Karshen Duniya



Mahangar Shi'a Game DaKarshen Duniya

A mahangar Shi'a: marhalolin tarihin dan Adam a marhalar sabani bayan wucewar zamanin annabwa (A.S) da wucewar imamai ma’asumai goma sha daya zai kasance kamar haka ne:

1- Zamanin boyuwa, wannan zamani ne da dauki-ba-dadi yake ci gaba tsakanin karya da gaskiya saboda rashin jagoran karshen zamani.

2- Zamanin bayyana, wato zamanin da gaskiya zata yi nasara gaba daya a kan karya da bayyanar jagoran karshen zamani.

A wannan kashe-kashen tarihin akwai muhimmin al’amari da yake nuna cewa shi’anci shi ne hakikanin musulunci da yake iya nuna wa dan Adam yadda karshen tarihinsa zai kasance.

1- Zamanin Boyuwa

A mahangar Shi'a ubangiji madaukaki bayan ya fitar da dan Adam adga aljanna sai ya aiko da annabawa domin shiryar da mutane wanda na karshensu shi ne Muhammad dan Abdullah (S.A.W).

Amma mu sani cewa; cikon annabawa ba ya nufin yanke alakar dan Adam da ubangiji madaukaki ko karshen shiriya, domin a mahangar Shi'a dalilin da yake wajabta aiko da annabawa (A.S) shi ne ainihin dalilin da yake wajabta ci gaban samuwar wannan al’amari na shiriya bayan cikamakon annabawa (S.A.W), wato saboda ci gaban samuwar shiriyar ubangiji bayan kammalar addini da cikar ni’ima[1] bayan Manzo (S.A.W) ya zama dole a samu wasu ma’asumai masu tsayawa da wannan al’amari.

Saboda haka a mahangar Shi'a imamamci ludufi ne na Allah kuma matsayi ne na ubangiji kamar anabta, wanda yake matsayi ne da Allah yake bayarwa, don haka zabar imami ma’asumi ya fi karfin al’amarin mutum[2].

Shi'a suna kore samuwar kowace irin yanke alaka tsakanin mutum da ubangiji bayan wucewar Annabi (S.A.W), suna karfafa samuwra alaka tsakanin duniyar wahayi (wato ubangiji madaukaki) da wannan duniyar ta kasa, kuma wannan aiki ne na imamai ma’asumai (A.S). Don haka ne ma da umarnin Allah imam Ali (A.S) ya zama halifan Annabi (S.A.W) da kuma sanya zuriyar Fadima (A.S) bayansa a matsayin halifofin Annabi (S.A.W) wadanda aka umarce su da ayyuka guda uku:

1- Tabbatar kafa hukumar Ubangiji

2- Makomar ilimi da addini

3- Wilaya da jagoranci

Wannan yana nufin alakar su da duniyar gaibi da kasancewarsu hujjar Allah a kan talikai wanda yake nufin samuwar cikakken kamilin mutum[3].

A mahangar Shi'a babu wani zamani da zai zo ba tare da samuwar halifan Allah a bayan kasa ba, ko zahiri mash’huri (kamar Manzon rahama a lokacin rayuwarsa), ko kuma badini boyayye (kamar imam Mahadi (A.S) a wannan zamanin) kamar yadda ya zo a ruwaya[4].

Shi'a suna ganin bayan daular addini ta Manzo da imam Ali (A.S) sauran dauloli sun kwace hakkin ma’asumai ne wadanda suke su ne hakikanin halifofin Manzo (S.A.W), kuma sun zalunce su a lokuta da dama kuma sun shahadantar da su, don haka ne ma lokacin da halifancin imami na goma sha biyu ya zo sai Allah ya boye shi daga azzalumai domin kada su kashe shi, kuma matukar tunanin mutanen duniya bai zama a shirye yake da karbarsa ba, har abada ba zai bayyyana ba kuma zai ci gaba da buya[5].

Ma’anar boyuwa: Shi'a suna imani da cewa shugaban duniya a karshen zamani an riga an haife shi a raye yake kuma yana cikinmu, sai dai saboda rashin wasu sharudda Allah ya boye shi daga mutane kamar yadda rana take buya a bayan gajimare duk da kuwa tana cikinsu suna amfana daga haskenta.

Don haka boyuwa ba yana nufin rashin samuwa a duniya ba ne, kamar yadda buyansa ba sakakke ba ne, domin yana bayyana ga wasu mutane duk sadda maslahar hakan ta kasance.

Wannan boyuwar tana da nau’i biyu ne: akwai karama da kuma babba.


1-1. Karamar boyuwa

Wannan lokacin ya fara ne daga shahadar baban imam Mahadi (A.S) imam Hasan Askari a shekara 260 hijira yayin da zalunci mai tsanani ya yi yawa a kan Shi'a a lokacin halifan abbasawa Mu’utamad. Don haka ne sai buyansa ya fara da boyuwa daga idanuwan ammawan mutane (jama’ar gari) banda kebantattun sahabbansa, al’amarin da ya kai har zuwa shekara ta 329 hijira wato shekaru 70 kenan. A wannan zamanin ya sanya mutane hudu a matsayin tsaka-tsaki tsakani a alakarsa da mutane, wadannan mutane su ne:

1- Usman dan Sa'id umari

2- Muhammad dan Usman dan Sa'id umari

3- Abul kasim Husain dan Ruh Nubkhati

4- Ali dan Muhammad Samari

Karamar boyuwa ta kare da mutuwar na’ibinsa na hudu da umarninsa a sakon da ya aika masa a rubuce kamar haka:

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai

Ya Ali dan Muhammad Samari Allah ya girmama ladanka a cikin ‘yan’uwanka, domin kai mai mutuwa ne nan da kwana shida, ka hada al’amarinka, kada ka yi wa wani wasiyya da shi domin ya tsaya a matsayinka bayan mutuwarka, hakika boyuwa cikakkiya ta faru….[6] …ka sani duk wanda ya yi da’awar ya gan ni kafin bayyanar sufyani da tsawa, to shi makaryaci ne kuma mai kage ne…[7].

2-1. Boyuwa Babba

Wannan lokacin ya fara tun daga shekara ta 329 hijira har zuwa wannan zamani namu a yau, a ruwayar Shi'a ma’anar boyuwarsa tana nufin ma’ana biyu ne[8]:

Ma’anar farko ita ce; yana ganin mutane amma su ba sa ganin sa kamar yadda ya zo a wata ruwaya.

Ma’ana ta biyu ita ce; mutane suna ganin sa amma ba su san shi ba, kuma ba sa gane cewa shi suka gani.

Hadisin da Rayyan ya karbo daga imam Rida (A.S) yana kunshe da wannan ma’anar ce: yana fadi game da imam (A.S) cewa ba a ganin jikinsa, kuma ba a kiran sa da sunansa[9]. Amma ruwayar na’ibinsa na biyu wato shaikh Muhammad dan Usman yana cewa na rantse da Allah duk shekara yana zuwa aikin hajji, yana ganin mutane yana sanin su, amma su mutane suna ganin sa sai dai ba sa gane shi[10].


Abubuwan Da Suka Kebanta Da Boyuwa Babba

1- Alakar imam (A.S) da mutane ta hanyar na’ibansa na musamman ta yanke, a wannan zamani imam (A.S) ya ayyana na’iban ne a dunkule wato su ne malamai wadanda suke hujja a kan mutane a kan al’amuransu na mas’alolin addini da hukuma, a wannan zamani babu mai haduwa da shi sai tsarkakan mutane su ma bisa dacewa[11].

2- Wannan zamani lokaci ne na jarrabawa ga muminai bisa sunnar Allah, amma mabiya masu ikhlasi ga imam (A.S) a wannan zamani ne za a rene su. Lokaci ne na tankade da rairayar bayin Allah na gari, da jarrabawa domin tsame na gari wadanda da su ne addini zai ci gaba da tsayar da adalci a bayan kasa.

3- Zamanin boyuwa babba ta wani bangaren lokaci ne na ci gaban ilimi da kimiyya da alaka, a daya bangare kuma lokaci ne da hukumar zalunci da danniya zata yawaita a duniya cike da zalunci[12], kuma za a iya kiran wannan lokaci zamanin sauraro.

Ma’anar Sauraro Da Kuma Siffofin Mai Sauraro

Sararo yana da ma’ana mai fadi sosai da ta hada da addini da wajen addini, kuma dukkan dan Adam yana sauraron wani hadafi a nau’in halittarsa da cikin zuciyarsa ko wane addini ne da shi.

Mutum a wannan marhala yana damfare da sauraron tabbatar hukumar Allah ce mai adalci da rayuwa ta daidaito wacce take ita ce hadafin halittar ‘yan Adam.

A mahangar Shi'a sauraro yana nufin bude idanuwa da sauraro domin fuskantar mai tseratar da dan Adam hujja dan Hasan Askari (A.S) wanda da bayyanarsa ne zai kawar da hukumomin zalunci kuma ya tsayar da adalci da taimakon mutanen duniya.

Mai sauraron imam Mahadi (A.S) dole ya zama yana da wadansu siffofi:

1- Ta fuskancin akida: dole ya kasance mai imani da jagorancin imam Mahadi (A.S).

2- Ta fuskacin ruhi: dole ne ya kasance mutum mai neman tabbatar adalci cikakke, mafi karanci shi ne ya kasance mai sauraronsa a kowane lokaci.

3- Ta fuskacin aiki da dabi’a: dole ne ya kasance mai damfaruwa da hukunce-hukuncen Allah da biyayya sau da kafa ga umarnin Allah, mai nisantar dukkan abubuwan da aka haramta da zuwa da dukkan wajibai[13].

Don haka sauraron ba yana nufin jefar da gyara al’amuranmu ba domin mu jira sai imam Mahadi (A.S) ya bayyana sannan sai mu fara gayara, ko mu ma mu shiga cikin azzalumai da masu barna da fasadi, domin wannan yana nufin wurgi da dokokin Allah (S.A.W) da yofinta daga umarninsa, abin da kur’ani da ruwayoyin da suka zo daga ma’asumai suka yi nuni da haramcinsa karara. Don haka mummunar fahimta game da ma’anar sauraron imam Mahadi (A.S) ta saba da kur’ani da hadisai kai tsaye:

“Kada ku yi barna a bayan kasa bayan gyara ta”. A’arafi: 56[14].

Daga cikin wasikar da imam Mahadi (A.S) ya aika wa shaikh Mufid yana cewa: “Kowannenku ya yi aiki da abin da zai kusantar da shi zuwa garemu, ya sanya soyayyarmu gareshi, ya nisanci duk wani aiki da yake sanya rashin yardarmu, domin al’amarinmu zai bayyana ne bagatatan[15].

Boyuwarsa ta yi kama da ta annabawa don haka muka ga shaihul Saduk yana kawo boyuwar annabawa kamar; Idris, Salihu, Nuhu, Ibrahim, Yusuf, Musa da wasiyyansu, yana kawo bayanin boyuwarsu a babin boyuwa a littafinsa na “Kamaluddin wa tamamun ni’ima”[16]

Kur’ani mai girma ya yi bayanin boyuwar annabawan da suka gabata kamar Khidr (A.S) wanda boyuwar imam Mahadi (A.S) ta yi kama da boyuwarsa fiye da kowacce. Boyuwa ce da saboda mu’ujizar kur’ani ba wanda ya iya musun ta.

Wanan kissa da Khidr (A.S) da Musa (A.S) ta zo a cikin surar Kahafi[17] wacce take kunshe da muhimman abubuwa kamar haka:

1- Boyuwar Khidr da rashin saninsa duk da kuwa yana rayuwa a cikin mutane, ba don Allah ya yi bayaninsa ba, ba wanda zai san shi.

2- Kamar yadda Khidr (A.S) yake sane da mas’alolin al’umma da na duniya kamar yadda ya san cewa shugabanni suna kwace jiragen ruwa marasa aibi don haka ya aibata shi, haka nan imam Mahadi (A.S) yake sanin al’amura da halayen duniya na raunanan mutane dalla-dalla.

3- Kamar yadda lalata jirgi da Khidr ya yi ya zamanto a boye ne, domin da masu jirgi sun gan shi da sun hana shi yin hakan, haka ma imam Mahadi (A.S) yake tasarrufi a boye cikin al’amura masu yawa ba tare da mutane suna ganinsa ba.

4- Shiryar da Annabi Musa (A.S) ga wasu al’amura ta hanyar Khidr (A.S), wato gina mutum da aiwatar da sakon Allah, haka ma imam Mahadi (A.S) yake gina mutane yana aiwatar da sakon Allah a boye[18].

Don haka ne imam Mahadi (A.S) bayan kare mazhaba da yake yi daga rushewa da kaucewa kuma shi ne akwatin sirrin Allah mai tarbiyyantar da mutane a boye a duniya.

Wasu daga ayyukan da suka faru a lokacin wannan boyuwar tasa babba mai tsayi sun hada da:

1- Tseratar da musulmi daga hannun karkatattun sarakuna masu kauce wa hanya.

2- Tseratar da wasu jama’ar musulmi daga hannun wasu ‘yan fashi da masu tare hanyar matafiya da karauka.

3- Gargadin ga mutane da tsoratar da su, da nuna musu cewa har yanzu sharuddan bayyanarsa ba su cika ba, kuma mutane ba a shirye suke da su dauki wannan nauyi mai girma ba.

4- Mayar da Hajarul aswad wajan da yake a Ka’aba a shekarar 339 ko 337 bayan harin Karamida zuwa Makka a sherkarar 317 da suka dauke dutsen Hajarul aswad.

5- Bayar da labarin wasu abubuwa muhimmai na siyasa da al’umma kafin mutane su sani.

6- Nasiha da son alheri ga mutane da kuma kama hannunsu da dora su kan tafarkin kyawawan halaye.

7- Bayar da taimakon dukiya ga wasu.

8- Warkar da masu cututtuka masu nakasa wadanda likitoci suka kasa yin maganinsu.

9- Nuna wa wadanda suka bace a Sahara hanya da kuma isar da wadanda aka bari a baya zuwa ga ragowar karauka.

10- Koyar da addu’a da zikiri masu madaukakan ma’anoni ga wasu mutane.

11- Dagewar imam Mahadi (A.S) a kan karanta addu’o’in kakanninsa tsarkaka wadanda suke kunshe da ma’anoni madaukaka, da hakikanin gaskiya da imani, wadanda an rubuta misalansu da yawa[19].

2- Zamanin Bayyana

A imanin Shi'a lokacin bayyanar imam Mahadi (A.S) wani abu ne wanda yake mai aukuwa a tilas da ba shi da makawa, koda kuwa rayuwar duniya ta rage saura kwana daya ne to sai Allah ya tsawaita wannan ranar domin ya zo ya kafa hukumar adalci.

A wannan mahanga imam Mahadi (A.S) shi ne misalin kadaita Allah a duniya a karshen zamani da bayyanarsa ne sunayen Allah kyawawa zasu samu bayyanar ma’anarsu kamar: Al’waliyyu, Al’adilu, Al’hakimu, Assuldan, Almuntakim, Al’mubiru, Al’kahiru, Azzahiru, bayyanar da ba su taba yin irinta ba da can, kuma matsayin halifan Allah a bayan kasa zai bayyana a aikace[20].

Ma’anar bayyana

Bayyana a mahangar Shi'a yana da ma’ana biyu ne kamar yadda zamu kawo a kasa:

1- Futowa daga cikin hijabin shamakin boyuwa.

2- Shelanta juyin juya hali da samar da juyin duniya mafi girma a kan zalunci.

Dukkanin wadannan ma’anoni guda biyu suna gaskata ga Bakiyyatul-Lah imam Mahadi (A.S), don haka zai zama shugaban duniya a zahiri a karshen zamani bayan fitowa daga shamakin labulen boyuwa da samar da juyin juya hali a kan zalunci a fili[21].

Amma game da yanayin duniya kafin bayyanarsa zamu iya kasa ruwayoyin da suka zo daga Shi'a kashi biyu kamar haka:

A- Ruwayoyin da suka zo suna nun alalacewar dan Adam a dabi’unsa da matsaloli da rushewar kyawawan dabi’u ta yanda zai zama mafi kaskanci daga dabbobi. Da yaduwar zalunci da fasadi a siyasance da al’ada da tafiyar da al’amuran al’umma, da tsaro da kekashewar zukata wanda daga karshe mutum zai tuke da kaiwa ga siffar kura da kyarkeci. A lokacin yanke kaunar samun gyaran yanayin duniya zai bayyana a fili.

Wadannan ruwayoyi zamu iya kasa su kamar haka:

1- Ruwayoyi mutawaitirai da suke nuna cikar duniya da zalunci gaba daya wadanda suke tawaturancinsu ya zo daga Sunna da Shi'a duka[22].

2- Ruwayoyin da suke nuna faruwar rikici mai yawa da rashin zama lafiya.

3- Ruwayoyin da suke nuna wahalhalu da bakin ciki da lalacewar al’amuran duniya.

4- Ruwayoyin da suke nuna dimuwa da rashin sanin makamar akidun addini da hakikanin imam Mahadi (A.S) sakamakon tsawaituwar boyuwarsa.

5- Ruwayoyin da suke nuna yaduwar jahilci a duniyar musulmi.

6- Ruwayoyin da suke nuna sabanin ra’ayoyi da daduwar kungiyoyi da mazhabobin bata.

7- Ruwayoyin da suke nuna karkacewar masu mulki da shugabannin kasashen musulmi da fasikanci da fajircinsu da kaucewarsu daga tafarkin gaskiya.

8- Ruwayoyin da suke nuna yaduwar karkacewa da sabo a al’ummar musulmi kamar zina, da wakoki, da wasannin banza, da neman jinsin juna da makamantansu.

B- Samuwar ruwayoyi da suke nuna bangaren ci gaba da yaduwar wayewar ilimi mai girma kamar sana’a da tattalin arziki musamman alakoki, abin da za a iya kiran sa da ci gaba da kyautatuwar halayen mutane ta wannan bangaren[23]. Akwai kuma masu nuna jarrabawa ga mutane domin ware na gari daga bargurbi. Don haka wannan yana iya nuna mana abu biyu, ta bangaren farko akwai lalacewa da ci baya, ta bangare na biyu kuwa akwai ci gaba da fadada. A dukkan wadannan fagage muna iya ganin ruwayoyi da suka zo da zamu iya kasa su gida uku:

1- Ruwayoyin da suke nuna abin da ya riga ya faru kamar mayar da halifanci zuwa tsarin mulukiya, samuwar hukumar Banu Umayya da Banu Abbas da yakin kiristoci ga duniyar musulmi da duk wadannan abubuwa ne da suka faru..

2- Ruwayoyin da suka shafi abin da yake faruwa a yau kamar lalacewar dabi’u da yaduwar fasadi da alfahsha da karkata, kuma da ci gaban ilimi da alakoki tsakanin mutane.

3- Ruwayoyin da suke nuna abin da zai faru nan gaba, wanda har yanzu bai faru ba tukuna kamar bayyanar Sufyani da Yamani, da Dujal, da Tsawa daga sama, da Bayyanar imam Mahadi (A.S).

ta yiwu muna iya cewa al’amarin bayyanar imam Mahadi (A.S) a mahangar Shi'a wani abu ne da Allah ya boye shi kuma ya zama sirri domin samun nasarar imam Mahadi (A.S) a kan makiyansa, don haka ne ma ruwayoyi suka zo suna karyata duk wani wanda yake ayyana lokaci; kamar wata ko shekara ko ranar da zai bayyana.

Amma za a iya bayanin alamomin bayyanarsa a dunkule kamar bayyanarsa a ranar ashura ko kwankin da suke wutiri ba shafa’I ba kamar ranar asabar. Sai dai ba yadda za a iya sanin wace ashura ce zai bayyana ko wace asabar ce ko jumma’a. Koda yake ruwayoyin da suka nuna shekarar bayyanarsa a wutiri take ‘yan kadan ne, amma cewa ranar ashura zai bayyana wannan ya zo da ruwayoyi masu yawan gaske da za a iya tabbatar da shi[24].

Ta kowane hali dai ba wanda ya san lokacin bayyanara sai Allah, kuma duk sadda ubangiji ya so ya bayyanar da shi to wannan zai tabbata, sai dai a dunkule idan mun duba ruwayoyi da hadisai zamu ga wannan bayyanar a kusa take idan an samu:

1- Fadawar mutane daidaiku da al’umma gaba daya cikin halin yanke kauna.

2- Gazawar addinan daga samar da abin da suke da’awarsa, kamar tsarin jari-hujja da ya gaza samar da ‘yanci na hakika, da kuma kwaminisanci da ya kasa samar da adalcin zamantakewa da na tattalin arziki da sauransu.

3- Wulakanta kimar addinan Allah a cikin al’ummu kamar bayyanar da munkarai da munanan dabi’u da halaye, kuma da halatta su kamar neman jinsin juna kamar dabbobi, da cin riba, da cin dukiyar mutane, da halatta giya da sauran kayan maye, da yawaitar saki, da karo da juna tsakanin aiki da zance, da cin shubuha, da yawaitar zina da zubar da jini, da halatta yin karya, da cin rashawa, da yanke zumunci, da yaduwar kage da karya, da bidi’o’I, da shugabancin jahilan mutane, da halatta waka da wasanni da muzik.

Da wulakanta mumini, da fakiri, da malami, da girmama fasiki, da azzalumi, da bata hukunce-hukuncen Allah, da halatta dukkan haram din Allah, da take wajiban Allah a kasa[25].

4- Addini da ma’abotansa zasu zamanto baki a cikin al’ummu, kuma kamar yadda mutane a farkon musulunci suka rika shiga cikin addinin jama’a-jama’a (surar Nasr) haka nan zasu rika fita daga cikinsa jama’a-jama’a[26].

5- Faruwar wasu abubuwa na sama da na kasa da suka hada da[27]:

- Yin ruwan sama na kwana arba’in

- Faruwar fitina da yaki mai tsanani da kashe sama da mutane miliyan uku, da rushe wasu birane da wasu garuruwa da dimuwa da firgici.

- Yaki da kashe-kashe a Iraki da Bagadad, kuma da mamaye ta, kuma da abubuwa masu yawa da zasu faru a Iraki da Kufa da Basara da Bagadad.

- Yunwa da Fari.

- Zuwan tuta tamanin zuwa yakin larabawa. (Ta yiwu tana nufin kasashe tamanin ne).

- Kashe wasu daga sarakuna.

- Motsin wasu mutane da gwagwarmayar neman hakki kamar Yamani, da Sayyid Khurasani, da Hashimi daga Gilana.

- Yaduwar wasu cututtuka masu kisa kamar annoba.

- Faruwar wasu canje-canje a sama kamar sama ta yi ja ta takure, da alamomi a rana da wata kamar bayyanar fuskar Annabi Isa (A.S) a rana da kuma faruwar iska ja da baka.

- Yaduwar wuta a wasu kasashe (tayiwu yaki ne a kan mai)

- Lalacewar ‘ya’yan itace a kan bishiyoyi (tayiwu saboda lalacewar yanayi da waje ne)

- Bayyanar masu da’awar annabta (masu da’awa 60)

- Juyin juya halin masu rauni a kan masu girman kai.

- Bayyanar Dujal.

6- Faruwar abubuwa 5 wadanda faruwarsu dole ne a cikin wasu watanni[28]:

- Bayyanar Sufyani.

- Kisfewa da ruftawar kasa.

- Kashe Nafsuz zakiyya.

- Kira daga sama cewa Mahadi (A.S) zai bayyana da kuma neman yi masa bai’a.

- Bayyanar Yamani

7- Shugabancin tattaunawar azzaluman kasashe kafin bayyanar Mahadi (A.S) wanda zai sanya yaduwar zalunci a duniya ta yadda za a kirga samuwar adalci wani abu ne wanda ba zai yiwu ba.

8- Yankewar kauna daga mutane daga samun gyara da kaunar samun wani mutum daga wajen Allah wanda zai zo domin tseratar da mutane, koda yake wannan al’amari yana bukatar gyara daga su kansu mutane domn Allah ba ya canza wa mutane abin da yake garesu har sai sun canza abin da yake ga kawukansu. (Ra’ad: 11)

Faruwar wannan canjin daga kawukan mutane da kuma taimakon Allah shi ne zai iya bayar da damar bayyanar Mahadi (A.S). Don haka ne neman bayyanarsa daga wajen Allah a aikace da mutane zasu yi yana daga cikin abin da zai sanya hakan, ba kawai a lafazin (maganar) baka ba.

9- Faruwar neman tattauna domin samar da adalci a duniya baki daya. Wannan kuwa zai kasance ne alhalin tattaunawa bisa yin zalunci ta riga ta yadu a duniya kuma ta mamaye ta, sai tattaunawa a kan yin adalci ta zo domin maye gurbin hakan wanda yake yana da alaka da bayyanar imam Mahadi (A.S).

10- Samuwar mutane masu tsarkin zuciya da sadaukarwa domin samar da gudanar da adalci, wadanda suka ci jarabawar Allah da daukaka, kuma suna shirye da yaki a cikin rundunar jagoran karshe.

Da izinin Allah bayyanarsa zata kasance, kuma zamanin juyi da cin nasarar adalci zai zo.



[1] Ma’ida: 3.

[2] Murtada Mudah’hari, Imamat Wa Rahbari, Shafi 92 – 94.

[3] Abin da ya gabata shafi: 55 – 83.

[4] Nahajul Balaga, Tarjume Muhammad Dashti, Shafi: 660 – 661.

[5] Ali Dawani, Danishmandan Amme Wa Mahadi Mau’ud, Shafi: 7-9.

[6] Allama Majlisi, Biharul Anwar, j 51, shafi 361. 

[7] Abin da ake nufi wani ya yi da’awar ya gan shi kuma ya yi da’awar ya sanya shi na’ibinsa na biyar.

[8] Muhammad Sadar, Tarih Gaiba Kubra, Shafi: 48 – 61.

[9] Shaihus Saduk, Kamaluddin Wa Tamamunni’ima, Shafi 370.

[10] Shaikh Dusi, Littafin Al’gaiba, Shafi: 221.

[11] An cirato daga littattafai masu yawa kamar Biharul Anwar jildi 13, j 53, shafi 213 – 221.

[12] Muhammad Sadar, Tarih Gaiba Kubura, Shafi: 34 – 37.

[13] Muhammad sadar, Tarih Gaiba Kubura, shafi: 356 – 359.

[14] Ayoyin Ma’ida: 44, 45, 47.

[15] Dabarasi, Ihtijaj, J 2, Shafi: 324. Da Sayyid Muhammad Sadar Shafi: 446.

[16] Kamaluddin Wa Tamamaunni’ima, J 1, Shafi: 254 – 303.

[17] Ayoyi: 65 – 68.

[18] Ayatul-Lahi Ja’afar Subhani, Bakiyyatul-Lah, Shafi: 70 – 76.

[19] Tarihi Gaibatul Kubura, Shafi: 143 – 158.

[20] Tajalli Tauhid Dar Nizame Imamat, Shafi: 44.

[21] Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Sayyid Muhammad Sadar, Shafi: 270 – 271.

[22] Mutawatirai ne ta yadda ya zama mustahili ne su zama karya saboda yakinin da suke bayarwa.

[23] Sayyid Muhammad Sadar Tarih Gaiba Kubura, Shafi: 289 – 347.

[24] Sayyid Muhammad Sadar, Tarihi Ma Ba’adaz Zuhur, Shafi: 287 – 296.

[25] Kamil Sulaiman, Ruzegare Rahayi, j 2, Shafi: 701-723. Da Ayatul-Lahi Ludful-Lah Safi Gulfaigani, Muntakhabul Asar, Shafi: 424 – 438.

[26] Littafin da ya gabata, j 2, shafi: 721, hadisi 1721, 1033. Da Muntakhabul Asar, Shafi: 424 – 438.

[27] Littattfan da suka gabata da wasunsu masu yawa.

[28] Abin da ya gabata.