Farisancin Shi'anciTo duk bayan wannan al’amari mene ne abin da ya kawo alakanta Shi’anci da yahudanci ko kuma cewa a cikinsa akwai fikirorin Farisanci ko kuma alamomin Farisanci, sannan kuma idan akwai wasu fikirorin da idan mun kaddara cewa wanda suka muslunta sun kawo su kuma sun bi su, ai ba ta wuce wani ra’ayi ne da ya yi riko da shi da wani dalili ko kuma ya zamanto bidi’a kamar yadda muka kawo, kuma ka san ra’ayoyin malamai a kan hakan. wannan irin wuce gona da iri ne kan musulunci da kuma daukar alhakinsu yana daga kaucewar tunani, kuma da sannu zaka san abin da Shi'a suka tafi a kansa daga Littafi da Sunna, kuma koda wasu sun dauka sun samu ne daga Farisawa sakamakon karancin saninsu ko kuma mummunan nufi da suke da shi, kuma Allah ne magani kan komai. c- Wannan irin da’awar da ake yi ta Farisancin Shi’anci zamu tabatar maka da cewa al’amarin akasin haka ne, kai idan ma ta inganta to ba laifi idan dai bafarise ya kasance musulmi kuma mu muna ganin a addinin musulunci babu kabilanci, kuma takenmu shi ne: "Ya ku wadanda suka yi imani mu mun halitta ku daga namiji da mace, kuma muka sanya ku jama’u da kabilu domin ku san juna, hakika mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku gareshi" Hujurat: 13. Don haka ne ma wannan mataki ya yi daidai da na musulunci kuma idan muna magana ne ta kabilanci to da sai mu kebanta da luggarmu kawai kuma babu wata lugga da zata kasance mun yarda dai ta, tare da cewa hankali yana kiran ne zuwa ga girmama mutane da kabilu, kuma maganar Imam Sadik (a.s) ta kayatar matuka a nan yayin da yake cewa: Ba ya daga ta’assubanci (bangaranci da kabilanci) ka so mutanenka, sai dai ta’asubanci shi ne ka sanya ashararan mutanenka sun fi zababbun wasu mutane da ba su ba. Musulunci ba ya bambancewa tsakanin wani jinsi da wani, kuma ba ya la’akari da musulmi don yana da wani yare kawai, amma idan dai mai magana yana fakewa ne da yare karkashin wata manufa daban da yake da ita, to lallai wannan mutumin da yake ganin mutane kamar gafalallu shi ne hakikanin gafalalle, kuma nan gaba kadan zamu ga hadafin irin wadannan mutane da suke da wannan raye-rayen. Akwai kuma wani abu daban cikin tasawwurin Farisancin Shi’anci kuma shi ne cewa dukkan ko galibin Shi'a Farisawa ne, kuma Farisancinsu ya yi galaba a kansu har sai da ya mamaye Shi’anci kuma wannan yakan kai ga karo da shari’ar musulunci saboda sabawarsa da wadannan akidoiji na musulunci kamar yadda suka raya, kuma wasunsu ma sun shelanta hakan a fili kamar yadda nan gaba zamu kawo hakan cikin wasu ra’ayoyi a kan wannan, kuma da sannu zaka ga wannan ra’ayi cewa barna ne ba daidai ba ne, kuma dukkan wanda ya san tarihin musulmi da akidunsu ya san ba haka ba ne, kuma ya san hakan batacce ne saboda wasu dalilai kamar haka: a- Akidun Shi'a sun cika littattafai masu yawa wadanda su ne madogara, kuma kowa yana iya dauka ya karanta, kuma suna hannun marubuta da masu bincike a dukkan laburorin duniya, kuma madogarar akidun Shi'a su ne; littafin Kur'ani da Sunna da ijma’I da hankali kamar yadda ya gabata, kuma mun yi nuni zuwa ga littattafai da suka yi bayanin hakan dalla-dalla hada da littafin â€کawa’ilul makalat’ na sheikh Mufid, da aka’id na Saduk da durar da gurar na sayyid murtadha, da a’ayusshi’a na sayyid muhsin al’Amin, da kuma littattafan hadisai da kuma littattafai hudu wadanda Shi'a suka dogara kansu a jumlace wadanda suka hada da "Man’la’ yahdhuruhul fakih", na Saduk, da "Usulul Kafi" na Muhammad kulaini, da "Tahzib" da "Istibsar", na sheikh Dusi, tare da cewa ba duk abin da yake cikinsu ba ne ya inganta gunmu. b- Sannan kuma farisawa wani yanki ne kankani na yawan Shi'awan da suke wannan duniya tamu, wadanda suka hada da Larabawa, da Indiyawa, da Turkawa, da Afganawa, da Kurdawa, da Mutanen kasar Sin, da mutanen Tibet, da sauransu, don haka ke nan Farisawa wani bangare ne kawai. c- Sannan kuma inda aka kafa dashen irin Shi’anci duk yana yankin Larabawa ne na jazirar Larabawa, kuma a â€کyan shi’ar farko babu wani daga wanda ba balarabe ba sai mutum daya wanda yake shi ne salmanul muhammadi kamar yadda Annabi (s.a.w) ya ambace shi wanda shi bafarise ne. kuma an ambace shi a cikin dabaka ta farko na Shi'a wadanda suke daga kabilu daban daban, kuma idan ka bi dabaka ta biyu da ta uku na Shi'a duk zaka samu mafi galibinsu duk Larabawa ne, kuma ba na son tsawaitawa a wannan wurin don akwai shi a littattafan tarihi kuma zamu kawo maka abin da zai tabbatar maka da hakan a karshen wannan fasali. Tare da dukkan abin da muka riga muka kawo na bayani to mene ne, kuma ta ina ne Shi’anci ya kasance Farisanci har ma ake daukar wannan kamar wani abu da aka riga aka tabbatar da shi. Don haka ne domin mu kawo duk abin da ya shafi wannan maudu’i to ya zama dole ne mu shiga yin bayanai dalla-dalla da kawo ra’ayoyi masu yawa da kuma dalilan da aka kawo don kafa dalili da nuna ingancin wadancan ra’ayoyi. Kuma ina tabbatar maka idan ka karanta abubuwan da suka zo raunin abin da suka kawo zai bayyana gareka, kuma zaka yi mamakin yadda irin wadannan marubuta duk da suna da ilimi da ba a rena shi amma suka gamsu da abin da suka kawo balle kuma har suna kawo shi domin su gamsar da wanin su saboda son rai da kuma bangaranci, Allah ya tsare mu daga wannan. Wannan kuwa yana daga gamsuwa da wata akidar danne gaskiya da rashin ba wa haske damar haskaka masa akidarsa da abin da ya riga ya dogara a kai har ya ga irin abin da yake haifarwa sakamakon mummunar makauniyar biyayya, sai ya ci karo da dalili mai inganci sai ya watsar da shi, ba ya duba ma’aunan shari’a ya yi riko da su. Daga Littafin Sheikh Wa'ili Na HAKIKANIN SHI'ANCI Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id
|