Shi'a da Shi'anci



Shi'a da Shi'anci

Ahlul Baiti (A.S) da mabiyansu sun imani da cewar Manzo rahama ya yi wasiyya ga mutum goma sha biyu a bayansa wadanda su ne halifofinsa, haka ma Ahlussunna sun tafi a kan Manzo ya yi nuni da cewa: "Halifofinsa har kiyama ta tashi guda goma sha biyu ne dukkansu daga kuraishi" a wata ruwaya Bani Hashim. Littattafai masu yawa na Ahlussunna da Mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) sun kawo har sunayensu wanda ya fara daga Ali (A.S) zuwa Mahadi (A.S) kamar adadin Nakibai na Bani Isra'ila da kuma Hawariyawan Annabi Isa (A.S) kamar haka: Ali Dan Abi Dalib (A.S) Hassan Dan Ali (A.S) Husaini Dan Ali (A.S) Ali Dan Husaini (A.S) Muhammada Dan Ali (A.S) Ja'afar Dan Muhammad (A.S) Musa Dan Ja'afar (A.S) Ali Dan Musa (A.S) Muhammad Dan Ali (A.S) Ali Dan Muhammad (A.S) Hasan Dan Ali (A.S) sai na karshensu Imam Muhammad Mahadi Dan Hasan (A.S) wanda zai cika Duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci.

A kowace al'umma wasiyyan annabawa da mabiyansu 'yan kadan sukan shiga halin wariya da kawar da su gefe guda a tsawon rayuwar duniya, sai 'yan kadan daga cikinsu da sukan rike jagoranci na wani dan lokaci. A kodayaushe al'amarin shugabanci da iko yakan ci gaba a hannun wadanda suka yi galaba a kan wasiyyan annabawa ne.

Farkon sabani da ya faru a al'ummar Manzo (S.A.W) shi ne na ranar da ya yi wafati yayin da jama'r annabi ta saba wa wasiyyar da ya bari na jagorancin imam Ali (A.S) a kan al'umma, wasu kuwa 'yan kadan da aka fi sani da Shi'ar Ali (A.S) ko kuma Shi'ar Ahlul Baiti (A.S) suka dake a kan hakan.[1]

Daya bangaren da ya yi galabar samun halifancin Manzo (S.A.W) wanda daga baya aka kira su da Ahlussunna a lokacin halifancin Mu'awiya dan Abu Sufyan. Koda yake yana da kyau a gane cewa da farko kalmar Sunna da ake nufi an kafa a wannan shekaru ba ana nufin abin da Manzo ya bari ba ne, abin da ake nufi shi ne la'antar Imam Ali ne da Daular Umawiyya ta assasa lokacin Halifancin Mu'awiya Dan Abi Sufyan, shi ya sanya Hajjaj Assaffah Assakafi yakan ce: "Shekarar kafa Sunna da jama'a, Shekarar Arba'in".[2]

Saboda haka Ahlussunna a wancan lokaci suna da ma'ana daban da ma'anar da ake nufi a yau, kamar yadda mabiya Mazhabar Ahlil Hadisi ta Ahmad Dan Hanbali ana kiran su da Ahlussunna, wato ba su yarda da hankali ba koda a wajan tabbatar da al'amuran Akida kamar Samuwar Allah da Siffofinsa sai ta hanyar hadisai, ko da yake su ma da farko ana kiransu Ahlil Hadis ne. Akwai kuma ma'anar da yawanci take zuwa kwakwalen mutane game da Ahlussunna a yau wato wanda ba ya kan tafarkin Ahlul Bait (A.S).

An samu sarakuna sun ci gaba da mulki a Duniyar musulmi shekaru masu yawa wanda da farko an kafa sharadin halifanci ga Kuraish a lokacin wafatin Manzo (S.A.W) har halifanci ya koma hannun Turkawa ta hanyar dogara da fatawar Abu Hanifa da ya jefar da sharadin kuraishanci ga halifan musulmi, al'amarin da ya sanya a siyasance Daular ta sanya hannun karfe wajan kare Mazhabar hanafiyya da kuma daukaka shi fiye da sauran ma'abota mazhabobi, Daular ta fara daga kakan su halifofin Daular Usmaniyya wato Usman har zuwa lokacin da Daular ta rushe a lokacin Kamal Atatuk a hannun Turawan yamma 'yan mulkin mallaka, suka rusa daular suka kuma salladu a kan kasashen musulmi da arzikinsu gaba daya.

A duk tsawon wadannan shekaru dubu daya da dari hudu tun ranar da Manzo (S.A.W) ya yi wafati har zuwa yau mabiya Ahlul Baiti (A.S) wata al'umma ce da take karkashin zalunci na kuraishi na Umayyawa, sannan a hannun Abbasawa da Usmaniyyawan Turkawa. A Tarihin dan Adam mabiya Ahlul Baiti (A.S) su ne Jama'ar da ta fi kowace al'umma dadewa tana karkashin zalunci mai tsanani na masu hukunci, karanta Tarihin al'ummu da jama'u da suka yi dauki ba dadi da asakala da sarakunansu shi yake nuna gaskiyar wannan magana.

Duba Tarihin "Sufurin Makabin" jama'ar da suka yi asakala da sarakunan Yahudawa da Gwamnatin Rum bayan Musa (A.S), nan da nan a ka kore su suka koma duwatsu da dazuka da koguna da sahara, suka kuma rubuta masifun da suka same su da tarihinsu har suka kare. Haka ma muminan da aka bari bayan Isa (A.S) suka fuskanci irin wannan su ma nan da nan suka kare.

Amma Mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) sun fuskanci kashe Imamansu tun daga na farko har na goma sha daya da kuma haramta musu rubuta ra'ayoyinsu, kusan farkon abin da dauloli sukan fitar na sharudda a kan mabiya mazhabar Ahlul Baiti (A.S) shi ne haramta musu rubuta ra'ayoyinsu koda ma Hadisan Annabi ne da Tafsirin Kur'ani, kuma da haramta wa mutane su karanta ra'ayoyinsu, da littattafansu, ko su saurara daga garesu, ko su yi tunani game da su don su san ra'ayoyinsu, har ma a wasu dauloli da aka yi duk wanda yake karanta littattafansu ko yake rubuta su daga cikinsu ana jifansa da tuhumomi ne da karairayi iri-iri da sauran kage-kage da makiyan Sunna da Shi'a din ne suka kage su, kai ana iya jifan sa da fita daga musulunci, kuma a halatta dukiyarsa, da mutuncinsa, da jininsa.

Halifancin kuraishawa ya kare daga kan Almu'utasim Abbasi, a wannan lokaci ne Rundunar Turkawa suka mamaye duk wani abu da ya shafi tafiyar da daula, hatta da halifa a wajan su ya zama kamar dan aiki ne da yake daukar albashi! Sa'annan halifancin kuraishawa ya kare koda a suna a hannun Turkawan Usmaniyawa, shi kuwa halifancin Turkawa ya kare a hannun 'Yan mulkin mallakar yamma, dukkan alkawuransu, da dokokinsu, da siyasarsu, suka zama Tarihi.



1 next