Ayar TsarkiAYAR TSARKAKEWA DA MA'ANAR IYALAN ANNABI A MUSULUNCI
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Zance dangane da ko su wanene Ahlul-Bait din Annabi (SAWA) na ci gaba da jan hankali a fagen tattaunawa ta akida a tsakanin Musulmi, masamman a duk inda 'yan Shi'a ke da bayyananniyar samuwa a tsakanin al'umma. Ra'ayoyi mabambanta kan bayyana tsakanin bangarorin Shi'a da Ahlussunna a kan haka, du a kokarin tabbatarwa ko kore wata akida. A nan, in Allah Ya yarda, za mu yi kokari wajen bijiro da abubuwan da malaman Musulunci suka bijiro da su wajen fayyace su waye ainihin Ahlin Manzo (SAWA), da jin dalilan kowa sannan da kwatanta dalilan da fitar da wanda ya fi karfi a cikin su. Bayanan Malamai kan ko su waye Ahlin Manzo (SAWA) ya zo ne yayin fassarar Ayar Tsarkakewa ta cikin Surar Ahzabi, inda Allah ke cewa: Allah na nufin kawai Ya kawar da kazanta ne daga gare ku Ahlul-Baiti, Ya kuma tsarkake ku tsarkakewa. (Surar Ahzabi, 33:33.) Dalilai mabambanta sun haifar da ba wannan aya -kamar yawa-yawan ayoyin AlKur'ani mai girma- fassarori dabam-daban wajen fayyace ko su wane ne Ahlul-Baiti da Allah ke nufi. Malaman Ahlusunna sun hakaito kusan fassarori bakwai da aka ba Ahlul-Bait a wannan aya, kamar cewa ana nufin "Mutanen Haramin Makka ne" da cewa "Mutanen Madina ne" da cewa "Annabi da Matansa ne su kadai". Wadanda duk ba a karfafa su ba a tsakanin Ahlussunna, don haka muma za mu kawar da kai daga gare su don gujewa bata lokaci a kana bin da keda karancin fa'ida. Fassarorin da aka fi tattauna su, kuma su zamu tattauna a wannan makala su ne zantukan:- 1- Wadanda suka fassara Ahlul-Baiti a wannan aya da cewa su ne matan Annabi su kadai, kuma babu wanda ke shiga cikinta tare da su. dalilinsu da ya sa wadannan suka zabi wannan fassara shi ne ganin cewa ayar ta zo a tsakiyar maganar da ake yi da su matan Annabin ne su kadai; da kasancewar ana iya amfani da kalmar saboda shigar su cikin iyali. Wannan fassara ana dangana ta ga Ikrama da Mukatil, kamar yadda Ibin Abi Hatim da Ibin Asakir suka fitar daga gare su, shi kuma Ikrama ya dangana fadar haka ga Ibin Abbas. Ga abin da Siyudi ya fitar a cikin tafsirinsa game da haka:- Ibin Jarir da Ibin Mardawi sun fitar daga Ikramah (r.a) cewa: "Ba abin da ku ke tafiya a kai ba ne, ayar ta sauka ne a kan matan Annabi."[1] Har ila yau Siyudi ya fitar da haka ta wata hanyar, cewa Ibin Sa'id ya fitar daga Urwa cewa:- Ayar tsarkakewa ta sauka ne a kan matan Annabi su kadai, kuma a dakin Ummul-Muminina A'isha aka saukar da ita.[2] Hakika wannan fassara na baci da dalilai kamar haka:- A- Cewa wannan ra'ayin Ikramah ne shi da Urwa (a wata riwayar da Mukatil), ko in ka so ka ce fahimtarsu ce. Hatta su da kansu kuwa ban yi tsammanin sun tilatastawa wani -hatta almajiransu- karbar wannan fassara dole ba. Don haka suna bukatar kawo dalilin da zai karfafa ra'ayinsu don yin nazari a kai; wannan kuwa shi ne abin da babu. Don haka ana da hujjar yin watsi da wannan fassara ta su, masamman idan aka sami ingantattun hadisai da ke bayyana sabanin abin da suka tafi akai. Akwai su kuwa. B- Alamu sun nuna cewa Ikrama ya fuskanci karfafan dalilai ne daga masu wata fahimta game da ayar. Muna iya fahimtar haka daga abin da ya bude maganarsa da shi na cewa: "Ba kamar yadda kuke tafiya a kai ba ne..." Ina ganin cewa dalilin da ya fuskanta dake kare fassarar da ta sabawa tasa na da karfi hatta a zuciyar Ikraman kansa; saboda haka ne ma a wani wurin aka hakaito shi yana daukar matsayi mai karfi da cewa: "Duk wanda ya so zan iya yin mubahala -tsinuwa- da shi a kan cewa ayar ta sauka ne a kan matan Annabi."[3] Wannan riwaya (in kiranta da riwaya ya inganta), a kashin kanta, tana tabbatar da raunin fassarar Ikrama, kuma shi da kansa yana jin raunin matsayinsa; in ba haka ai babu bukatar mubahala, abu na dalili!, ga wadancan sun bayyana nasu dalilai sai a kawo abin da ke goge su kawai! C- Bugu da kari kuma masu wannan fassara ba su da amsar da za su bayar ga dalilin da ya sa aka kebe wannan da yin amfani da lamirin jam'in maza ko maza da mata; in da aka ce "Ankum" da "Yutahhirakum"; domin da ana nufin matan Annabi ne su kadai -kamar yadda wadancan ke ikirari-, da babu makawa a yi amfani da lamirin da aka yi amfani da shi a ayoyin da suka gabaci wannan aya da wadanda suka zo bayan ta, wato da sai a ce: "Ankunna" da "Yutahhirakunna". D- Ga kuma wani hadisin da Ibin Kathir ya fitar ta hanyar Muhammad bin Rayyan, daga Hassan bin Ibrahim, daga Sa'id bin Masruk; isnadinsa ya kare da Yazid bin Haban zuwa Zaidu bin Arkam; wanda Zaidu ya bayyana rashin shigan matan Annabi cikin Ahlinsa ya da tabbatar da ma'anarta danginsa. A hadisin an tambayi Zaidu ne cewa: "Shin matansa na cikin Ahlul-Baiti ?" Sai Zaidu ya ce: "A'a, wallahi mace na kasancewa tare da namiji na wani lokaci, sannan ya sake ta sai ta koma zuwa iyayenta da danginta. Iyalansa su ne asalinsa da tsatsonsa, wadanda aka haramta wa (cin) sadaka bayansa."[4] Wannan na daga dalilin dake nuna cewa ba ''yan Shi'a kawai keda akidar rashin shigan matan Annabi cikin AHALINSA ba. 2- Wadanda ke ganin cewa ayar ta sauka ne a kan matan Annabi da danginsa; don haka kalmar Ahlul-Bati a wannan aya tana nufi matan Annabi da danginsa na daga Iyalan Ali, Iyalan Akil, Iyalan Abbas da Iyalan Ja'afar. Wannan shi ne ra'ayin da Gogan namu ya so dauka, amma sai ya kasa bijioro da shi bisa tsarin da malamai kan kawo. Wannan ne ya sa na ce karatu bai nuna ba a wajensa. Ko ta halin kaka dai, wadanda suka dauki wannan fassara sun dauka ne saboda kokarin gujewa shubuhar lamirin "KUM" a cikin "ANKUM" da "YUTAHHIRAKUM" da ayar ta yi amfani da shi, wanda kuma ba ya bayar da ma'anar taron mata su kadai, maimakon haka yana nuni ne ga taron maza su kadai, ko taron maza da mata. Don haka suke ganin idan suka hado wadannan iyalai hudu tare da matan Annabi sun tsira kenan, tun da sun sami haduwar maza da mata. Dalilan wadancan na dogara da wannan fassara tasu su ne:- A- Ayar ta zo ne cikin jerin ayoyi bakwai da ke jere da juna, wadanda kuma ke magana da matan Annabi (SAWA); saboda haka babu abin da zai fitar da su daga cikin ta. Amsar wannan ita ce: Zuwan ayar cikin jerin ayoyin da ke magana da matan Annabi (SAWA) ba ya nuna saukar ta a kan abin da sauran suka sauka a kai da rashin kadaitar mahallin sakaur ta; domin maganganun Larabawa -da AlKur'ani ya sauka bisa tsarinsu- cike suke da shigar wata magana a tsakanin wata magana dabam alhali ta tsakiyar ba ta da alaka da bangarorin maganar da ta shiga tsakaninsu. Wannan wani abu ne zahiri ga wanda ya saba da zantukan Larabawa; kai! ana ma daukar haka daga cikan hikima. Sukan kira jumlar da shiga tsakiyar maganar da bata da alaka da su da suna "Jumatul-Mu'taridha" ko "Jumlatul-Istitradiyyah"; sukan yi amfani da haka ta salo dabam-daban. To kasancewar AlKur'ani da harshen Larabci aka saukar da shi, kuma yanayin da yake magana yanayi ne dake tattare da hikima da fasahar da suka sa shi ya zama mafi girman mu'jizar Manzon Allah (SAWA); to kuwa a dabi'ance zai rika yin amfani da duk hanyoyin maganar larabci ta mafi hikimar fuska. Wannan aya ta tsarkakewa na daya daga cikin wuraren da AlKur'ani ya nuna wannan gwaninta. Bugu da kari ba nan ne kawai inda AlKur'ani ya yi amfani da wannan fasaha ba! Ya yi amfani da ita a wasu wuraren da suka hada har da cikin wannan aya mai alfarma: An haramta muku (cin) mushe, da jini da naman alade, da abin da aka yanka shi da (sunan) wanin Allah, da (dabba) wadda aka makure, da wadda aka doka, da wadda ta fado (daga sama), da wadda `yar'uwarta ta soke ta da kaho, da abin da namun daji suka ci; sai dai abin da kuka sami yankawa (daga wadancan). Kuma (an haramta muku) yin rabo da kibau na caca, wadannan duk fasikanci ne - daga yau wadanda suka kafirta sun yanke kauna daga (karya) addininku, saboda haka kar ku ji tsoronsu ku ji tsoroNa. A yau Na cika muku addininku, Na kuma cika ni'imaTa gare ku, Na kuma yarda addinin Musulunci ya zama addini (gare ku) - wanda ya matsu (ya ci daya daga cikin abubuwan da aka haramta) don tsananin yunwa ba mai karkata zuwa ga yin sabo ba, to Allah Mai gafara ne Mai rahama." (Surar Ma'ida, 5:3) Wane ne zai tabbatar mana da cewa juzu'in da ke magana game da yanke kaunar kafirai ga karya addinin Musulunci da cikan addini da ni'imar Allah ga Muminai yana da alaka (kai tsaye) da magana a kan hukunce hukuncen dabbobi da yanka? Wane ne zai tabbatar mana da cewa tare suka sauka kuma kan abu daya suka sauka? Babu; alhali kuwa cikin jeri daya suke, kai! cikin aya daya ma. To ai haka al'amarin yake game da ayar tsarkakewa, babu bambanci. Kuma babu shakka kan cewa hakan ya samo asali ne daga hada jerin AlKur'ani, wanda ya saba da jerin saukarsa. Da wannan za mu fahimci cewa kasancewar ayar tsarkakewa cikin jerin ayoyin dake magana da matan Annabi (SAWA) ba lizimta saukarta a kansu da magana da su, ko kore saukarta a kan wasunsu banda su; masamman kuma idan hadisai ingantattu da ba a tantama a kansu suka tabbatar da haka, kamar yadda za mu gani nan gaba. B- Masu wannan ra'ayi na kafa dalili da Hadisin Zaidu bin Arkam da Muslim ya friwaito shi, wanda ke cewa: Zubair dan Harb da Shuja'a dan Mukhallad sun ba ni labari daga Ibin Aliyyah, ya ce: Zubairu ya ce: Isma'il bin Ibrahimu ya ba ni labari da cewa: Abu Hayyan ya ba ni labarin cewa: Yazid bin Haban ya ce: Ni da Hissain bin Sabra da Amr bin Muslima mun tafi wajen Zaidu bin Arkam, yayin da muka zauna a wurinsa sai Hissain ya ce: "Hakika ka riski alheri mai yawa ya kai Zaidu, ka ga Manzon Allah (SAWA) ka kuma ji zancensa, ka yi yaki tare da shi, ka kuma yi salla a bayansa; hakika ka sami alheri mai yawa. Ba mu labarin abin da ka ji daga Manzon Allah ya kai Zaidu." Sai Zaidu ya ce: "Ya dan dan'uwana, wallahi shekaru na sun yawaita, kuma zamani na ya dade, na mance wasu daga abubuwan da na hardato su daga Manzon Allah (s.a.w.a); don haka duk abin da na ba ku labari ku karbe shi, wanda kuwa ban gaya muku ba kar ku kallafa wa kanku neman saninsa." Sannan ya ce: "Manzon Allah ya (taba) tashi cikin mu yana mai huduba a tsakanin Makka da Madina, sai ya gode wa Allah ya kuma yabe shi, ya yi wa'azi ya tunatar, sannan yace:- Ya ku mutane! ni ban kasance ba face wani mutum da ke gab da manzon Ubangijina ya zo min in amsa masa. Lallai kuwa ni mai barin nauyaye biyu ne a cikin ku, na farkonsu littafin Allah Madaukaki, a cikinshi akwai shiriya da haske; to ku yi riko da littafin Allah ku kuma kama shi hannu biyu-biyu.. Sai Zaidu ya ci gaba da cewa: "Sai ya kwadaitar a kan riko da littafin Allah, sannan ya ce:- '...da kuma kebabbun mutanen gidana (Ahlul-Baiti), ina tunatar da ku Allah a kan mutanen gidana..' ya fadi haka har sau uku." A nan sai Hissain ya ce: Su wane ne kebabbun mutanen gidansa ya Zaidu? Ashe matansa ba sa cikin mutanen gidansa? Sai Zaidu ya ce: Matansa na cikin mutanen gidansa, amma Ahlul-Baiti su ne wadanda aka haramta wa (cin) sadaka a bayan shi. Sai (Hissain) ya ce: Su wane ne wadannan? Sai Zaidu ya ce: Su ne iyalan Abbas da iyalan Akil da iyalan Ja'afar da iyalan Ali. Sai (Hissain) ya ce: wadannan duk an haramta sadaka a kansu? Sai (Zaidu) ya ce: Kwarai kuwa.[5] A nan duk da cewa Zaidu ya yi ishara da rashin shigar matan Annabi (SAWA) cikin Ahalinsa da ma'anar Shari'a, da shigarsu da ma'anar lugga, sai dai ya tabbatar da shigan danginsa na gidajen nan hudu. Amma mu a ganin mu wannan fassara ba ingatacciya ba ce; saboda duk inda masu yin ta suka kai suka komo, cikin tsaikon nassin ruwayar Zaidu suke yawo; wato bayan Zaidu ya tabbatar da mashahurin hadisin nan `Thakalain' da ke jona Ahlul-Bati da AlKur'ani wajen wajabcin biyayya da shiryar wa da Isma, sai aka tambayi Zaidu ko su wane ne Ahlul-Baiti, sai shi kuma ya fadi ra'ayinsa da fahimtarsa, wanda ke iya zama daidai ko kuskure; don haka muna iya cewa: Mun yi riko da abin da ya ruwaito, mu bar abin da yake ra'ayin sa ne; abin da kuwa Allah Ya wajabta a kan mu ke nan. Abin da muke bukata shi ne nassin hadisin Manzon Allah (s.a.w.a) da ke nuna ce Ahlul-Baiti (na wannan aya) sune wadancan iyalai hudu; babu shi kuwa a nan. Wani abu da ya zama dole in yi ishara da shi a nan shi ne cewa a iyaka sanina babu hadisi ko daya da ke nuna wannan fassara daga Manzon Allah (SAWA). Maimakon haka wannan riwaya ta Zaidu ita ta rika bayyana da isnadai dabam-dabam. Ke nan abin ijtihadi ne daga Zaidu, yana da lada daya idan ya yi kuskure. C- Wani dalili da masu ra'ayin saukar ayar tsarkakewa a kan matan Annabi (SAWA) da iyalan nan hudu ke bayarwa shi ne cewa: Ai matar mutum ita ke gaba a iyalinsa a cikin harshen shari'a da hankali, kamar yadda Gogan namu ya yi ishara. To amsar wannan ita ce: Da farko dai wahayi ba ya la'akari da wata al'ada ko hankulan wasu mutane, don haka don wasu mutane ko wasu al'adu sun yi la'akari da matar mutum a matsayin iyalinsa, wannan ba ya nuna cewa haka daidai ne a ganin Shari'a. Wannan kenan ya fitar da fadar cewa dole matar mutum ta zama iyalinsa a harshen Shari'a. Idan muka yi la'akari da ma'anar kalmar Iyali a harshen larabci za mu samu ba ta da ma'ana daya takamaimai. Idan aka dangana ta da wani, tana iya nufin duk wadanda ke karkashin kulawarsa, ko wadanda yake da alakar jini da su, ko matarsa ita kadai ko wasu kebabbu daga danginsa. Don haka fassara daya ta lugga bata yiwuwa a nan. Yanayin da kalamar ta zo da halin da aka yi amfani da ita a magana ne kawai zai bayyana manufarta. Wato dai tana da abin da suke kira da "al-Mushtarak al-Ma'anawi". alKur'ani ya yi amfani da kalmar da ma'anoninta na lugga kamar a kan Annabi Ibrahim da Mala'iku suka yiwa matarsa albishir da samun da, ita kuma ta nuna mamaki saboda kasancewarta ba ta haihuwa kuma mijinta ya tsufa, sai Mala'iku suka ce mata: Yanzu kya yi mamaki kan al'amarin Allah! Rahamar Allah da AlbarkarSa su tabbata gare ku MUTAN-WANNAN GIDA (Ahlul-Bait). Hakika Shi (Allah) abin godewa ne Mai girma. (Hudu: 73) Mutan gidan Annabi Ibrahim (AS) a nan ya kunshi matarsa. A cikin Surar Daha kuma an yi bayanin zancen Musa da cewa: Lokacin da ya gano wuta sai ya ce da Iyalinsa "Ku zauna (a nan) lallai ni na hangi wuta (zan je) ko na zo muku da garwashinta… Daha: 10). Iyalinsa (AHLUHU),wanda ya maimaita a surar Kasasi aya ta 29 da Surar Namli aya ta 7, yana nuin matarsa ita kadai. Amma AlKur'ani bai shigar da matar Annabi Ludu cikin Iyalinsa ba, kamar yadda ya zo da cewa: Saboda haka sai Muka tserar da shi da iyalinsa, sai matarsa kawai ita ta kasance daga wadanda suka saura {don fuskantar halaka} (al-A'arafi:83). Kai akwai ma inda AlKur'ani ya yi amfani da kalmar IYALI da ma'anar da ba ta kunshi mata da miji ba, kamar yadda ake iya fahimta daga wannan aya mai albarka: Idan kuwa kuka ji tsoron lalacewar dangatakarsu (mata da miji), to ku aika wakili daga IYALINSA da kuma wakili daga Iyalinta; idan suna nufin gyara to Allah Zai daidaita tsakaninsu.. (Al-Nisa'i:36) Dacewar dukkan Musulmi ne cewa IYALINSA/IYALINTA a nan yana nufin danginsu. Don haka yayin da aka dangana AHAL da Annabi (SAWA), hadisai kawai ke iya fayyace ainihin ma'anarta. Wannan shi ne nazarin Shi'a. Idan muka koma dalilan saukar wannan ayar tsarkakewa, wadda a cikinta ne aka ambacin 'Yan Gidan-Annabi (Ahlul-Bait), za mu ga ba sa taimakawa kowa face ta 'yan Shi'a. Dalilan 'Yan Shi'a A kan Tasu Fahimtar
Sanannen abu ne cewa 'yan Shi'a na fahimtar cewa Ahalin Annabi (SAWA) su ne Ali, da Fatima, da Hassan da Hussaini (Amincin Allah da YardarSa su tabbata gare su baki daya). Amma a dunkule idan muka koma muka yi nazari a kan riwayoyin da suka yi magana game da saukar ayar tsarkakewa (wadda ita ke iyakance ko su waye Ahlul-Bait), za mu gansu sun kasu kashi uku kamar haka:- A- Riwayoyin dake nuna saukarta a kan matan Annabi su kadai; wannan mun bayyana cewa ra'ayi ne na Ikrama da Urwa da Mukatil. Bayanai kuwa sun gabata a kan rashin ingancin wannan fahimta a tsakanin Musulmi baki daya. B- Riwayoyin dake nuna saukarta a kan dangin Annabi (SAWA) na daga Iyalan Ali, da na Abbas, da na Akil da na Ja'afar; wanda ijtihadin Zaidu bin Arkam ne. Shi ma wannan bayani game da shi ya gabata. C- Hadisin dake bayyana saukar ayar a kan wasu kebabbu daga Iylan Annabi (SAWA) wadanda sune: Ali, Fadima, Hassan da Hussaini (AS), tare da shi Manzon Allah (SAWA) din. Wannan shi ne gaskiya idan aka yi nazarin hadisan da suka tabbatar da haka din. Ga wasu daga cikin wadannan hadisai kamar haka:- 1- Siyudi ya fitar daga Ibin Jarir da Ibin Munzur da Ibin Abi Hatim da Dabrani da Ibin Mardawi, daga ummul-Muminina Ummu Salma (RA) matar Annabi (SAWA), ta bayyana cewa: Manzon Allah (SAWA) ya kasance a dakinta a wani wurin zama na shi, a lokacin ya lulluba da wani mayafi sakar Khaibara, sai Fadima (AS) ta zo da wani akushi dauke da abinci, sai Manzon Allah ya ce mata: "Kira mijinki da 'ya'yanki Hassan da Hussaini." Sai ta kira su; a daidai lokacin da suke cikin cin abinci sai wannan aya ta sauka ga Manzon Allah, sai Manzon Allah ya kama gefen mayafinsa ya lullube su da shi, sannan ya fito da hannunsa daga cikin mayafin ya daga sama ya ce:- "Ya Ubangiji wadannan ne Iyalina (Ahlul-Baiti), kuma kebabbu na; don haka ka tafiyar da kazanta daga gare su ka kuma tsarkake su tsarkakewa." Ya fadi haka har sau uku. Daga nan sai Ummu Salma (RA) ta ce: "Sai na shigar da kaina cikin lullubin na ce: `Ya Manzon Allah, shin ina tare da ku?' Sai ya ce: "Kina tare da alheri" har sau biyu.[6] Siyudi ya fitar da wannan hadisi ta hanyoyi masu yawa, haka ma Ibin Kathir. 2- A wani hadisin da Siyudi ya fitar, ya zo cewa: Ummu Salma (RA) ta ce: "Ayar tsarkakewa ta sauka ne a dakina, a lokacin akwai talikai bakwai a dakin, sune (Mala'ika) Jibirilu, (Mala'ika) Mika'ilu, Annabi, Ali, Fadima, Hassan da Hussaini, a lokacin ni ina bakin kofa, sai nace: 'Ya Manzon Allah! ni ba na cikin Ahlul-Baiti?' Sai Annabi (SAWA) ya ce: 'Kina bisa alheri, cikin matan Annabi.'_ Babu shakka kan cewa hadisan dake magana a kan saukar wannan aya a kan wadannan ta hanyoyi masu yawa sun wuce haddin tawatiri, ta yadda ba za su bar fagen tantama a kan ingancinsu ba, wannan ne ma ya sa manyan malaman hadisi a bangaren Ahlussunna da amintattunsu suka riwaito su, suka kuma sanya su cikin jerin hadisansu. Ga wasu daga wadannan malamai kamar haka:- 1- Muslim, ciki Sahih, da isnadinsa zuwa Sufayya bint Shaibah daga A'isha, a juzu'i na 3, shafi na 188, babi na 9, hadisi mai lamba 2,424, bugun Darul-Fikir dake Beirut. 2- Muhyis-Sunna Alhassan bin Mas'ud al-Bagawi, cikin littafinsa Misbahus-Sunna, juzu'i na 4, shafi na 183, hadisi na 4,796; bugun Darul-Ma'arifa dake Beirut. Har ma ya bayyana ingancin hadisin. 3- Abu Hatim Muhammad bin Haban (wanda ya rasu s shekara hijira ta 354), a cikin jerin hadisan da yake ganin sahihancinsu, kamar yadda Ala'uddin Ali bin Bulban ya fitar a cikin littafinsa Al-Ihsan Bi Ta'arib Sahihi Ibin Haban, juzu'i na 9, shafi na 61, hadisi na 6,937, bugun Darul-Umiyya da ke Beirut. Ya sadar da isnadinsa zuwa Wasilatu bin Al-Ash'as. 4- Tirmizi, a cikin Jamu's-Sahih, juzu'i na 5, shafi na 351, hadisi na 3,205; da shafi na 352 hadisi na 3,206; da shafi na 603 hadisi na 3,787; da shafi na 699 hadisi na 3,871, bugun Dar Ihyau't-Turath al-Arabi dake Beirut. 5- Dabarani, a cikin littafin Majma'us-Sagir, juzu'i na 1, shafi na 134. 6- Ibin Hajar Al-Askalani, a cikin littafisa Al-Madalibul-Aliya, shafi na 360, wanda aka buga a kasar Kuwait. 7- Ibin Hajar, a cikin Fatahul-Bari (Sharhin Bukhari), juzu'i na 7, shafi na 60, bugun Masar. 8- Baihaki, a cikin Sunan al-Kubra, juzu'i na 2, shafi na 149-152; da juzu'i na 7, shafi na 63. 9- Dabari (Abu Ja'afar), a cikin littafin Jami'ul-Bayan, juzu'i na 22, shafi na 6 da na 8, bugun madaba'ar Al-Halbi da ke Masar. 10- Allama Ibrahim bin Muhammad al-Baihaki, a cikin littafin al-Mahasinu Wal-Masawi'u, shafi na 298, bugun Beirut. 11- Bukhari, cikin littafinsa Tarikh al-Kabir, juzu'i na 1, sashi na 2, shafi na 70, lamba na 1,719 da 2,174, bugun Haidar Abad. 12- Jaluddini Siyudi, a cikin littafin Mafhamatul-Akran Fi Mubhamatul-Kur'an, shafi na 32, bugun AlKahira. 13- Hakim Haskani, a cikin littafin Shawahut-Tanzil, juzu'i na 2, shafi na 10 har zuwa shafi na 92, daga hadisi na 632 har zuwa hadisi na 774, ta hanyoyi dabam-dabam har fiye da 140; bugun madaba'ar al-A'alami da ke Beirut. 14- Zahabi, a cikin littafin Siyaru A'alamun-Nabala'i, juzu'i na 2, shafi na 122, da juzu'i na 3, shafi na 254 da na 283 da na 265, da juzu'i na 10, shafi na 347; bugun Mu'assasatur-Risala da ke Beirut. 15- Ibin Asakir, a cikin littafin Tarikh Damashk, a babin tarihin Imam Hassan (AS), shafi na 63-72, hadisi na 113-128; bugun madaba'ar Muhammadi dake Beirut. 16- Ahmad bin Hambali, a cikin Masnad, juzu'i na 1, shafi na 330, bugun Maimuniyya da ke Masar; da juzu'i na 5, shafi na 25, bugun Darul-Ma'arif da ke Masar. Ya kuma bayyana ingancin hadisin. 17- Nasa'i, a cikin littafinsa Khasa'is Amirul-Mumini_, shafi na 4. 18- Ibin Athir, a cikin littafinsa Usudul-Gabati Fi Ma'arifatis-Sahabati, juzu'i na 2, shafi na 12 da na 20, da juzu'i na 3, shafi na 413, da juzu'i na 5, shafi na 521 da na 589. 19- Wahidi, a cikin littafinsa Asbabun-Nuzul, shafi na 203. 20- Ibin Arabi, cikin littafin Ahkamul-Kur'ani, juzu'i na 2, shafi na 166. Da wasun wadannan masu yawan gaske wadanda yanayi ba zai bari a kawo su duka ba. Ina ganin saboda yawan hanyoyinsu da ingancin isnadinsu ne ma ya sa dole har mutane irin su Ibin Taimiyya -tare da irin bakar kiyayyarsa ga zuriyyar Manzon Allah, masamman ma Ali bin Abi Dalib- suka mika wuya da cewa a kansu (wato Ali, Fadima, Hassan da Hussaini) ta sauka, kamar yadda ya fada cewa:- Yayin da Allah Madaukaki Ya bayyana cewa Yana bukatar kawar da kazanta daga mutan gidan AnnabiSa (Ahlul-Baiti), Ya kuma tsarkakesu tsarkakewa; Annabi (SAWAa) ya kira mafi kusancinsa daga mutanen gidansa, wato wadanda suka fi kebanta da shi, sune: Ali, Fadima da shugabannin matasan Aljanna (Hassan da Hussaini). Sai Allah Ya hada musu hukunta tsarkakewa a garesu da cika addu'ar Annabi a kansu.[7] Haka nan ya maimaita ambaton saukarta a kan wadanda 'yan Shi'a ke fada fatawa ta 5/5 na cikin littafinsa al-Fatawal-Kubrah[8]. Duk kuwa da cewa a wani wurin kiyayyar ta tsingule shi, ta sa shi ya yi karo da kansa, yayin da ya ce: Wannan ba wani abu ba ne sai nufi kawai daga Allah na tsarkake su da addu'ar Annabi gare su da haka, amma wannan ba ya nufin cewa Allah Ya tsarkake su da gaske!! Maimakon haka, shi wani horo ne da aka hore su da shi, daga abin da ya ke bayyana cewa wannan na daga abin da aka hore su da shi ba bayar da labarin abin da ya faru ba ne, akwai abin da ya bayyana cikin `Sahih' cewa Annabi (s.a.w.a) ya kewaye mayafi a kan Ali, Fadima, Hassan da Hussaini, sannan ya ce: "Ya Allah wadannan sune kebabbun iyalina (Ahlul-Baiti), don haka ka kawar da kazanta daga garesu ka kuma tsarkake su tsarkakewa." Wannan hadisin Muslim ya riwaito shi cikin `Sahih' dinsa daga A'isha, haka nan masu `Sunan' sun riwaito shi daga Ummu Salma."[9] Bayan Ibin Taimiyya ya yarda cewa `Ashabul-Kisa'i' (wato Ali, Fadima, Hassan da Hussaini) sune Ahlul-Baiti din da ake nufi a ayar tsarkakewa, sai kuma -kamar yadda ya saba- ya shiga kokarin kautar da hadisin daga muradinsa, ta hanyar kawo shakku cikin addu'ar Manzon Allah (SAWA) gare su. Ya manta cewa shi da kansa ya nuna manufar wannan addu'a da cewa: "Kebanci ne ga Manzon Allah (SAWA), abin da ke nuna kokarinsa (SAWA) na nuna cewa wannan aya a kansu ta sauka ba wasun su ba." Allah Ya tsarkake su daga mummunan abu, Ya kuma kare su da rahamarSa. Ahlul-Baiti Ma'asumai Ne
A wani dogon hadisi da Shaukani ya fitar, an riwaito Annabi (SAWA) yana bayyana manufar tsarkake Ahlinsa da cewa: Sannan Ya sanya kabilun (a cikin) gidaje (dabam-daban), sai Ya sanya ni cikin mafi alhairin gidaje, wannan shi ne fadarSa Madaukaki: "Allah na nufin kawai Ya kawar da kazanta ne daga gareku Ahlul-Baiti, Ya kuma tsarkakeku tsarkakewa." Domin ni da mutanen gidana (Ahlul-Baiti) tsarkakakku ne daga zunubbai.[10] Har ila yau a kan haka Ibin Jarir da Ibin Abi Hatim sun riwaito daga Katada ya ce: "Allah Ya tsarkake su daga mummunan abu, Ya kuma kare su da rahamarSa." Wannan ba ra'ayin Katada ba ne, domin a wani wuri ya bayyana inda ya samo wannan fahimta da kuma karin bayani a kan haka da cewa: Dhahhak bin Mazakim ya bayyana cewa: Manzon Allah (SAWA) ya kasance yana cewa: Mu Ahlul-Baiti ne da Allah Ya tsarkake su, (mu ne) bishiyar Annabci kuma ma'adanin sako, kuma wurin kaiwa-da-komowar Mala'iku, gidan rahama kuma ma'adanar ilimi. Kalmomin Tsarkakewa daga zunubi, da Bishiyar Annabci, da Ma'adanin Sako da Wurin kaiwa-da-komowar Mala'iku duk bisa rahamar Allah; su ne siffofin Isma da Shi'a ke imani da su ga Ahlul-Baiti (AS). A Karshe
Ta bayyana nassosin Shari'a na hadisan Manzo (SAWA) da suka fito ta bangarorin dukkan Musulmi suna karfafa saukar Ayar Tsarkakewa ne a kan kebabbun nan biyar da Shi'a ke fada. Duk wani abu ba wannan ra'ayi ne da ijtihadodi dake karo da nassosi. Don haka Manzon Allah ya yi bayanin ko su waye Ahlinsa da kansa. Limamin Sharri sai dai ba mai bin Sunna ba ne wajen fada da 'yan Shi'a bisa fassararsu da ta ginu a kan dalili. Ya ragewa mai neman gaskiya ya san abin yi kan haka. Sai mun hadu a bayani kan Matan Annabi a wajen 'yan Shi'a. allah Ya sada mu da alheri Bissalam |