Hakkin Rai



Hakkin Rai

A game da hakkin rayuka imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: “Amma hakkin ranka a kanka shi ne ka sanya ta cikin biyayya ga Allah, sai ka ba wa harshenka hakkinsa, ka ba wa jinka hakkinsa, ka ba wa ganinka hakkinsa, ka ba wa hannunka hakkinsa, ka ba wa kafarka hakkinta, ka ba wa cikinka hakkinsa, sai ka ba farjinka hakkinsa, kuma sannan sai ka nemi taimakon Allah (s.w.t) a kan hakan”[1].

Yayin da Imam Sajjad (a.s) ya tashi bayanin hakkin rayi sai ya koma zuwa ga mariskai, wannan lamarin yana nuna mana muhimmancin mariskai a fili kuwa, ‘yan mariskai dai su wasu tagogi ne da mutum zai iya bi ta cikinsu domin ya riski kaiwa zuwa ga rayinsa. Sannan ita kuma rai tana amfani da su ne wurin cimma burinta da bukatunta, kasancewar rai tana da sha’awa da fushi sai takan yi amfani da wadannan kofofi da tagogi domin cimma burinta.

Idan ta yi kwadayin wani abu na haram sai ta yi amfani da mariskai gwargwadon yadda take bukatar cimma burinta, sai ta ci abinci ta sha wani abin sha yayin da ta bukaci hakan, wannan abin ci da shan yana iya yiwuwa na haram ne da aka hana shi a cikin shari’a. Sannan tana yin kallo abin da aka  haramta mata kallonsa, ko ta ji abin da aka hana ta sauraronsa, ko ta  taba abin da aka hana ta tabawa, ko ta yi tafiya zuwa wurin da aka haramta zuwa, ko ta biya sha’warta ta hanyar zina.

Haka nan tana yin fushi sai ta kauce wa hanyar gaskiya, sai ta yi girman kai, ko ta ki fadin gaskiya, ko ta ki yin hakuri da sauran halaye makamancin wannan, wannan kuwa duk tana amfani da wadannan mariskai ne domin nuni da wadannan abubuwan. Da haka ne sai mutum ya siffantu da munanan halaye, sai su kasance dabi’arsa, sai ya yi kasa cikin faduwar daraja, ransa ta yi muni kwarai da gaske, sai ya kasance mai nisantar ubangijinsa, da zarar taimakon Allah da ludufinsa sun bar shi sai ya kasance mai saukin ja gun shedan.

Shedan yana jan wasu matane da igiyoyi, wasu da sarkokin karfe, wasu da hannayensa, amma irin wannan mutum da ya kai karshe wurin lalacewa yana iya kira ne kawai sai ya amsa ya zo masa da gaggawa. Don haka ne tun farko Imam Zainul-abidin (a.s) ya nemi mutum ya kiyaye wadanna kofofin da shedan zai iya shigowa zuwa zukata ta cikinsu, sannan sai ya nemi taimakon Allah (s.w.t) a kan hakan”.

Idan muka yi haka ne zamu kare rayukanmu daga cutuwa daga wutar lahira, da kuma rabauta a nan duniya, ranmu tana da hakki a kanmu kan hakan. Kuma fadin ubangiji da nuni cewa Mu kiyaye kawukanmu da iyalanmu daga wuta yana gaskata hakan, don haka haramun ne mu cutar da kanmu cutarwa ta lahira kamar mu yi sabo da su wanda zai jawo musu azaba, haka ma cutarwa ta duniya kamar kin cin abinci da shan ruwa, da kin shiga inuwa, da shan guba. Don haka ne ma wasu malamai suka haramta shan taba idan tana cutarwa, wasu kuwa suka ce: Ba ta zama haramun da farko amma in ta kai matsayin in mutum ya sha tana cutar da shi to a nan ta zama masa haramun[2].

Mafi munin zaluntar kai shi ne hana kai sanin Allah da manzanninsa da Ilimin aikace-aikace da suka shafi sanin duniya da lahirar dan Adam, idan mutum bai san Allah ba sai ya kamanta shi da halittu sai ya bauta wa Allah (s.w.t) yana mai shirka da shi. Masu hikima suna cewa: Sanin kawukanmu ya dogara kan amsar wadannan tambayoyi ne kamar haka: Ni wane ne? Daga ina nake? A ina nake yanzu? Kuma Ina za ni?.

Rayinmu tana bukatar irin nata abincin da abin shan kamar yadda jiki yake bukata, mafi dadi a ciki shi ne sanin Allah da ganawa da shi ta hanyar addu’o’i da sauran ibadoji, amma babban asasi shi ne saninsa da farko, domin in ba saninsa yaya za a gana da shi?[3] Rashin sani ko wane iri ne yana daidai da sanya rai a kurkuku.

Haka nan ba ya halatta ga mutum ya halakar da ransa ta kowace hanya, kamar ta hanyar ganganci da mota ko babur da kowane irin abin hawa da zai iya kaiwa ga cutar da jiki, ko kin shan magani ga maras lafiya.

Mafi muhimmancin bahasi game da rai shi ne na sanin ta, duk wanda ya san ransa to ya san ubangijinsa[4], wannan kuwa ya zo a hadisai masu yawa. Kuma jahiltar rai shi ne mafi munin abu ga mutum, domin duk wanda ya jahilci kansa to ya ya jahilci Ubangijinsa, duk kuwa wanda ya jahilci Ubangijinsa to ya kai karshen tabewa. Muhimmancin Sanin rai ba wani abu ba ne boyayye, domin da saninta ne za a san me ye ya hau kanta, kuma mene ne hakkinta, mene ne zai gyaranta da lalacewarta.



1 2 3 4 5 6 next