Wilayar AliDa Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
A wasu darussa da suka gabata, mun fahimci cewa sakon Ghadir da ya zo tsakanin ayoyi biyu, ta Isar Da Sako da ayar Cikan Addini, shi ne ya cika addini, kuma da shi ne hujjar Allah ta cika a kan mutane. Haka da wannan sako ne addinin Musulunci ya zama yardajje a wajen Allah. Mun tabbatar da cewa wannan sako shi ne nada Ali (AS) a matsayin majibincin al'amari Musulmi. Da wani zancen, Manzo (SAWA) ya karbar masa bai'ar Musulmi, kuma ya hore su su mika masa wilaya. Mun tabbatar da cewa kalmar maula a hadisin ba ta iya daukar wata ma'ana, daga cikin duk ma'anonin da take iya dauka, sai kalmar aula, wanda shi ne zancen Wilaya. Wannan ne zai iya bude mana kofar yin 'yar sassarfa a kan nazariyyar Wilaya a addini. Wilaya kalma ce ta larabci da ke iya daukar ma'anoni dabam daban; wannan ne ma ya ba wasu kofar yin tawilin hadisin Ghadir da wawantar da mutane a kan manufarsa, sai dai asalin kalmar na da ma'anarta, wadda duk wata ma'ana da ba wannan ba, ta aro ce da aka ba kalmar bisa ka'idar larabci da suke kira da majaz, ba hakika ba. Ibnu Munzur, a cikin Lisanul-Arab, wajen bayanin kalmae Waliyyu, ya fitar da cewa: "Daga Sunanye Allah Madaukaki akwai al-Waliyyu; wato mamallakin abubuwa baki daya, kuma mai gudanar da su. Ibnu Athir na cewa: 'kamar dai kalmar Wilaya na nuna gudanarwa, da iko, da kasancewa a hannu ne'". Sibawaihi, wanda shi ne madugu uban-tafiya a Nahawun larabci, ya ce: "Walaya, da fataha (wato wasali bisa) shi ne asalin kalmar (al-masadar). Wilaya, da kasara (wato wasali kasa) kuwa, suna ne. (duba Lisanul-Arab n Ibnu Munzur). Daga Tushe
Daga asaln kalmar, kamar yadda madugun Nahawu -Sibawaihi- ya fada, kalmar Wilaya na nuna iko da mulki ne. Mulki na hakika a kan abubuwa kuwa, yana hannun mai cikakken iko ne, wannan da al'amuran samarwa, da halitta, da wanzuwa, da dauwamarwa ke komawa gare Shi; wannan kuwa Shi ne Allah Madaukaki. Irin wannan Mulki ne malaman mu ke kira da al-Wilayah al-takwiniyyah, wadda ke nufin Wilayar Halitta Da Gudanarwa. (Duba littafn Wilayatul-Fakih, na Haidar Aali Haidar, shafi na 42). Haka nan Shari'a na amfani da kalmar a kan mulkin da ake ba talikai kamar Annabawa, da Imamai, da Fakihai masu adalci a lokacin fakuwar Imamai, da sunan al-Wilayah al-Tashri'iyyah, wadda ita ce ikonsu a kan mutane, a matsayinsu na jakadun Allah da hujjojinsa a kan mutane. Babban bambancin dake tsakanin wadannan biyun shi ne cewa na farkon sun kira ta da Hakikiyyah, wato ita ce tushe da ta taro ikon tasarrufi ta hanyar samarwa da rasarwa bisa dogaro da kai. yayin da ta biyun suka kira ta da Nisbiyyah, mai nuna matsayin mai mukamin a kan iya kawo gyara a fagagen ayyuka; kuma ta iyakntu da iyakokin shar'antawa da tsara rayuwar mutane ta zama daidai da bukatun Mahaliccinsu. Daga nan za ta bayyana cewa Wilayar Imam Ali tana cikin nau'i na biyu ne. A nan dole mu yi ishara da cewa a nan ba magana muke yi a kan ikon takwini da Annabawa da Imamai ke iya tasiri a cikin su, kamar raya matacce, da irin dawo da rana bayan ta fadi, da tsaga wata ba. Wannan zancensa na wani babi daban da bai shigo iyakokin makalarmu ba. Abin da muke nufi da kasa Wilaya zuwa wadda ta kadaita da Allah Shi kadai, idan har wani ya same ta, to bisa sababi ne da 'izini' daga asalin mai ita, Allah Madaukaki. Sai kuma wadda da ma mahallinta mutum ne, ita ce Wilayar Tashri'iyyah. Sai a lura da kyau. Wilaya A Mahangar Musulunci
A dunkule, tunan tunanen Musulunci baki dayan su suna daukar siga ce ta Musuluncin a matsayinsa na akida. Ta fuskar akida kuwa, ana iya lura da cewa Musulunci na kallon mutum ne a matsayin shugaba da ke wannan doron kasa, wanda kuma yake da cikakken iko na nassi. Don haka Musulunci ya kyamaci duk wata lalatataccen biyayya da dan Adam kan tsinci kansa a ciki a wasu lokuta. Don haka, shugabanci da Khalifanci da Musulunci ke kallon mutum da shi a wannan rayuwa, yana kallonsa ne a matsayin khalifancin mutum a sararin samuwa a fagen Takwini, wato halitta da mahaliccin duniya kuma Mai rike da akalar al'amura da ikon wanzarwa a doron kasa Ya kirkira. Don haka, khalifancin mutum a doron kasa na karkashin dokokin samuwarta ne, da ke hannun Kudura da bata da iyaka, wato Allah kenan: Ya ce Ubangijinmu Shi ne Wanda Ya ba kowane abu halittarsa sannan Ya Shiryar da shi (shiriya ta halitta). Taha:20:50. Sannan samuwar mutum na karkashin dokokin samarwar Ubangiji -Allah- ne, wanda ya sa dole mutum ya zama karkashin gudanarwar Allah: Allah Wanda Ya halicci kowane abu kuma Shi Mai wakilci ne a kan komai. (al-Zumar:64). Ta hanyar bin ka'idojin halitta, hankalin mutum na iya riska da fahimtar lizimcin biyayya da aiki da abin da Allah ke so. Domin hankali na riskar irin alakarsa da bukatarsa ga Zatin Allah, wannan bukata da alaka da ba sa yankewa; alhal kuma Shi Allah Ya wadata daga komai, kuma Shi Ya san dabi'ar halitta ta mutum. Har wa la yau, wannan hankalin shi ke riskar irin maslaha ta hakika da ke tattare da bin tsare tsaren Allah, wadanda shari'o'inSa shka shara don toshe tawayar mutum, wanda kuma shi mutum din, da ma iyakantacce ne, saboda ba shi da ingantacciyar sura ta tsarin rayuwa: Hukunci na Allah ne kawai, (kuma Shi) Ya yi horo da kar ku bauta wa kowa sai Shi. (Yusuf:40). Kamar haka hankali ke iya fahimtar cewa dokoki tun farko suna hannun Kudura ne, ba a hannun wani dabam ba. Daga nan ne akidar nan ta Musulunci ta fito, wadda ke cewa: "Hakkin shari'anta shari'a da ikon haka sun takaita ne ga Allah Madaukaki shi kadai". Don haka ba biyya da da'a ga waninsa, sai wanda ya zo a kasan naSa horon; ba a kafadarsa ba, balle kuma samanSa. Wannan shi ne tsagwaron Tauhidi. Manufa a nan, ita ce fitar da janibin nan na 'yantarwar Musulunci da ikonsa na amsa bukatar mutumin jiya, da na yau, da na gobe da siga iri daya, don tserar da shi (mutum din) daga nau'o'in bautar gumaka na jiya, da na yau, har da na gobe, ta dukkan fuskokin da suka bayyana (na duwatsu da katattaki ne ko na mutane da aljanu da makamantan haka). Musulunci, da mabuwayin daidaicn nan nasa da kowa ke iya gani, shi ke iya fuskantar da shar'ance shar'ancensa ta hangensa na Takwini, wanda ke nufin cewa iko da mulkin halitta, duk a hannun Mahalicci suke, Shi kadai, kuma ba Shi da abokin tarayya a kan haka; to a bisa wannaWilaya al-tashri'iyyah ma tasa ce, ba tare da aboin tarayya ba. Shi ke da ikon sa ta (ita Wilayar) a inda Ya so, don Shi Ya fi sanin inda ta cancanta: Allah ne Ya fi sanin inda (ya cancanta) Ya aje sakonSa. (al-An'am:124). Wilaya: Bukatar Dole Ga Dan Adam
Idan muka lura da mutum, a matsayinsa na tushen al'umma ko cibiya ta zamantakwa (bias la'akari da cewa daga daidaikun mutane ake gina al'umma kuma ake samar da zamantakewa), kuma muka yi la'akari da shi ta fuskokin tawayarsa ta dabi'a (wadda ke tagwaitar halittarsa), za mu sami bukatar Wilaya bayyane karara a fagen rayuwarsa. haka nan tunanin wata rayuwa ta hakika ga al'ummar dan Adam wadda a cikin ta duk tsare tsaren siyasa, da shari'a, da dokoki ke gudana yadda ya kamata (irin wannan tunani) ba ya yiwuwa har sai tare da tunanin Wilaya a gefe guda, saboda matsayin da Wilayar ke da shi na ikon tsari da magance matsaloli ta dukkan fuskoki. Ya zuwa yanzu abin da aka bayyana a sama ba ya bukatar wani dalili fiye da wanda ya gabata. Domin waiwayen farko ga dokokin zamantakewa da tsare tsaren siyasa na tabbatar da waccan hakika. Ana iya ganin tsare tsaren kotunan shari'a, a matsayinsu na hanyoyin magance tawayar da kan addabi mutane a matsayinsu na daidaikun da al'umma, a karkashin kowane tsarin siyasa na duniya komai raunin tsarin kuwa; ga daman da kundayen tsarin mulki ke ba ba shugaban kasa ko firaminista da sauransu; duk wadannan na nuni ne ga wannan bukata ta Wilaya. Kai fiye da haka ma, mafi yawan gwamnatocin da daulolin da ke wuce iyaka a da'awar 'yancin dan Adam ma suna nuni ne ga imani da Wilaya. Misali, duk dokar da Congrass ta fitar a Amurka tana daukar sigar biyayya ta dole, kuma dokar Congrass ce kawai ke iya ba shugaban Amurka ikon zartarwa ba tare da ya saurari kudurin majalisar wakilai ba. Wannan haka yake, ci-gaban kasashen Yamma na tafiya ne tare da girmama tunanin Wilaya, da ma'anar da muka bayyana, kuma yana ba shi sigar lizimci. Domin a tsare tsaren siyasar kasashen Yamma na yanzu, majalisar dokar da majalisa ke kudurtawa ko kudurin mafi girman cibiyar siyasa ta kasa, takan zama dole a aiwatar da ita. Sai dai akwai bambanci tsakanin nazarin Wilaya a Musulunci da nazarinta a tunanin Turawan Yamma, saboda bambancin akida da kowa ke iya gani a tsakanin tunane tunanen biyu. Babban bambancin shi ne cewa Musulunci ne kawai ya iya bambance wa tsakanin Wilayah al-Takwiniyyah da Wilayah al-Tashri'iyyah, sannan ya sa na biyun ya zama reshe ne ga na farko. Tunanin Yamma ba shi da hanyar wannan bambancewa bisa abin da ya shata wa kansa na akida da tunani. Haka nan Wilayar Musulunci na samo asali ne daga kokon zuciyar addinin Musulunci da akidarsa; don haka kake ganin sharadin adalci da amana ga majinbincin Wilaya al-Tashri'iyyah; alhali a tsarin turawa tsohon barawo, ko wanda aka sani da zalunci na iya darewa kan mukamin da ya fi girma a kasa, matukar dai ya biya bukatun tsarinsu zabe ko nadi. Musulunci ne kawai ya takaita da tunanin "Mafifici na shugabana": Shin yanzu wanda ke (iya) shiryarwa zuwa ga gaskiya shi ya fi cancanta a bi; ko wanda ba ya (iya) shiryarwa sai dai (ma) a shiryar da shi? me ya same ku kuke (irin wannan) hukunci? (Yunus:35). Wilayar Ali A Nassosin Musulunci
Ya zuwa yanzu mun fahimci cewa sakon Ghadir dai na Wilaya ne, kuma mun fahimci bukatar dan Adam ga wannan Wilaya, da cewa tsare tsaren siyasu da suka wanzu kuma ake ganin sun sami nasara a fannoni da dama, sun ginu ne a bisa imani da Wilaya, an san haka ko ba a sani ba. Haka mun yi nuni da cewa Wilayar Musulunci da ke hannun Manzo (SAWA) ne Allah Ya hori Manzon naSa (SAWA) da ya mika akalarta ga Ali (AS) kafin ya bar duniya;, har ma ya ba shi lamunin kariya a kan haka. Kuma Manzo (SAWA) ya aiwatar da wannan aiki bisa shaidar Musulmi a tsawon tarihi. Abin tambaya a nan shi ne: Shi wannan wani abu ne da Allah Ya hukunta shi daga baya, ko kuwa tun fil-azal Allah Ya riga Ya kaddara haka, don haka dole ya zama Annabawa da Manzannin nan na Allah guda 124,000 sun san wannan Wilaya da makomarta ta karshe, kamar dai yadda suka san Annabcin karshe da wanda ya hau kansa a matakinsa (Annabcin) na karshe, wanda shi ne Muhammad al-Mustafa (SAWA)? Bayanin nan na karshe shi ne dalilan da hankali da shari'a ke karfafawa. Wannan shi ne abin da za mu yi bayanisa ta hanyar takaita da ambaton nassosin shari'a da ke karfafa wannan akida, da barin dalilan hankali don gudun tsawaitawa da tsaurarawa. Da farko ya wajaba a san cewa haihuwar Wilayar Ali a wannan addini ya zamananci haihuwar Musulunci ne baki dayansa. Kuma nassosin Musulunci da suka yi ta jadda wannan Wilaya sun yawaita; ga kadan daga cikin su: 1- Fadar Allah Madaukaki, a cikin AlKur'ani mai girma: Lallai Allah ne kawai Majibincin (al'amuranku), da ManzonSa da wadanda suka ba da gaskiya, wadanda suke tsayar da sallah (kuma suke) bayar da zakka (sadaka) a lokacin da suke ruku'u. duk kuwa wanda ya mika Wilaya ga Allah da ManzonSa da (wadannan) Muminai, to hakika rundunar Allah su ne masu galaba. (al-Ma'ida:55-56). Duk da cewa a bisa al'adarsu ta neman makubuta daga duk wani abu da zai zika musu hujja a kan matsayin Ali (AS) da 'ya'yansa (AS), wasu malaman Ahlusunna su yi kokarin kawo shakku a kan saukar wannan aya a kan abin da muke fada, saboda amfani da lafazin jam'i maimakon mutum daya a lafazin da ke cikin ayar mai cewa: "wadanda suka ba da gaskiya" da "Muminai". Sai dai, kamar ko yaushe, zakara bai ba su sa'a ba, domin ba su sami goyon bayan ka'idar harshen larabci da ke halasta hakan ba, kamar yadda wasu ayoyin AlKur'ani suka kara karfafa haka yayin magana da mutum daya ta amfani da sigar jam'i. Wannan shi ne abin dacewa a kai dangane da wanda aya ta 173 ta cikin Surar Aali Imrana ta sauka a kansa. Haka dalilin saukar wannan ayar bai tagaza wa ra'ayinsu ba. |