Hukumar MahadiFagen Hukumar Duniyar ImamMahadi (A.S) Hukumar imam Mahadi (A.S) ba ta nufin wani bangare na duniya zai kasance a hannunsa ba ne, abin da take nufi dukkan duniya zata kasance a hannunsa ne. A bisa ruwayoyin da suka zo: daularsa zata hade garin Makka da Madina da Kufa da Najaf da dukkan duniya ne, wasu ruwayoyin sun yi nuni da mamayewar musulunci ga dukkan duniya ta hannunsa, wasu kuwa a wannan al’amari sun kamanta shi da Zul-karnain (A.S) ne da hukumarsa ta hada gabaci da yammacin duniya. Akwai kuma wasu ruwayoyin da suka yi nuni da wasu kasashe da zai bude kamar Rum, Cana, Turkiyya, Dailam, Sindu, Hindu, Kabul Shah, Khazr. kuma dukkan wadannan ruwayoyoi mutawatirai ne, kamar yadda hukumarsa zata hada har da aljanu[1]. A hukumarsa babu wata alkarya da zata rage har sai an shaida da babu abin bauta sai Allah. Babu wani sabanin ra’ayi ta fuskacin addini da kasa da kabila, kuma duk wata iyaka da take tsakanin kasashe an kawar da ita. Bukair yana rawaitowa daga imam Musa kazim (A.S) game da ayar nan: Gareshi ne dukkan wanda yake sammai da kasa ya mika wuya da biyayya da kuma tilas (Ali imaran: 83), ya tambayi imam (A.S) sai ya ba shi amsa da cewa wannan game da imam Mahadi (A.S) ne, wato hukumarsa zata mamaye dukkan duniya[2], Imam Sadik (A.S) ma ya fada kamar hakan. Imam Ali (A.S) ma game da tafsirin “Shi ne wanda ya aiko manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin… (Tauba: 33, Saff: 9) ya kawo wannan ma’anar da aka ambata, wato cewa game da imam Mahadi (A.S) ne[3]. Manzon rahama (S.A.W) yana cewa: Wannan addini zai shiga duk abin da dare ya shiga cikinsa[4]. Wannan kuwa al’amari ne da yake nuna yadda addini zai mamaye dukkan duniya gaba daya. Imam Bakir (A.S) game da ayar nan: Wadannan da idan muka tabbatar da su a duniya sai su tsayar da salla su bayar da zakka… (hajji: 41) yana cewa: Wannan ta alayen Muhammad (S.A.W) ce: Mahadi (A.S) da sahabbansa, Allah zai mallaka musu gabacin duniya da yammacinta[5]. A wani hadisin imam Sadik (A.S) yana fada game da ayar: Ka gaya musu ranar budi wadanda suka kafirce imaninsu ba zai amfanar da su ba, kuma ba za a saurara musu ba. (Sajada: 29) cewa: Ranar budi, ita ce ranar da za a bude wa imam Mahadi (A.S) duniya.[6] Tsawon zamanin hukumar imam Mahadi (A.S) Ruwayoyi masu yawa sun zo suna bayanin farkon tashinsa da farawar gwagwarmayarsa ta juyi da cibiyar daularsa, amma an samu sabani mai yawa game da tsawon shekarun zamanin da daular imam (A.S) zata yi da sabani mai yawa. Wasu ruwayoyi sun iyakance shi da shekaru bakwai, wasu sun zo da shekaru takwas masu tsawon shekaru saba’in na wannan zamanin namu, wasu kuwa sun zo da shekaru goma sha bakwai, da sha tara, da ma watanni, da shekaru talatin da tara, da arba’in, da saba’in, kai har ma da 309 adadin tsawon baccin As’habul kahafi a cikin kogo, wasu ruwayoyin ma sun zo da cewa zata dade har zuwa tashin kiyama[7]. Wasu ruwayoyin sun yi nuni da cewa, shekaru sun ninninka yadda suke; wato saboda sannu-sannu a cikin juyawar falaki duk shekar daya zata zama tana da tsayin shekaru goma irin na yau, wata ruwayar ta yi nuni da abin da kur’ani ya yi magana na kasancewa rana daya tana da tsayin shekaru 50 000 ne daga shekarun duniya[8]. A wata ruywa daga Manzo (S.A.W) ya zo cewa: Zai rayu a cikinsu shekaru bakwai, ko takwas ko tara, matattu zasu yi burin su rayu domin su ga adalci da nutsuwa[9]. Mufaddal dan Umar ya tambayi imam Sadik (A.S) game da tsawon muddar hukumar imam Mahadi (A.S), sai ya ba shi amsa yana mai nuni da wata aya, ya ce: “… shi mai dawwama ne har abada, mulki ne wanda ba ya karewa, hukuma da ba ta yankewa, al’mari ne da ba ya bacewa sai da zabin Allah da nufinsa wanda ba wanda ya sani sai shi, sannan sai alkiyama ta zo da dukkan abin da Allah ya siffanta a littafinsaâ€[10]. A wani hadisin kudsi ya zo cewa: Kuma lallai hakika zan jujjuya kwanukan tsakanin waliyyan bayina har zuwa ranar kiyama[11]. Da wannan ne zamu ga cewa shekara bakwai ko takwas da kuma har abada ba yadda za a yi su hadu a hankalce, duk da hankali yana karbar tsawon muddar hukumarsa, don haka ne ya zama wajibi mu rarrabe tsakanin shekarunsa da kuma tsawon muddar daularsa da ci gabanta a hannun wasu bayansa. Sahid sadar na biyu yana fada a littafinsa mai suna “Ma ba’adaz zuhur†mafi yawancin hadisan da suka yi magana game da tsawaitar al’amrinsa suna nuni zuwa ga daularsa ne ba shekarunsa ba. Kodayake wasu ruwayoyin an karbo su ne ba daga ma’asumi ba, wasu kuwa ruwayar mutum daya ce, wanda a dunkule aka yi nuni da shekaru 309. Wasu suna ganin cewa, duba zuwa ga lokuta masu sassabawa yana nuna fahimtar cewa; bayani ne na marhaloli mabambanta na rayuwa da kuma hukumar imam Mahadi bayan bayyanarsa (A.S)[12]. Don haka ne ana iya cewa: gudanar da adalci a cikin shekaru na farko na gabatarwa (shekaru 7-8), da matsakaita (shekaru 30-40), da masu yawan mudda (shekaru 309 ko sama da hakan), saboda haka ne shahidus sadar sani, yake cewa: Tun da imam Mahadi (A.S) zai kafa hukumar adalci ne wacce zata iya dorewa har zuwa karshen zamani, to yana inganta wannan al’amari ya kasance abu ne mai yiwuwa a kasa da shekaru goma, kuma wannan abu ne ingantacce[13]. Amma wani abu tabbatacce shi ne, wanzuwarsa zata kasance har sai an samu wasu abubuwa kamar haka: “Zai cika duniya da adalciâ€. Adalci zai mamaye dukkan duniya ta yadda zalunci ba zai taba dawowa ba. Kuma ta yiwu a samu bude kasashe da cin nasara kasa da shekaru goma, amma tarbiyyar mutane da canza su yana bukatar lokaci mai tsawo ne. Dorewar hukumar Mahadi (A.S) har zuwa tashin kiyama wani abu ne wanda yake na tilas musamman idan mun yi nuni da hukumar ma’asumai da al’amarin da ya zo na raja’a. za a iya cewa bayan aikin imam Mahadi (A.S) ya kare na shimfida adalci a duniya zai koma zuwa ga ubangijinsa, amma halifofinsa zasu ci gaba da tafiyar da ita har zuwa ranar kiyama, don haka hukumarsa zata ci gaba har zuwa kiyama. [1] Tarihu Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 451 – 463. [2] Tajalli Tauhid, da Nizame Imamat, da Kitabe Bakiyyatul-Lah, Shafi: 47 – 49. [3] Abin da ya gabata. [4] Abin da ya gabata. [5] Muntakahbul asar, shafi: 470, h 1. [6] Abin da ya gabata, h: 2. [7] Ruzegare Rahayi, j 2, shafi: 601, h 791. [8] Abin da ya gabata, shafi: 635. [9] Abin da ya gabata, shafi: 601, h 791. [10] Biharul Anwar, j 13, j 53, shafi: 34 – 35. [11] Tarihu Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 620 – 633. [12] Abin da ya gabata. [13] Abin da ya gabata. |