Shi'a Ba Su Ne Rawafidawa BaA fili yake cewa wannan jumla ta nuna cewa Rawafidhawa ba su ne Shi'a ba, domin samun bambanci a jerin da ya kawo. Irin wannan ne muke samu a cikin maganganun waninsa na daga ma’abota sani da ilimin addinai da mazhabobi suka cirato da wannan ma’anar ta lugga, kuma dukkan mutane da suka nisanci jagoransu ana kiran su da rawafidhawa. Kuma siffanta sahabban Zaid da wannan suna yana daga siffantasu ne da ma'anar kalmar don haka ne aka kira su da wannan suna bisa dogaro da bairn sa da suka yi yayin da suka nemi ya barranta da shaikhaini kamar yadda aka fada. 1- Wadannan da suka nemi barranta daga Zaid da sun kasance Shi'a ne to da babu makawa suna kwadayin taimaka wa Zaid ne, da kuma neman Shi'a ga shiga sahun dauki-ba-dadi da azzalumai ne domin matsayinsu yana da alaka da matsayi irin na Zaid, kuma idan ya samu rushewa to wannan yana nfin su ma sun rusu ke nan, musamman da yake cewa: Abokan gabarsu Umayyawa suna kashe duk wani wanda yake karkata ga alayen Abu Dalib hatta da a kan zato da tuhuma, to mene ne ya kai su ga kirkiro wannan bala’ai da zai kai karewar rundunar Zaid da kuma hasararsa a fagen yaki, da mutuwarsa shahidi a hannun Umayyawa. Don haka ba makawa wadannan mutane ba Shi'a ba, sai dai su wata jama’a ce da aka yi dasisarsu domin su kawo bala'i da fitina don gamawa da Zaidu da kawo masa rushewa a fagen daga. 2- Idan mun kaddara cewa akwai jama’a guda daya kebantacciya da take da ra’ayin kin shaihaini to mene ne ma’anar sanya wannan suna ga dukkan mai son Ahlu-baiti (a.s) har al’amarin ya kasance an sallama shi a matsayin suna ne da ya kebanta da su kawai, don haka ne sai ga Shafi'i yana fada a cikin baitinsa da ya shahara yana cewa: Ya kai mahayin muhassabi a filin mina Ka shelanta ga na zaune da na tsaye a taronta A sahur idan mahajjata suka kwarara zuwa mina Kwarara kamar tunkudar kogin Furat mai kwarara Shin kun sani cewa Shi’anci ne mazhabata Ni ina fadin haka kuma ban warware ba Idan son alayen Muhammad shi ne rawafidanci
|