce masa: mace. Sai ya ce: Me ya sanya a gado kason namiji yake biyu, na mace kuwa daya. Shin zaka iya kiyasta wannan! Sai na ce: A'a. Sai ya ce mini: Me ya sanya Allah ya hukumta yanke hannun barawo saboda ya saci dirhamomi, amma idan wani ya yanke hannun wani, sai diyya ta kasance dirhami dubu biyar. Shin zaka iya kiyasta wannan! Sai na ce: A'a. Labarin ya zo mini cewa kana fassara wata ayar littafin Allah "Sannan da sannu za a tambaye ku a wannan ranar kan ni'ima" (Takasur: 8). Kana cewa shi ne abinci mai dadi, da ruwan sanyi, a rana mai tsanin zafi. Sai ya ce: Da wani mutum ya kira ka ya ba ka abinci mai dadi, kuma ya shayar da kai ruwan sanyi, sannan sai ya yi maka gori, da me zaka danganta shi. Sai ya na ce: Rowa. Sai ya ce: To ashe ke nan shin kana ganin Allah madaukaki zai yi rowa. Sai Abuhanifa ya ce: To me ake nufi da wannan ni'ima? Sai Imam Sadik (a.s) ya ce: Soyayya garemu Ahlul-baiti (a.s) . A fili yake cewa hadafin Imam Sadik (a.s) shi ne ya nuna wa Abuhanifa cewa ba yadda za a yi kiyasi ya zama daya daga hanyoyin samun hukuncin shari'a!. Sabanin yadda Dumairi bashaif'e yake neman ya nuna a cikin "Hayatul Haiwan". A fadada bayani a nan: Ra'ayin kiyasi bai bar fikihu ba hatta da ibadar akida sai da ya shiga, misali ra'ayi yana ganin sanya wani abu gaban mai salla don kada wani ya gindaya ya wuce ta gabansa tsakaninsa da Allah ubangijinsa, wannan lamari ne da imam Kazim yana yaro ya yi wa Abuhanifa raddinsa, ya sanar da shi cewa; Ubangijinsa ba jiki ba ne, don haka ba ya ganin wani abu zai iya shiga tsakaninsa da shi. Addinin Musulunci ludufi ne na Allah ga bayinsa da ya aiko da shi domin tsara rayuwar dan Adam, kuma wannan addini yana da hakkin kare shi a kan kowane musulmi da bakinsa da basirar da Allah ya ba shi, da wajabcin saninsa da taimakawa wajan yada shi a aikace , da kokarin hada kan mabiyansa, da raddi cikin hikima ga masu gaba da shi, da girmama fahimtar ma’abotansa don ba ka sani ba ta yiwu shi mai waccan fahimtar da ta saba da taka shi ne yake a kan daidai. Kada mutumin da bai fahimta ba ko bai sani ba ya tsoma baki da jayayya a kan mas’alolin Addini wannan na malamai ne. Shari’a ta hana jayayya da jahilci, don haka kada malami ya sa mutane cikin rikicin Addini, haka ma maras Ilimi kada ya sanya kansa cikin rikicin Addini, bayyana ra’ayi kan mas’aloli abu ne na malamai, kamar dai lamarin likitanci ne da babu mai shiga sai likita. Imam Ali Zainul-abidin asSajjad (a.s) ya yi nuni da cewar idan muka san hakkin Allah madaukaki, muka yi biyayya gareshi babu shirka, to ya yi mana alkawarin gyara mana lamurran duniya da lahira, sannan ya kiyaye mana abin da muke so a cikinsu. Wane alheri da ni'ima ne ya fi wannan a cikin samuwar dan Adam gaba daya. Game da Kaddara kuwa: Yana daga cikin maganarsa yayin da mai tambaya ya tambaye shi: Shin tafiyar mu zuwa Sham da hukuncin Allah ne da kuma kaddarawarsa? Bayan magana mai tsayi yana mai cewa: Kaiconka! Kai kana tsammanin hukunci na tilas, da kuma kaddara ta lallai! Da kuma ya kasance haka ne da lada da azaba sun zama wasa, kuma da alkawari da narko sun saraya. Allah madaukaki ya umarci bayinsa bisa zabi, ya hana su bisa tsoratarwa, kuma ya kallafa musu mai sauki, bai kallafa musu mai tsanani ba, ya ba su mai yawa a kan dan kadan da suka aikata, kuma ba a saba masa don rinjayarsa, ba a bi shi don tilastawa ba, bai kuma aiko annabawa don wasa ba, bai saukar da littafi don raha ba, bai kuma halicci sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu don barna ba. “Wannan shi ne tsammanin wadanda suka kafirta, to azabar wuta ta tabbata a kan wadanda suka kafirtaâ€‌. Hafiz Muhammad Sa'id hfazah@yahoo.com www.hikima.org Saturday, May 14, 2010
|