Halayen Zahra-4



Halayen Sayyida Zahara (s.a) - 4

Ibn Shahri Ashub ya fada cewa: “Ahmad Bilaziri ya ruwaito, haka ma Abul kasir alkufi a littattafansu, da murtadha a cikin Shafi, da Abu Ja’afar a cikin talkhis cewa Annabi (s.a.w) ya aure ta tana budurwa ne, kuma wannan yana karfafa abin da aka fada a littattafan Alanwar da albida’I cewa Rukayya da zainab ‘ya’yan Hala ‘yar’uwar Hadiza ne”[1].

Kuma su ma’abota wannan ra’ayi suna da dalilansu a cikin littattafan hadisai da na nasabobi da na tarihi[2].

Kuma abin da yake cikin sahihul buhari yana karfafa wannan lamarin cewa: “daga Nafi’u cewa wani mutum ya zo wa Dan Umar sai ya ce; Ya baban Abdurrahman me ya sanya ka kake yin hajji wata shekara wata kuma ka yi Umara ka bar yaki saboda Allah madaukaki, kuma ka san cewa Allah ya kwadaitar game da shi?

 Sai ya ce: Ya kai dan dan’uwana an gina musulunci a kan abubuwa biyar ne: Imani da Allah da manzonsa, da salloli biyar, da azumin watan Ramadhan, da bayar da zakka da hajjin dankin Allah.

Sai ya ce ya kai baban Abdurrahman shin ba ka ji fadin Allah madaukaki a littafinsa ba: “idan wasu jama’a biyu na muminai suka yi fada ku yi sulhu tsakaninsu idan kuwa daya ta yi zalunci a kan dayar to ku yaki mai yin zalunci har sai ta koma zuwa ga al’amarin Allah” (Hujurat: 9). “Ku yake su har sai ya kasance babu wata fitina addini ya kasance na Allah ne” (Bakara: 193)?

Sai ya ce: Mun yi wannan yayin da musulunci ya kasance kadan ne, ya kasance ana fitinar mutum daga addininsa ko su kashe shi ko kuma su azabtar da shi har sai da musulunci ya yi yawa babu wata fitina yanzu.

Ya ce: me zaka ce game da Ali da Usman?

Sai ya ce: Amma Usman Allah ya yi masa afuwa amma ku kuna kin yi masa afuwa, amma Ali shi dan Ammin Annabi ne kuma surukinsa, sai ya nuna gidansa ya ce: Wannan ne gidansa kamar yadda kuke gani”[3].

Ibn Umar yana nunawa da hannunsa zuwa ga gidan Ali (a.s) cewa; ya kasance tare da Annabi (s.a.w) kuma muna iya ganin yadda ya kawo cewa shi ne surukin Annabi (s.a.w) mijin ‘yarsa amma bai fadi hakan ga Usman ba, wanda wannan yake nufin shi mijin agololinsa ne! Madogara: Masa’ilu Majallati JaishusSahaba; Al’ustaz Ali Kurani Alamili

‘Yar Annabi (s.a.w) Fadima Zahara (a.s)

Ita ce Fadima Zahara (a.s) kuma babanta shi ne Muhammad dan Abdullahi, kuma babarta ita ce sayyida Hadiza uwar muminai, mijinta shi ne Imam Ali shugaban wasiyyai, kuma daga 'ya'yanta da jikokinta akwai imamai masu tsarki.

An haifi Fadima ishirin ga jimada sani a shekara ta arba'in daga rayuwar Annabi (s.a.w) kuma ta yi shahada tana abar zalunta a ranar talata uku ga jimada sani shekara ta sha daya hijira, shekarunta goma sha takwas ne.

Imam Ali (a.s) shi ne ya binne ta a Madina ya boye kabarinta da wasiyyarta domin ta kafa hujja kan al'umma da zaluntar ta da aka yi da kuma kwace mata hakkinta. Kuma ta kasance kamar babanta a ibada da zuhudu da fifiko da takawa, kuma Allah madaukaki ya saukar da ayoyin Kur'ani game da ita[4].

Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana yi mata lakabi da "shugabar matan talikai" kuma ya yi mata alkunya da "babar babanta" yana son ta so mai tsanani, kuma yana girmama ta girmamawa mai girma, har ya kasance idan ta shiga wajansa sai ya yi maraba da ita ya mike tsaye domin girmama wa gareta, sannan kuma ya zaunar da ita wurinsa, wani lokaci har ya sumbanci hannunta, kuma ya kasance yana cewa: Allah yana yarda da yardar Fadima yana kuma fushi da fushinta[5].

Ta haifa wa Imam Ali (a.s) Imam Hasan da Imam Husain da Muhsin (a.s) wanda aka yi barinsa saboda cutarwa da babarsa ta fuskanta, da kuma sayyida Zainab, da Ummu kulsum (a.s).

Wafatin Nana Fatima (a.s): Kamar yadda muka san ice cewa sayyida Zahara (a.s) ta samu kantaa cikin wani hali na bakin cikin rabuwa da Mahaifinta, ta yadda kullum tana cikin kuka da bakin ciki. ta yadda ba za ta iya kamewa ba, wannan hakika yana faruwa ne saboda abu uku:-

·       Ta fi kowa sanin matsayi da darajar Mahaitinta, muhimmancin rayuwarsa cikin al'umma da abin da wafatinsa ya kunsa na rashi cikin wannan afumma.

·       Abubuwan da za su sami zuriyarta a baya na kisa da dauri a daidai lokacin da kowa ya juya musu baya, ba su da wani mai taimako sai Allah.

·       Fitintunu da bala'i da al'ummar musulmi za su dinga shiga. sakamakon barin wasiyyar manzo ta biyayya ga Imam Aliyu ((a.s)) da sabawa wasiyyar Manzo (s.a.w). ta yadda shugabancin musulmi zai koma hannun jabbirai  mashaya giya da sunan khalifancin Mahaifinta bayan wasu lokuta kamar yadda ya faru a daulolin Banu Umayya da Banu Abbas

Ba ka jin komai sai kuka cikin gidan Imam Ali (a.s), mutanen Madina ko'ina sai kuka kake ji. Matan Banu Hashim dukkansu sun hadu cikin gidan suna ta kuka. Imam Aliyu ((a.s)) yana zaune a tare da shi akwai Hasan da Husaini, suna ta kukan rabuwa da mahifiyarsu. Ita kutna Ummi Khulsum ta fita waje tana kuka tana cewa: "Ya Babanmu, Ya Manzon Allah, hakika yau kam mun rasa ka dukkannin rasawa, babu saduwa nan duniya har abada, mutane kuwa sai zuwa suke ba iyaka suna yi wa Imam Aliyu ((a.s)) ta'aziyya.

Sai Abubakar da Umar suka ce: In za a yi mata salla a bari sai sun zo ko kuma a aika musu. Nana (a.s) ta yi wafati ne bayan la'asar zuwa magriba, lokacin da jama'a suka ga dare ya yi ba a yi mata salla ba, sai suka yi zaton jana'izar sai gobe za a yi, don haka sai suka watse. sai wadanda aka sanar da su yadda abin yake kawai suka tsaya. Cikin wannan daren Imam ((a.s)) ya yi mata wanka, Asma'u tana zuba mishi ruwa, sannan ya sanya mata likkafaninta. Lokacin da dare ya yi nisa sosai mutane sun yi barci. sai Imam ya kira jama'arsa suka yi wa Nana ((a.s)) salla. wanda suka hada da: Salmanul Farisi. Ammar Ibn Yassir. Abu Zarri Gifari. Mikdad. Huzaifatul Yamani. Abdullahi Ibn Mas'ud. Abbas Ibn Abdulmuttallib. Fadeel Ibn Abbas. Akilu. Zabair Ibn Ayywam, Buraida da wadansu 'yan jama'a daga Banu Hashim.

Imam Ali (a.s) ya shige gaba don ya yi wa diyar Manzon Allah salla. Yana mai cewa: "Ya Ubangiji 'yar Manzonka ta yarda da ni, ya Ubangiji! hakika ta faku cikin kawaici, ka yaye mata. Ya Ubangiji an kaurace mata ka sadar da lta, Ya Ubangiji hakika an zalunce ta ka bi mata hakkinta, kai ne mafi alkhairin masu hukunci". Sannan sai ya yi mata salla raka'a biyu, ya daga hannuwansa sama yana cewa: "Wannan 'yar Manzonka ce Fatima, ka fitar da ita daga duhu zuwa haske".

An samu ruwayoyi daban-daban dangane da inda kabarin sayyida Zahara (a.s) yake, amma wasu sun tafi a kan cewa yana Bakiyya ne, wasu kuma sun tafi a kan yana cikin dakinta. lokacin aka fadada Masallacin Manzo (s.a.w) sai ya zama yana cikin Masallacin Manzo (s.a.w). Kodai mene ne ya faru an riga an boye kabarin nata kamar yadda ta yi wasiyya da hakan ga Imam Ali (a.s) domin ta nuna zaluntarta da wannan al'umma ta yi na rashin kula da hakkinta da na mijinta.

Wannan al'amarin kawai ya isa ga mai karatu ya yi tunani a kai, me ya sa haka ta faru In ba dalili, me ya sa yanzu ba wani mahaluki cikin al'ummar annabi (s.a.w) da zai iya zuwa  Madina ya ce ga barin 'yar Manzon Allah?!

Bayan haka mata kabari ne, sai Imam (a.s) ya shiga cikin kabarin sannan Abbas da dansa Fadhal suka mika mishi ita ya sanya ta cikin kabarin. Hawaye suna ta zubo masa bi da bi! Bayan ya sanya ta sai ya ce: "Ya kasa ga amana nan na ba ki, wannan ita ce diyar Manzon Allah, da sunnan Allah Mai Rahma, Mai jinkai, da sunan Allah bisa addinin Manzon Allah! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com
--------------------------------------------------------------------------------
[1] Ibn Shahri ashub, manakibu aali abi talib: 1/138
[2] Banatun nabiyyi am raba’ibihi na sayyid Ja’afar Murtada. Da halfiyyatu Kitabi ma’asatuz Zahara (a.s) da kuma assahih min siratinnabiyyi: 2/129 na mawallafin: 6/24
[3] Buhari, sahihul buhari: 5/157
[4] Fadima azzahara fil kur'ani.
[5] Ihtijaj: shafi; 354.