Mauludin Annabi (s.a.w)Da SunanSa Madaukaki Amincin Allah ya tabbata ga Annabi da Alayensa
Mauludi: Wani buki ko taro ne domin tunawa da ni'imomin Allah da ya yi mana da rahamarsa da ya saukar zuwa ga bayinsa domin shiriya ga dukkan talikai. Magana kan mauludin Annabi (s.a.w) da sakon da ya zo da shi abu ne mai matukar kima da daraja wanda babu wani abu da ya kai shi muhimmanci, domin kuwa yana nufin bayanin sakon da dan Adam ba zai samu tsira ba sai ya yi riko da shi. Don haka zamu yi gajeren bayani kan Mauludin Annabi (s.a.w), da Sakonsa, da kuma Musulmi. Sai dai an samu wasu masu karancin diraya da fahimtar littafin Allah da sunnar Annabinsa (s.a.w) suna ganin munin Mauludi. Jama’a ce da ta tasirantu da koyarwar Banu Umayya masu gaba da Manzon Allah (s.a.w) masu jin haushin shelanta "Ash'hadu anna Muhammdar Rasulul-Lah" da ake yi a kan mimbari sau biyar a kowace rana. (Sharhu Nahajul Balaga: Ibn Abil Hadid; 1/113, 1263. Muwaffakiyyat: Ibn Bukair. Murujuz Zahab: 1/341. Tahzibut Tahzib: 7/319). Don haka babu mamaki idan an samu masu riko da koyarwar da ta samu daga wannan asalin suna kiyayya da tunawa da mafi girman ni'ima da Allah ya yi wa bayinsa ta samar da Manzon Allah (s.a.w). Dalilan da ake kafawa domin nuni ga halascin mauludin Annabi (a.s) duk ishara ce kawai ga mai hankali, domin wanda yake musun Mauludi shi ne ake neman ya kawo dalili kan haramcinsa: A cikin Kur'ani Mai daraja da Sunnar Ma’aiki an yi nuni da abubuwan da suke haramu, kuma Mauludi ba ya daga cikinsu. Don haka mai son karyata Mauludi shi ne mai bukatar ya kawo dalili kan wannan haramcin, domin haramun a bayyane take kuma tana da iyaka, amma abubuwan da aka halatta suna da fadi kuma ba su da iyaka. Daga cikin dalilan akwai ayoyi kamar haka: "Ba mu kasance masu azabtar da mutane ba sai mun aiko wani Dan sako". Da yake nuni da cewa; Duk abin da babu wani haramncinsa da muka sani a shari'a to halal ne yin sa, sannan a hankalce akwai munin azabtarwa ba tare da bayani ba". Wadannan lamurran an san su da "Bara'a shar'iyya da akaliyya" a cikin ilimin Usulul Fikhi, da suke nuni da cewa; Duk abin da ba a san haramcin ba daga nassin shari'a kuma babu wani abu da yake nuni da shi, to halal ne. Wadannan abubuwan fararru sababbi suna da yawa matuka kamar; Mauludin Annabi, da Musabakar Kur'ani, da kafa Kungiyoyi domin ayyukan alheri, da wasannin motsa jiki.
|