'Yan'uwantaka Da Daidaitawa



NA UKU: TAFARKIN ‘YAN’UWANTAKA DA DAIDAITAWA

Amma bisa ma’aunin tafarki na uku, shi ne cewa abin da alakar zamantakewa ta kumsa shi ne “’yan’uwantaka da daidaitawa”. Muna iya ganin koyarwar wannan tafarki cikin bayanai daban-daban na alakokin zamantakewa, ko kuma ka’idojin alakar, kamar yadda za a ga hakan idan aka koma ga abubuwan da muka ambata a baya, kamar batun fara gabatar da sallama (gaisuwa), haramcin kaurace wa mumini, fadada tunani cikin alakoki, wanda hakan na nuni ne da daidaituwa da kuma ‘yan’uwantaka.

Haka nan cikin batun karfafa ginin alaka ta zamantakewa, misali tarurruka da haduwa da juna, musanyen ziyarce-ziyarce ko kuma tausayi da rahama tsakani, ko kuma amsa wasikun da aka aiko wa mutum, da dai sauransu.

Haka kuma muna iya ganin wadannan abubuwa cikin dokoki da ka’idojin na gaba daya musamman cikin ka’idar lizimtuwa da abubuwan da suke wajibi, kauna da kyautatawa.

A ka’ida ta farko za mu iya ganin batun alaka ta gaba daya ta daidaitawa tsakanin musulmi, kamar isar da amana, tsayar da shaida, hakkokin zamantakewa na gaba daya, kamar halartar jana’iza da gai da mara lafiya.

Haka nan hakkokin dan kasa na mutum musulmi irinsu haramcin zubar da jini da dukiyarsa, wato kashe shi bai halalta ba, haka nan karban kudadensa, haka wuce gona da iri kan mutumci da iyalansa, hatta shiga gidansa da kallon cikinsa ba tare da izininsa ba.

Haka nan hakkoki na ma’anawiyya na mutum musulmi irinsu kiyaye mutumci da karamarsa, rashin halalcin kaskantar da shi da cin mutumcinsa, ko kuma wulakanta shi, ko cin namansa, ko bayyanar da sirrinsa.

Kai ba ya halalta a zalunce shi, da wofantar da shi, ko cutar da shi, ko tuhumarsa ko tsoratar da shi, ko zubar da mutumcinsa, zaginsa ko la’antarsa, sanya ido kan shige da ficensa, kamar yadda karin bayani zai zo nan gaba.

Kamar yadda za mu ga hakan cikin ka’ida ta hudu da kyau cikin dukkanin tafarki da hanyoyin da Allah Madaukakin Sarki Ya yi bayani kansu, kuma Ahlulbaiti (a.s) suka jaddada su kamar gaisuwa tsakanin mutane, kyautatawa wajen kalami, girmama sauran mutane, saduwa da mutane cikin fara’a da sakin fuska, gaisuwa da musafaha, runguma da sumbanta, da dai sauransu da za a iya ishara da su a wajajen da suka dace nan gaba.

Mai yiyuwa fitaccen abin da ke nuni da wannan lamari shi ne abin da aka ruwaito a babin sallama (gaisuwa) da suka hada da na daga wajibcin mayar (amsa) da sallama ga kowa don tabbatar da wannan daidaituwa, haka nan wajibcin amsa wasikun da aka aiko wa mutum.

An ruwaito Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Amsa wasikar da aka aiko wa mutum wajibi ne kamar wajibcin amsa sallama, mai fara sallama shi ya fi cancanta da Allah da ManzonSa[1]”.



1 2 next