Ma'ajin Sirri da Wakilci



Ma'ajin Sirri da Wakilci

Idan mutum ba shi da wani “sirriâ€‌ to ba shi da ma’ajin sirri. To mene ne wannan sirrin a rayuwar imamai? Me ne abin da sahabban imami a game ba za su iya rikewa ba sai wata jama’a da bata wuce a kidaya ta ba take da dacewa da cancantar rike shi? Kuma da haka ta sami darajar “ ma’ajin sirriâ€‌?

Hankula na baya-bayan nan manisanta daga ainihin abubuwan da suka auku a tarihi da rarrabe su suna fassara wannan  sirrin da cewa shi ne sirrorin gaibi da iko kan ababen da suka keta al’ada da kuma mu’jizoji.

Ni ina imani da ikon wannan sifa tsarkakka ta Ahlulbaiti wadanda Allah ya zabe su domin ci gaba da nauyin rungumar sako da iyar da shi bayan kaurar Manzon Allah, na yarda  suna dauke da irin wannan iko da irin wadannan ilmomi. Kamar yanda nake imani da cewa adon da suka yi da wannan karfin da kuma wadannan ilmomi ko kadan ba ya karo da dubin da musulunci ke yiwa bil Adama da ka’idojin dabi’a da kuma dabi’ar kaunu. Amma fa wanna karfi da ilmomi ba su ne “ sirrin imamâ€‌ ba.  Ai irin wannan karfi da kuma ilmomi su ne mafi bayyanar dalilai masu tabbatar da imamanci da gaskiyar da’awar imani. To me zai sa imami ya boye wadannan al’amura ya kuma yi wasici ga sahabbansa da boyewa, a riwayoyi mayawaita, wadanda yawansu da karfafa juna ya kai littafan shi’a na hadisi suna kebe babi mai suna “babin boyewaâ€‌? Dole ne wannan sirri ya zama cewa idan ya yadu zai zame wa Imam da sahabbansa wani hadari mai girma, wannan kuma ba zai zama al’amuran gaibi da masu  keta al’ada ba.

  Shin sirrin shi ne ilmomi da ma’arifar Ahlubaiti? Shin shine irin ganinda mazhabin Ahlulbaiti yake yi wa musulunci da fikihunsa da kuma hukunce-hukunce sa? Ba mu musun cewa ilmomi Ahlulbaiti ana yada su a zamanin danniyar Umayyawa da Abbasiyawa ta hanyar hikima da dabara domin kada ko wani sususu da shashasha ya kutsa cikinsu, amma wadannan ilmomi ba zai yiwu a ce su ne sirrin Imam ba. Duk da kebantar da take tattare da wadannan ilmomin ana karantar su a daruruwan makarantin  fikihu da hadisi a wadansu manyan biranen lardunan musulunci a wancan lokacin. â€کYan shi’a sun kasance suna nakaltawa juna wadannan ilmomin tare da sharhinsu. Muna iya cewa wadannan ilmomi da ma’arifa kebantattu ne amma ba na sirri ba. Kebantuwarsu tana nufin cewa yaduwarsu ta takaita ga haular â€کyan shi’a, amma a halaye na musamma suna isa ga wadanda ba shi’a ba ma. Sam ba masu takaita da kadan daga sahabban  imamai, boyayyu ga wanin su ba ne.

  Gaskiyan al’amarin shi ne sirrorin su ne al’amuran da suke ta’allaka da bayanan da suka danganci shirin tsare-tsaren imami,……….shirin da yake kutsawa cikin filin daga a siyasance da zimmar cimma manufar juyi,…… ko wadanda suka danganci dabarun da shirin ya haifar, ko ayyukan da zai aiwatar, ko suka danganci sunaye da nauye-nauye mambobin shirin ko hanyoyin kudi ko labarai, da rahotannin da suka ta’allaka da muhimman ababen da suke faruwa. Wadannan da ire-irensu sirrori ne wadanda ba dama wani ya tsinkaya idan ba jagora ba ko mataimakan da suke rike da ayyuka daban daban. Tana yiwuwa a sami yanayin da ya dace da bayyana wadannan sirrori a kwaye lulubinsu, ko a kusa ko kuwa tare da jinkiri, sai dai kafin wannan lokaci ba dama wani ya sami masaniya kan wadannan sirrori face wanda aikinsu yake da dangantaka da su kai tsaye, su ne kuwa “ma’ajin sirriâ€‌. Duk wani zarcewarsu zuwa ga makiya (shi kuwa laifi ne mai girma wanda ba’a yafewa) laifi ne wanda ka iya janyo rushewar jihadi da ayyuka da kuma tsararrar jama’an nan. Wannan zai fahimtar da mu abin da Imam (a.s) yake nufi da cewa:  “ Jidalin da mai gaba da mu (nasib) yake janyo mana baya wuce wanda  mai baza sirrinmu zuwa wanda ba ahalinsa ba yake jawowa. Mai baza sirrinmu  ba zai bar duniya ba sai makami ya ci shiâ€‌[1]

KOFA DA WAKILI

A  alakar sirri tsakanin Imam (a.s) da shi’a ta yiwu a bukaci isar musu da wasu bayanai ta hanyar “ mai shiga tsakaninâ€‌ ko kuma sila. Wannan kuwa dabara ce mai ma’ana, abin da aka saba bisa alada. Yan leken asiri masu lababawa da zimmar gane alakokin Imam (a.s) su kan faki zaman ganawarsa da mabiyansa a lokacin aikin haji a Makka da Madina yayin da ayarai daga nisan duniya suke zuwa. Fakon irin wadannan zama ya kan kai ga ganowa bakin zaren babban shirin tsare-tsaren Imam. Saboda haka kake ganin Imam (a.s) wani lokaci yana nisanta wasu mutane daga gare shi da kalami mai taushi, a wani lokacin kuma da lafazin suka. Alal misali Imam ya ce da Sufyan Sauri:- “Kai mutum ne abin nema, sarauta kuma tana da â€کyan leken asiri a kanmu, saboda haka ka fita amma ba korar ka aka yi baâ€‌[2]

Wani lokaci sai ka ga Imam (a.s) yana rokon jinkai ga mutumin da ya yi kicibis da shi a kan hanya amma ya kau da kai kamar bai gan shi ba, a  wani zubin kuwa yana laifanta wani wanda ya gan shi a makamancin wancan yanayin ya kuma yi wa Imam sallama tare da karramawa da girmamawa.[3]

  Irin  wadannan yanayi na bukatar samuwar wani mutum da zai zama sila taskanin Imam  da mai neman bayanai masu iso shi daga wajen Imam, to wanna silan shi ne “kofaâ€‌ kuma wajibi ne ya zama daya daga mafiya amincin mabiyan Imam, wadanda suka fi kusaci da shi, kuma suka fi wadatuwa wajen sanin bayanai da hanyoyin sadarwa. Dole ne ya zama tamkar kudan zuma wacce da muggan kwari za su san zumar da take dauke da ita da sun sassare ta sun kuma kai hari kan gidanta.[4]



1 2 next