Addinin Musulunci



“Sai dai muna jifan barna da gaskiya ne sai ta bata ta sai ga ta a rushe”. Anbiya: 21.

“Hakika barna mai gushewa ce”. Isra’: 81.

Na biyu: Ubangiji zai cika haskensa koda kuwa kafirai sun ki.

“Suna son su rushen hasken Allah da bakunansu, Allah kuwa mai cika haskensa ne koda kuwa kafirai sun ki”. Saff: 8.

Na uku: Addinin Allah wato musulunci zai yi galaba a kan duk wani addini.

“…kuma da addinin gaskiya domin ya dora shi a kan duk wani addini”. Tauba: 33. Da Saff: 9.

A bisan asasin ruwayoyi masu yawa wannan al’amari zai kasance ta hannun Muhammad Mahadi (A.S) dan Hasan Askari (A.S) ne domin taimakon raunana da muminai salihai na gari[12].

“Koda kuwa rana daya ce ta rage zuwa ga Tashin kiyama. …da Allah ya aiko wani mutum daga ahlin gidana ya cika ta da adalci kamar yadda aka cika ta da zalunci”[13].

Duba Zuwa Ga Dalla-Dallan Tarihi

Kur’ani yana ganin cancanjawar tarihi wani abu ne wanda yake karkashin dokokin sunnar Allah. Idan muka duba kur’ani a dunkule zamu ga cewa; yana ganin dokokin halitta da na shari’a daidai suke a kowace al’umma, zamu ga hikimar kawo tarihin wasu mutane da al’ummu da sakamakon ayyukansu domin daukar darasi ne daga abin da ya gabata. Daukar darasi kuwa ba zai yiwu ba sai idan al’amarin tarihi bai takaita da mutum daya ko wata jama’a ba, ya zama wani abu ne da wasu al’ummu zasu iya maimaita shi:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 next