Halayen Zahra-3



Halayen Sayyida Zahara (s.a) - 3

Haka nan aka gaggauta mata fitunu da jarabawowi a rayuwa a shekaru na budurci har zuciyar ta ta tsage saboda rashin uwa!! Bakin ciki ya girgiza ta tana karama mai rauni, ta kusa ta fadi kasa ba don juyawa da Baban (s.a.w) ya yi zuwa gare ta ba da gaggawa yana mai shafe mata hawaye kamar yadda take shafe masa, ta kafu a kan hakuri da juriya!!.

Tana mai dimuwa cikin lamarinta, ba ta san mai zata yi ba; shin zata yi juriya ne da bala’in da ya same ta na rashin uwar da babu wata uwa kamarta ko kuma zata yi wa Babanta da babu uba kamarsa ta’ziyyar rashin matarsa da babu wata mata kamarta ne!.

Nan da nan sai ta zabi ta kasance mai ta’aziyya da lallashi ga uban domin bazatar da aka yi masa na amminsa da matarsa, tana mai yakini cewa ba ya rasa mata maras misali ne kawai ba, har ma ya rasa mai kariya ne mai dauki-ba-dadi da gwagwamarya domin kare hadafinsa kamar yadda amminsa Abu Talib (a.s) yake daya rukunin mai kare shi mai kuma lallashi da tausayi mai juriya, kuma ga shi ya rasa masu ba shi kalmomi masu dadi da ra’ayi mai dacewa.

Sai Fadima ta yunkura ta motsa a wannan karon ba domin ta tambayi Babanta ba sai domin ta lallashe shi ta kara masa karfin gwiwa ta kawar da bakin cikinsa tana mai shafe masa hawayi daga kumatunsa masu albarka (s.a.w) tana nuna masa kauna irin wacce uwa kan nuna wa danta da kuma son nan da ya rasa daga Khadiza, domin haka ne ta zama Babar banta kuma ‘yarsa a lokaci guda[1].

Haka nan ta zama uwa ga uban (a.s) a kiyayewa da kauna kuma ‘ya a nasaba da tarbiyyatarwa da koyi amma uwa a kula da kiyayewa.

Haka nan ta fara wata marhala ta rayuwa sabuwa ta fara sabon shafi na rayuwa da Babanta ko zata iya zama kamar khadija ga Babanta (s.a.w) kamar yadda Ali (a.s) ya zama kamar amminsa (s.a.w) Abu Talib (a.s) gareshi.

Haka nan Fadima ta sha wahala tana mai cire kayoyi daga digadigan Babanta tana mai shafe masa jini daga kafafunsa tana mai wanke hannyansa da shafe masa kasa daga fuskarsa tana mai kawar da bakin cikin nan na ‘ya’yan hanji da kayan ciki daga bayansa da kirjinsa, har shekarar ta ta tara ta wuce.

Babanta ya kasance karkashin zaluncin masu makwabtaka da shi har ta wayi gari tana mai nemansa wata rana sai ta yi kicibis da kazanta a kansa da kasa da kayoyi, saboda haka ta gaggauta tana mai kawar da wannan da hannayenta masu ni’ima tana mai kuka saboda abin da ya sami Babanta na daga cutarwar Kuraishawa da gabarsu da kuma cutarwar makota da makusantansa daga Bani Abdi Manafi, sai wannan ya sanyaya masa zuciya, fushinsa ya kau, zuciyarsa ta kwanta hankalin ‘yarsa ya faranta, tana mai kuka daga halin da ta gan shi a ciki, shi kuma yana mai ce mata: “Kada ki yi kuka ya ‘yata Allah zai kare Babanki”.

Kafirai ba su kyale Fadima (a.s) ba kamar yadda ba su kyale Babanta ba kamar yadda wani mafi wautarsu Abu Jahal (L) ta ji shi yana zagin Babanta (s.a.w) saboda haka ne ma ta kasa mallakar kanta ta yi raddi ga shi Abu Jahal (L) da kalmomi masu hikima da ke cike da fasahar nan ta Bani Hashim amma saboda Abu Jahal ba shi da kunya da mutunci bai san shi ba har abada, sai ya daga hannunsa ya mare ta a fuskarta yana mai ci gaba da zagi da cin mutunci ga Manzo (s.a.w), Fadima (a.s) ta tafi tana mai bakin ciki da kuka sakamakon abin da yake yi wa Babanta, har ta wuce wuri da Abu Sufyan yana mai jin kukanta da ganin hawaye na zuba a kumatunta (a.s) yana mai tambayar ta me ya same ki ya ‘yar Muhammad!

Haka nan wata rana Fadima (a.s) ta wuce wasu mutane daga manyan Kuraishawa suna shawara kan al’amarin Muhammad (s.a.w) sai ta ji wasu suna cewa: Wallahi ba ma ganin Muhammad (s.a.w) zai daina abin da yake yi, idan mu ka kyale to lallai zai shuna mana bayinmu a kanmu da ma’aikatanmu, kuma zai canza matanmu da ‘ya’yanmu ta yadda babu wata dubara da zata rage garemu, me kuke gani?.

Abu Jahal (L) ya motsa yana mai cewa ina ganin ku kashe shi kawai. Sai wani ya ce: Yaya zamu yi da fushin Bani Hashim da takubban dakarunsu?. Abu Jahal ya ce: Amma yadda za a yi shi ne, kowanne daga cikinku ya dake shi da takobi dukan kwaf daya sai ku yi musharaka a jininsa gaba daya ta yadda Bani Hashim ba za su iya daukar fansa ba sai dai maganar diyya.

Da Fadima ta ji wannan magana sai zuciyarta ta cika da tsoro a kan Babanta, ta lizimci wajan, ta ki barinsa, idanunta suna kula da hanya har sai ta ga Babanta ya bullo da sauri sai ta gaya masa duk abin da Kuraish suka yi  na makirci da kaidi.

Sai ya gaya mata cewa kada ta damu: “Ki tabbata ya ‘yata Allah ba zai taba ba su dama a kan Babanki ba”. Annabi ya wuce masallaci har sai da ya shiga ya wuce mutanen da suke mitin a kansa domin kashe shi, sai suka yi shiru suka rufe idanunsu saboda abin da suka gani a fuskarsa na haiba da kwarjini, suka mance abin da suka yi ittifaki a kansa dazu, har sai da Manzo (s.a.w) ya tsaya a kansu ya dauki kasa jimki daya ya watsa a kansu yana mai cewa: “Fusaku sun muzanta”.

Sannan ya fuskanci Ka’aba ya yi salla ga Allah madaukaki (s.w.t) a kusa da su, Fadima (a.s) tana tsaye tana ganinsu ba wanda ya motsa daga cikinsu kamar ba wanda ya gan shi, yayin da ya gama sallarsa da munajatinsa sai ya rike hannun ‘yarsa suka tafi gida tare!

Haka nan ta sami wani kunci mai yawa na abin da ta gani wata rana, Babanta yana salla a Ka’aba, ga Abu Jahal (L) da wasu daga Kuraishawa kamar su Asi dan Wa’il Assahami da Haris dan Kais Assahami (L) suna yanka rakumi. Sai Abu Jahal da Umayya dan Khalf (L) suka waiga suka ce da yaransu: Waye zai zo mana da mahaifar rakumin Bani Saham sai ya dora shi a kan bayan Muhammad! (s.a.w) idan ya yi sujada?

Wannan tunani ya yi wa wasunsu daidai Ukuba dan Abi Mu’id (L) da Utba da Shaiba ‘ya’yan Rabi’a (L) suka tashi suka dauko tunbi da mahaifar suka dora kan kafadun Manzon Allah (s.a.w) yana mai sujada.!

Fadima (a.s) ta ga abin da aka yi wa Babanta sai ta gaggauta tana mai jin zogi da bakin ciki mai tsanani a kan abin da ta ga ni, hawayenta suna kwarara a kan kumatunta, saboda haka sai ta bayar da duk kokarinta wajan ganin ta kawar da wannan dauda daga kafadun Babanta (s.a.w), Annabi mai girma Uba mai rahama ya daga kansa yana kallon ‘yarsa Fadima (a.s) idanunsa cike da rahama da tausayi da kauna da yarda da bege gareta, tare da dukkan abin da zuciya zata iya nuna wa na nutsuwa da tabbata da hakuri, sannan sai ya rike hannayenta tsarkaka ya tattaro ta zuwa kirjinsa madaukaki ya ce: “Mamakin yadda kika zama babar babanki da wuri haka Ya Fadima”[2].

Bai bar wannnan waje mai daraja ba tare da ita, wajan da kafiran Kuraish suka bata da dauda sai da ya daga hannayensa zuwa sama yana mai addu’a yana cewa: Ya Allah! ina kai karar Abu Jahal (L) da Utba da Shaiba ‘ya’yan Rabi’a (L)  a wurinka ka. Ya Allah! ina kawo karar Umayya dan Khalf (L) da Walid dan Utba (L) da Ukuba dan Abi Mu’id (L) da…[3].

Kada ka so ka ga irin farin cikin Fadima ‘yar Manzo (a.s) a wannan rana sakamakon irin matsayi da ya ba ta na wannan kalma ta (Babar Babanki) da ya daukaka ta zuwa gare shi, kamar yadda ta iya sanya wa a ran Babanta (s.a.w) a wannan ranar da aka samu haduwa a ruhi guda biyu da haduwar kanshi da kanshi, kuma haske da haske, cewa ruhin Baban (s.a.w) mai kira zuwa ga Allah ya samu sanarwa daga ruhin ‘yar mai neman ta zama uwa ga Baban (a.s) cewa ruhinta ruhi ne mai cike kuma kunshe da tausayi irin na uwa ga uban kuma kariya mai karfi mahalarciya a kowane abu da ya faru ga uban (s.a.w), wanda sau da yawa irin wadannan abubuwa suka yawaita bayan Kuraishawa sun samu dama da wafatin Abu Talib!!, sanarwar da ruhin uban ya samu daga ruhin ‘yar shi ne cewa ita uwa ce, don haka ta cancanci wannan kalam ta Babar Babanta.

Fadima (a.s) ita Kadai Ce ‘Yar Annabi (s.a.w) saboda wasu dalilai masu karfi da suka hada da: Na farko: Ambaton ‘ya’ya da jam’i a fadinsa madaukaki cewa: “Ya kai Annabi ka gaya wa matanka da ‘ya’yanka da matan muminai su sassauto da mayafansu wannan shi ya fi da a san su domin kada a cutar da su, kuma hakika Allah ya kasance mai gafara mai rahama.

Wannan al’amari ba ya nuna cewa manzon Allah (s.a.w) yana da ‘ya’ya sama da daya, al’amarin yana kan kaddarawa ne da ba dole ya kasance yana da samuwa ta zahiri ba, kuma akwai da yawa a kur’ani inda aka yi maganar jam’I na gaba daya amma ana nufin abu daya da shi kamar yadda Allah yake fada a cikin ayar mubahala da cewa: “idan suka yi jayayya da kai kan al’amarinsa to ka ce ku zo mu kira ‘ya’yanmu da ‘ya’yanku da matanmu da matanku da kawukanmu da kawukanku sannan sai mu yi addu’a mu sanya la’ana kan makaryata” (aali imrana: 61).

Kuma dukkan musulmi sun hadu a kan cewa abin da ake nufi da kawukanmu shi ne Annabi (s.a.w) da kuma Imam Ali (a.s), mata kuma wanda jam’I ne ana nufin Fadima Zahara (a.s) ‘ya’ya kuma wanda shi ma jam’I ne ana nufin Imam Hasan da Husain (a.s).

Na biyu: Malaman Shi'a suna da wani ra’ayi kan wannan al’amari, akwai masu ganin Rukayya da Zainabi da Ummu kulsum ‘ya’yan Annabi (s.a)  ne, wasu kuma suna ganin agololinsa ne kuma ‘ya’yan Hala ‘yar’uwar sayyida Hadiza (a.s) da babarsu ta mutu sai sayyida Hadiza (a.s) ta dauki rainonsu, suna ganin cewa Hadiza ta kasance budurwa ba ta yi wani aure ba kafin Annabi (s.a), kamar yadda aka yada game da ita ba, kuma wannan shi ne ya fi kusa da gaskiya, kuma ita ce magana mai karfi.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

--------------------------------------------------------------------------------
 
[1] Ma'aikin Allah (s.a.w) ya yi wa 'yarsa wannan lakabin; duba al'isaba fi tamyizis sahaba: 4/377. al'isti'ab: 4/380. Makatilul Dalibiyyin: 3/132.

[2] Hashiya, shafi: 67.

[3] Dabari: Zakha'irul Ukuba, shafi: 47