ZamaninBayyana



3- Ruwayoyin da suke nuna wahalhalu da bakin ciki da lalacewar al’amuran duniya.

4- Ruwayoyin da suke nuna dimuwa da rashin sanin makamar akidun addini da hakikanin imam Mahadi (A.S) sakamakon tsawaituwar boyuwarsa.

5- Ruwayoyin da suke nuna yaduwar jahilci a duniyar musulmi.

6- Ruwayoyin da suke nuna sabanin ra’ayoyi da daduwar kungiyoyi da mazhabobin bata.

7- Ruwayoyin da suke nuna karkacewar masu mulki da shugabannin kasashen musulmi da fasikanci da fajircinsu da kaucewarsu daga tafarkin gaskiya.

8- Ruwayoyin da suke nuna yaduwar karkacewa da sabo a al’ummar musulmi kamar zina, da wakoki, da wasannin banza, da neman jinsin juna da makamantansu.

B- Samuwar ruwayoyi da suke nuna bangaren ci gaba da yaduwar wayewar ilimi mai girma kamar sana’a da tattalin arziki musamman alakoki, abin da za a iya kiran sa da ci gaba da kyautatuwar halayen mutane ta wannan bangaren[4]. Akwai kuma masu nuna jarrabawa ga mutane domin ware na gari daga bargurbi. Don haka wannan yana iya nuna mana abu biyu, ta bangaren farko akwai lalacewa da ci baya, ta bangare na biyu kuwa akwai ci gaba da fadada. A dukkan wadannan fagage muna iya ganin ruwayoyi da suka zo da zamu iya kasa su gida uku:

1- Ruwayoyin da suke nuna abin da ya riga ya faru kamar mayar da halifanci zuwa tsarin mulukiya, samuwar hukumar Banu Umayya da Banu Abbas da yakin kiristoci ga duniyar musulmi da duk wadannan abubuwa ne da suka faru..

2- Ruwayoyin da suka shafi abin da yake faruwa a yau kamar lalacewar dabi’u da yaduwar fasadi da alfahsha da karkata, kuma da ci gaban ilimi da alakoki tsakanin mutane.

3- Ruwayoyin da suke nuna abin da zai faru nan gaba, wanda har yanzu bai faru ba tukuna kamar bayyanar Sufyani da Yamani, da Dujal, da Tsawa daga sama, da Bayyanar imam Mahadi (A.S).



back 1 2 3 4 5 next