Ali dan Abu dalibTarihin imam Ali dan Abu dalib (AS)Sunansa da nasabarsa :Ali dan Abi dalib dan Abdul mudallibi dan Hashimi dan Abdul manafi. Mahaifiyarsa :Fadimatu â€کyar Asadi dan Hashimi dan Aabdu manafi. Al-kunyarsa :Abul Hasan , Abul Husaini, Abus sibdaini , Abur raihanataini , Abu turab……. Lakabinsa :Amirul munin , Sayyidul muslimin , Imamul muttakin , Ka’idul gurral muhajjalin , sayyidul ausiya , sayyidul arab , Almurtada , ya’asubuddini , Haidar , Al-anza’al badin , Asadul lahi…… Ranar haihuwarsa :13rajab shekara talatin bayan shekarar giwa wato bayan haihuwar annabi(SAW) da shekara talatin. Inda aka haife shi:Makka cikin ka’aba. Yakokinsa:ya yi musharaka a yakokin manzo (SAW) gaba daya banda yakin Tabuka da manzo ya umarce shi da ya zauna a Madina domin tafiyar da al’amuranta amma yakokin da ya jagoranta da kansa a lokacin halifancinsa su ne :Aljamal da Siffaini da Annahrawan. Matansa:1-Fadimatuz zahra (AS)’yar manzon Allah (SAW) 2- Amama â€کyar abil asi 3-Ummul banin Alkilabiyya 4-Laila â€کyar mas’ud 5-Asma’u â€کyar Amis 6-Assahba’u â€کyar Rabi’a (ummu habib) 7-Khaula â€کyar Ja’afar 8-Ummu sa’ad â€کyar Urwa 9-Makhba’a â€کyar Imru’ul kais. Tambarin zobensa :Al-mulku lillahil wahidil kahhar.
|