Samun TsiraA nan fa mutum ya sani wani alkawari ne zai dauka tsakaninsa da Ubangijinsa wanda ba shi da wani abu da yake boye masa, wannan ubangijin duk da mun san ba shi da ‘yan sanda ko masu gadi da muke gani a fili, amma mu sani yana da wadanda suka fi wannan, domin akwai mala’iku da suna ganin komai namu, su ba sa gajiya, ba sa bacci, ba sa gafala, ko sha’afa, kuma ba sa mantuwa, kuma suna rubuta dukkan abin da muke yi. Idan mai daukar alkawari ya san girman Ubangijinsa to zai san girman wannan alkawari da ya dauka, idan kuma ya san cewa wannan alkawarin da ya dauka ba fa amfanin Allah ba ne, ko wani daban, dukkaninsa amfaninsa ne, to a nan ma zai sake sanin kimar wannan alkawarin. Lura: Lura ita ce abu na biyu kuma tana nufin cewa wannan alkawarin da muka dauka da wayewar safiya, zamu yi kokarin ganin mun kiyaye mun aikata shi tun safe har zuwa dare. Sai mu kiyaye mu ga ba mu yi wani abu na sabo ba tun safiya har dare, idan muka fara yin rada ko gibar wani muka tuna sai mu daina, idan hannunmu zai taba haram sai mu tuna sai mu fasa, idan idanuwansu zasu kalli haram, ko kunnenmu zai ji haram, ko kafarmu zata je wurin haram, duk idan muka tuna da wannan alkawarin da sharadin sai mu janye. Haka nan idan muka ga zamu ki aikata mai kyau, kamar muka ki tausaya wa wani muka hana shi sadaka, ko muka ji nauyin tashi mu yi salla, ko muka ki taimaka wa wani, ko muka ki fadin gaskiya, sai mu tuna cewa mun yi alkawarin zamu yi kyakkyawa saboda Allah, don haka sai mu yi kyakkyawan. Hisabi: Hisabi shi ne abu na uku, kuma yana nufin cewa da dare ya yi lokacin da zamu kwanta sai mu yi kawukanmu hisabi, mu duba mu ga cewa shin mun aikata wani mummuna a yau kuwa, idan muka ga mun yi wani mummuna sai mu nemi gafarar Allah madaukaki da cewa ya yafe mana. Kamar idan mun saba wa Allah da yin karya, sai mu nemi gafara kuma mu yi niyyar ba zamu sake ba, amma idan mun cuci wani ne da wani abu nasa to sai mu nemi gafara kuma mu mayar masa da kayansa kamar mun karbi kudinsa kuma muka hana shi, sai mu mayar masa da shi. Sannan mu sake dubawa idan mun ki yin wani kyakkyawa, kamar wani ya zo neman taimako wurinmu kuma muna da yadda zamu taimaka masa amma ba mu yi, to sai mu yi alkawarin zamu taimaka masa, kuma ba zamu sake yin wannan halin na rashin yin alheri ba. Haka nan idan muka ga ba mu yi salla Idan zai yiwu bayan neman gafara sai mu yi sallar dare raka’a takwas, mu yi shafa’i da wutiri raka’a uku, domin neman gafara da kuma neman dacewa nan gaba, wannan ya zo a ruwaya cewa; sallar dare kaffarar zunuban rana ce. Idan kuwa ba zamu iya yin salla ba, to sai mu nefi gafarar Allah da bakinmu ta hanyar neman gafararsa, da kuma a zuciyarmu ta hanyar jin cewa ba zamu sake ba, kuma wannan ya kasance da gaske saboda sabawa a nan tana nufin wasa da alkawarin da muka daukar wa Allah madaukaki. A game da yi wa kai hisabi ne Imam Ali (a.s) ya ce: “Wanda ya yi wa ransa hisabi to ya rabauta, wanda kuwa ya gafala daga shi -ran nasa- to ya yi hasara, wanda ya ji tsoro ya aminta, wanda ya yi lura ya samu basira, wanda ya samu basira ya fadaka, wanda kuwa ya fadaka to ya samu ilimiâ€[1]. Bayan dukkan bayanan da suka gabata, zamu so mu kawo wasu misalai guda biyu daga Kur’ani mai daraja Don haka sai bala’o’i suka yawaita, zubar da mutunci ya yi kamari, sai fyade, da sata, da kisa, ga rashin kimanta juna, da rashin ganin mutuncin juna, sai ya zamanto mutum ya koma kurar mutum, idan mutum ya ga mutum tamkar tunkiya ta hangi kura saboda tsoron cutuwa, ko kuma rashin shiri da juna kamar kura da damisa.
|