Taimama
Yin Taimama:kafin taimama dole ne a tanadi kasa mai tsarki da za a yi taimama da ita kamar yaddaAllah (SWT) ya yi umarni, da yadda ya zo a hadisan manzonsa (SAW) Bayan nan sai a buga hannaye biyu gaba daya a kan wajen mai tsarki sau daya. Sa’annan shafar fuska daga saman goshi wato matsirar gashin kai zuwa saman karan hanci har tukewa zuwa karshensa da duk hannaye biyu a lokaci guda. Amma hannaye za a shafa fuska da su ne daga tudun farkon tafin hannu kusa da wuyan hannu har zuwa tukewar ‘yanyatsu kamar yadda aka nuna cikin hoto. sa’annan shafar hannun dama da na hagu daga wuyan hannu zuwa karshen ‘yan yatsu kamar yadda aka nuna a hoto. A kula sosai cewa shi hannun da yake shafa shi ne zai rika motsawa har zuwa karshen wanda ake shafa. Sa’annan a shafa hannun hagu da hannun dama kamar yadda muka siffanta kuma aka nuna a hoto na sama da kuma sharadin da muka ambata a shafar hannun dama.
|